Jirgin Sama Ya Rikito Ya Fada cikin Teku, Mutane Sun Mutu

Jirgin Sama Ya Rikito Ya Fada cikin Teku, Mutane Sun Mutu

  • Mutane shida, ciki har da yara maza biyu masu shekaru 8 da 10, sun mutu bayan wani ƙaramin jirgin sama ya faɗa cikin teku a Amurka
  • Jirgin samfurin Cessna 210 ya tashi ne daga birnin New Orleans zuwa Fort Myers da ke jihar Florida kafin ya faɗa cikin Tekun Mexico
  • Jami’an tsaron gabar teku na Amurka sun ce an gano gawarwakin mutum shida a cikin jirgin bayan shafe sa’o’i ana gudanar da aikin ceto

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Amurka – Mutane shida, ciki har da yara maza biyu, sun rasu bayan wani jirgin sama ya faɗa cikin Tekun Mexico a gabar jihar Mississippi ta Amurka a ranar Talata.

Hukumar tsaron gabar teku ta Amurka ce ta tabbatar da mutuwar mutanen, inda ta ce masu aikin ceto sun gano gawarwakin mutane huɗu manya da yara biyu masu shekaru 8 da 10 a cikin jirgin.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kashe malamai 2, sun yi awon gaba da mutane sama da 10

Jirgin sama a teku
Wani jirgin sama a cikin teku. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Rahoton BBC ya nuna cewa jirgin mai samfurin Cessna 210 ya faɗa ne a yankin Tekun Mexico tsakanin garin Pascagoula da tsibirin Horn Island.

Jirgin ya ɓace bayan tashi

Bayanan shafin bibiyar zirga-zirgar jiragen sama na FlightAware sun nuna cewa jirgin na kan hanyarsa daga birnin New Orleans zuwa Fort Myers, jihar Florida.

Sai dai hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta rasa hulɗa da jirgin da misalin ƙarfe 3:45 na yamma, wanda ya yi daidai da ƙarfe 9:45 na dare agogon GMT.

Rahoton Sky News ya nuna cewa daga bisani, jirgin ya faɗa cikin teku, inda aka fara aikin neman mutanen da ke cikinsa.

An gano gawa 6 a hadarin

Mai magana da yawun hukumar tsaron gabar teku, Juan Ros, ya ce masu aikin ceto sun shafe sa’o’i suna neman jirgin da mutanen da ke cikinsa.

Ya bayyana cewa a farkon binciken, jami’an sun gano rigunan ceton rai guda uku, ƙaramin jirgin ruwa na ceto da kuma wani ɓangaren cikin jirgin da ke shawagi a kan ruwa.

Kara karanta wannan

An kashe rayuka da aka tarwatsa 'yan Obi Kwankwaso a wajen kamfen

Shugaba Donald Trump
Shugaban Amurka, Donald Trump. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Daga bisani, masu aikin nutsewa cikin ruwa sun gano gawarwakin mutane shida a cikin babban ɓangaren jirgin.

Kwamanda Trevor Blount, wanda ya jagoranci aikin ceto, ya ce duk da cewa sakamakon ba shi ne abin da suke fata ba, sun yi farin ciki da haɗin gwiwar hukumomi da ya taimaka wajen gano mutanen cikin gaggawa.

Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Amurka (FAA) da Hukumar Binciken Hatsarin Sufurin Jiragen Sama (NTSB) sun ce suna sane da lamarin, kuma za su gudanar da bincike domin gano musabbabin hatsarin.

An kashe tsohuwar sojar Amurka

A wani labarin, kun ji cewa wata tsohuwar sojar rundunar sojin Amurka mai shekaru 36, Allison Lynn Anderson, ta rasu bayan wasu karnuka sun far mata a jihar Georgia.

Anderson, wacce uwa ce ga yara uku, an same ta da munanan raunukan da suka yi sanadin mutuwarta a ranar 16 ga Nuwamban 2026.

Ɗiyarta ta bayyana alhinin rasuwarta, tana mai cewa mahaifiyarta ta rasu ne kafin ta samu damar sanar da ita cewa za ta zama kaka a karon farko.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng