Siyasar Kano: NDC Ta Tsoma Baki kan Zarge Zargen da Gwamna Abba Ya Dorawa Kwankwaso
- Jam’iyyar NDC a Kano ta soki Gwamna Abba Kabir Yusuf kan zarge-zargen da ya jinginawa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso
- Gwamna Abba ya yi zargin cewa Kwankwaso ne ya ba shi umarnin tattaunawa da fadar shugaban kasa domin komawa APC
- NDC ta ce kalaman gwamnan sun saɓa wa matsayar gwamnatin Kano da ta musanta kulla yarjejeniya da Fadar Shugaban Ƙasa a watan Janairun 2024
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Jam’iyyar NDC ta jihar Kano ta soki Gwamna Abba Kabir Yusuf kan zargin da ya yi cewa an matsa masa lamba domin ya taimaka wajen shirya tattaunawa tsakanin Fadar Shugaban Ƙasa da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
NDC ta yi lfatali da zargin da Abba ya yi cewa Kwankwaso ne ya takura masa ya zauna da Shugaba Bola Tinubu kan yiwuwar komawarsa jam’iyyar APC.

Kara karanta wannan
Zance ya ƙare, El Rufai ya tsage gaskiya a gaban kotu kan zargin kutse a wayar Nuhu Ribadu

Source: Twitter
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa hakan na kunshe ne a a cikin wata sanarwa da Mai Magana da Yawun Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen NDC, Hon. Hashimu Sulaiman Dungurawa, ya sanya wa hannu ranar Laraba.
NDC ta musanta zarge-zargen Abba
Jam’iyyar ta bayyana zarge-zargen a matsayin abin takaici, tana mai cewa kalaman gwamnan sun saɓa wa matsayar da gwamnatin Kano ta bayyana a baya game da zargin tattaunawa da Fadar Shugaban Ƙasa.
NDC ta ce hirar da Yusuf ya yi da BBC a baya-bayan nan ta haifar da tambayoyi game da kalaman da ya yi a kan batun a baya.
Rahotanni sun bayyana cewa Yusuf ya yi zargin cewa an rinƙa lallashinsa tare da matsa masa lamba domin ya taimaka wajen gudanar da tattaunawa tsakanin Kwankwaso da Fadar Shugaban Ƙasa kan yiwuwar komawarsa APC.
NDC ta tuna da sanarwar 2024
Da take mayar da martani, NDC ta tuna cewa gwamnatin jihar Kano ta fitar da sanarwa a ranar 29 ga watan Janairun 2024, inda ta musanta cewa an cimma wata yarjejeniya da Fadar Shugaban Ƙasa bayan hukuncin Kotun Ƙoli kan zaɓen gwamna.
NDC ta ce kalaman da gwamnan ya yi a yanzu, bayan kusan watanni 34 da fitar da sanarwar, sun saɓa wa matsayar da gwamnatin ta bayyana a wancan lokacin.
Sanarwar NDC ta ce:
“Canza magana da gwamnan ya yi kan batu guda bayan watanni 34 kacal, tare da zargin Sanata Kwankwaso, abin ƙyama ne kuma abin takaici.”
Jam’iyyar ta ƙara da cewa shawarar da Abba ya yanke na komawa APC zaɓin siyasarsa ne na kansa, kuma Kwankwaso bai umarci shi ya ɗauki wannan mataki ba.

Source: Facebook
Jam’iyyar NDC ta yi gargaɗi kan zargin
Haka kuma, NDC ta nuna damuwa cewa zargin da gwamnan ya yi na iya jefa Fadar Shugaban Ƙasa cikin abin kunya tare da rage amincewar jama’a ga hukumomin siyasa da na shari’a a ƙasar.
Saboda haka, jam’iyyar ta yi kira ga gwamnatin jihar Kano da ta janye zargin, musamman ɓangaren da ya shafi mutuncin Kwankwaso.
Kwankwasiyya ta maida martani ga Abba
Kun ji cewa ƙungiyar Kwankwasiyya ta zargi Gwamna Abba Kabir Yusuf da ƙoƙarin ɗora wa Sanata Rabiu Kwankwaso alhakin sauya sheƙarsa zuwa APC.
Kwankwasiyya ta dage cewa bai kamata a ɗora wa Kwankwaso alhakin matakin da Abba ya ɗauka na shiga jam’iyya mai mulki ba, inda ta.bukaci gwamnan ya kare wannan mataki bisa dalilansa.
Asali: Legit.ng
