Yadda Za Ka Nemi Rancen Kudi daga Gwamnatin Tarayya Ta Hanyar Danna Lambobi a Wayarka
- Gwamnatin tarayya ta bullo da tsarin SPARK da zai bai wa ’yan Najeriya damar karbar rancen kudi domin sayen wayoyin hannu da sauran na’urori
- Masu bukatar amfani da tsarin za su iya shiga ta hanyar danna lambobi (USSD Code) a wayoyinsu na hannu da ba su da intanet
- CREDICORP ta ce tsarin zai taimaka wa masu karbar bashi na farko wajen gina tarihin karbar bashi da kuma samun karin damar hada-hadar kudi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Gwamnatin tarayya ta bullo da wani sabon tsarin neman rancen kudi ta hanyar danna lambobi (USSD), wanda zai bai wa ’yan Najeriya damar samun rancen sayen wayoyin hannu da sauran na’urori
Tsarin zai bai wa yan Najeriya damar neman rancen kudi daga gwamnatin tarayya domin sayen wayoyi ko kwanfutoci ta kananan wayoyinsu ba tare da sun yi amfani da intanet ba.

Kara karanta wannan
Ciyaman ya sha da ƙyar da miyagun yan daba suka farmaki wurin zaɓen fitar da gwanin APC

Source: Facebook
Leadership ta rahoto cewa shirin ba da lamuni na Nigerian Consumer Credit Corporation (CREDICORP) ne ya kaddamar da tsarin mai suna SPARK domin fadada damar samun bashi ga yan Najeriya.
Lambobin da za ku nemi rance
’Yan Najeriya masu sha’awar amfani da tsarin za su iya shiga ta hanyar danna lambar *347*333# a wayoyinsu.
A cewar CREDICORP, an tsara SPARK ne domin saukaka wa jama’a samun rance, tare da taimaka musu wajen gina tarihin karbar bashi a hukumance ta hanyar biyan basussuka yadda ya kamata.
Shirin ya bayyana cewa bayanan yadda mutum ke biyan bashinsa za su taimaka wajen inganta matsayinsa a tarihin karbar bashi, tare da bude masa damar samun wasu hanyoyin hada-hadar kudi a nan gaba.
CREDICORP ta kara da cewa ana sa ran tsarin zai samu karbuwa da kuma isa ga karin ’yan Najeriya kafin karshen shekarar 2026.
An kaddamar da SPARK a Aba
An kaddamar da tsarin ne a wajen baje kolin kayayyaki da ayyukan CREDICORP mai taken “CREDICORP for All” a Aba, jihar Abia.
Taron ya hada masu cin gajiyar shirin, cibiyoyin hada-hadar kudi, ’yan kasuwa da wakilan gwamnati domin nuna yadda rancen sayen kayayyaki zai taimaka wajen bunkasa sana’o’i da inganta rayuwar jama’a.
CREDICORP ta fadi manufar shirin
Da yake jawabi a wajen taron, shugaban CREDICORP, Uzoma Nwagba, ya ce bai kamata a takaita damar samun aron kudin sayen kayayyaki ga wasu tsirarun mutane da cibiyoyin hada-hadar kudi na gargajiya ke yi wa hidima ba.
Ya ce:
“Bai kamata rancen sayen kayayyaki ya zama gata da wasu tsirarun mutane kadai za su samu ba. Ya kamata ya zama dama da duk wani dan Najeriya mai aiki zai iya amfana da ita.”

Source: Twitter
Nwagba ya ce an tsara shirin ne domin samar da damarmakin rance ga ’yan kasuwa, matasa da masu harkokin sufuri.
Ya kaqra da cewa tsarin SPARK zai bai wa ’yan Najeriya hanya mai sauki ta fara gina tarihin karbar bashi a hukumance.
An fara rabon tallafin N50,000 a Najeriya
Kun ji cewa Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da shirin NERSI, wanda zai rika bai wa iyalai masu karamin karfi tallafin N50,000 duk wata.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne ya kirkiro shirin domin samar da tallafin gaggawa ga miliyoyin ‘yan Najeriya da ke fama da matsin tattalin arziki.
Asali: Legit.ng

