'Na Gama da 2': Wike Ya Roƙi Tinubu Ya Kara Masa Jihohi 2 domin ba Shi Nasara a 2027

'Na Gama da 2': Wike Ya Roƙi Tinubu Ya Kara Masa Jihohi 2 domin ba Shi Nasara a 2027

  • Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya roƙi Shugaba Bola Tinubu da APC su ƙara masa jihohin Imo da Kwara domin ya jagoranci yaƙin neman zaɓen 2027
  • Wike ya ce ya kammala aikin da aka ba shi na daidaita al'amuran siyasar Rivers da Abuja, don haka yana neman ƙarin jihohi biyu
  • Tsohon gwamnan Rivers ya bayyana cewa akwai matsalolin siyasa da rarrabuwar kawuna a Imo da Kwara da yake son taimakawa wajen shawo kansu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya roƙi Shugaba Bola Tinubu da Darakta Janar na kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC, Abdul'aziz Yari karin jihohi.

Wike ya buƙaci da su ba shi damar jagorantar yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa a jihohin Imo da Kwara a zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Dalilin matsalar Atiku da minista a 2023 da ya jawo Wike ya tarwatsa PDP

Wike ya nemi alfarma wurin Tinubu
Ministan Abuja, Nyesom Wike da Shugaba Bola Tinubu. Hoto: Lere Olayinka, Bayo Onanuga.
Source: Twitter

2027: Wike ya nemi alfarma wurin Tinubu

Wike ya bayyana hakan ne yayin wani taron tattaunawa da mazauna yankin Gokana da mambobin ƙungiyar Rainbow Coalition a jihar Rivers, cewar Channels TV.

Ministan ya ce ya kammala aikin da aka ba shi na kula da harkokin siyasar Rivers da Babban Birnin Tarayya, don haka yana ganin ya kamata a ba shi wasu jihohi biyu domin ya taimaka wajen ganin Tinubu ya samu nasara.

A kalamansa:

“Kun san an ba ni Rivers da Abuja domin in kula da su, amma a gaskiya mun kammala aikin jihohin biyu, don haka babu wani aiki da ya rage. Yayin da nake tafiya yanzu, zan roƙi darakta janar da shugaban ƙasa su ƙara mini wasu jihohi biyu domin in kai su ga nasara.”
Wike ya bukaci karin jihohi 2 kan zaben 2027
Ministan Abuja, Nyesom Wike yayin taro. Hoto: Nyesom Ezenwo Wike.
Source: UGC

Labarin da Wike ta samu kan jihohi 2

Tsohon gwamnan na Rivers ya ce ya samu labarin cewa ana fuskantar wasu matsalolin siyasa a jihar Imo, don haka yana son zuwa domin taimaka wa Tinubu.

Kara karanta wannan

Abin da matasa suka yi wa Dauda Kahutu Rarara a masallacin Abuja ya fusata jigon APC

Ya kuma ce akwai rarrabuwar kawuna a jihar Kwara, yana mai roƙon Tinubu da Yari su ba shi damar jagorantar yaƙin neman zaɓe a jihohin biyu.

Wike ya ce yana da burin taimaka wa jam'iyyar APC wajen ƙarfafa goyon bayan Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027 da ke tafe, cewar Vanguard.

Wannan kira da Wike kamar shagube ne ga gwamnonin jihohin 2 saboda sabanin da suka samu game da kafa kungiyarsa ta Rainbow Coalition da wasu ƴan APC ke adawa da ita.

Wike ya yi wa Amaechi zazzafan martani

A wani labarin, an ji cewa Nyesom Wike ya bukaci masu tallar Bola Tinubu su hana ADC da NDC samun 25% na kuri'un Abuja a zaben 2027.

Ministan ya bukaci ‘yan kwamitin yakin neman zaben APC su kara kaimi wajen karya musamman ADC da jam'iyyar NDC mai adawa a Najeriya.

Wike ya ce ayyukan Bola Tinubu a Abuja za su taimaka wajen jawo wa APC kuri'u, akasin hasashen wasu ‘yan adawa ke yi saboda su lissafin son rai suke yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.