Yadda Gwamnatin Tarayya Take Zabar Wadanda Za Su Samu Tallafin N50,000 a Najeriya
- Gwamnatin Tarayya ta yi bayanin yadda take zaben mutanen da za su amfana da tallafin N50,000 domin rage radadin halin da ake ciki
- Ta ce tana zaɓar waɗanda za su amfana da tallafin N50,000 ne daga bayanan katin shaida na ƙasa da kuma Rajistar Talakawa da Masu Rauni
- Gwamnati ta jaddada cewa babu wanda zai biya kuɗi ko neman shiga cikin jerin waɗanda za su amfana da shirin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Yayin da mutane da dama ke ci gaba da karbar tallafin N50,000, Gwamnatin tarayya ta yi karin haske kan yadda take daukar mutanen da za su amfana.
Gwamnatin ta kaddamar da tallafin kuɗi na N50,000 ƙarƙashin shirin National Emergency Relief and Stabilisation Intervention (NERSI) domin rage wa talakaaa radadin halin da suke ciki.

Source: Twitter
Ma'aikatar jim kai da yaki da talauci ta tarayya ta wallafa cikakken bayani a shafinta na yanar gizo kan wannan tallafi da ake turawa mutane karkashin shirin NERSI.
Yadda gwamnati ta zabi mutane
Wannan ƙarin bayani ya zo ne a lokacin da ’yan Najeriya da dama ke neman sanin yadda gwamnati ke gano mutanen da za su amfana da tallafin da kuma sharuddan da ake bi wajen tantance cancantarsu.
Bisa bayanan da ke shafin NERSI, ana zaɓar waɗanda za su amfana ta hanya biyu, na farko bayanan katin shaida na ƙasa (NIN) da kuma Rajistar Iyalan Talakawa da Masu Rauni (National Social Register).
Sanarwar ta ce:
"Ana zaɓar waɗanda za su amfana daga sahihan bayanan katin shaida na ƙasa da kuma rajistar al’umma, sannan a tantance su domin tallafin ya isa ga iyalai matalauta da masu rauni.”
Muhimmancin lambar NIN
Lambar Shaidar Ɗan Ƙasa (NIN) ita ce Hukumar Kula da Bayanan Shaidar Ɗan Ƙasa (NIMC) ke bayarwa bayan mutum ya yi rajista.
Ana amfani da lambar wajen tabbatar da sahihancin asalin mutum, sannan ana haɗa ta asusun kamfanonin hada-hadar kudi kamar Opay da mutum ke amfani da shi wajen tura kuɗin tallafin ga waɗanda aka zaɓa.
Rijistar talakawa ta NSR
A gefe guda, National Social Register (NSR) wata ma’ajiyar bayanai ce da ke ɗauke da bayanan iyalai matalauta da masu rauni a Najeriya. Ofishin Haɗa Ayyukan Tsare-tsaren Tallafin Jama’a na Ƙasa (NASSCO) ne ke kula da rajistar.
A cewar NASSCO, rajistar tana ɗauke da bayanan mutane sama da miliyan 70.
Hukumar ta ce yin rajistar mutanen da ke cikin mawuyacin hali aiki ne mai matakai daban-daban.
Bayan haka, ƙungiyoyin ma’aikata da aka horar suna haɗa kai da mazauna yankunan da shugabannin al’umma domin gano iyalan da suka fi buƙatar tallafi.
Daga nan ne ake yi wa iyalan da aka gano rajista ta hanyar amfani da na’urorin zamani, sannan a tantance halin rayuwarsu bisa wasu alamomin talauci.

Source: Getty Images
Ana iya zaɓar iyalan da suka shiga cikin kaso shida na mafi talauci domin shigar da su cikin National Beneficiary Register, wadda ake amfani da ita wajen gudanar da shirye-shiryen tallafin kuɗi.
A cewar shafin NERSI, yin rajista a NIMC da kuma NSR wajibi ne kafin a iya zaɓar mutum domin samun tallafin N50,000.
FEC ta hade ayyukan jin kai wuri 1
Kun ji cewa Majalisar Zartarwa ta Tarayya ta amince da sabon tsarin haɗa ayyukan agajin jin ƙai, tallafin zamantakewa da shirye-shiryen yaƙi da talauci wuri guda.
Sabon tsarin, wanda aka sanya wa suna One Humanitarian One Poverty Response System (OHOPRS), na da manufar inganta ayyukan yaki da talauci a fadin Najeriya.
Asali: Legit.ng


