Gwamna Abba Ya Shirya Daukar Mataki Mai Tsauri kan Jami'an Gwamnati a Kano
- Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi barazanar kai jami’an da suka karkatar da motocin asibitin zuwa hukumomin yaƙi da cin hanci
- An raba motocin asibiti masu ƙafa uku 484 ga mazabu 484 na jihar domin jigilar marasa lafiya cikin gaggawa
- Gwamnan ya ce za a hukunta duk wanda aka samu da amfani da motocin wajen amfanin kansa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi barazanar hukunta duk jami’an ƙananan hukumomin da suka karkatar ko suka yi amfani da motocin asibiti 484 ba bisa ƙa’ida ba.
Gwamna Abba Kabir ya yi gargaɗin cewa duk wanda aka samu yana amfani da motocin wajen amfanin kansa ko kuma cin zarafin shirin zai fuskanci hukuncin da ya dace.

Source: Facebook
Daily Trust ta ruwaito cewa Abba ya yi wannan gargaɗi ne a ranar Talata yayin ƙaddamar da shirin motocin agajin gaggawa na karkara mai suna Abba Gida-Gida Rural Ambulance Service.
Gwamna Abba ya gargadi jami'an gwamnati
A ƙarƙashin wannan shiri, an tanadi motar asibiti ta musamman mai ƙafa uku ga kowace mazaba daga cikin mazabu 484 na jihar Kano.
Gwamnan ya ce duk wanda ya karaktar da motocin za a gurfanar da shi gaban Hukumar Yaƙi da Masu Yi wa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta’annati (EFCC) da Hukumar Korafe-korafen Jama’a da Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano.
Ya ce an sayi motocin ne da kuɗin al’umma, saboda haka dole ne a yi amfani da su kawai wajen jigilar marasa lafiya cikin gaggawa, musamman mata masu juna biyu, yara, waɗanda suka yi hatsari da sauran masu rauni da ke buƙatar kulawar likita.
Gwamnan ya umarci shugabannin ƙananan hukumomi da jami’an da aka ɗora wa alhakin kula da motocin da su tabbatar da gyaransu yadda ya kamata, ɗaukar ma’aikatan da aka horas da kuma samar da ingantaccen tsarin sa ido.

Kara karanta wannan
Gwamna ya fallasa yadda APC ke ɗauko hayar matasa su halarci yaƙin neman zaben Tinubu
Ya kuma yi kira ga sarakuna, shugabannin addinai, kansiloli da shugabannin al’umma da su sa ido kan shirin domin tabbatar da cewa motocin suna gudanar da aikin da aka tanade su dominsa.
Dalilin samar da motocin asibiti
Abba Gida-Gida ya ce an ƙirƙiri shirin ne domin magance jinkirin samun kiwon lafiya, musamman a yankunan karkara, inda lalacewar hanyoyi da nisan asibitoci ke hana marasa lafiya isa wuraren jinya cikin lokaci.
Ya bayyana cewa an zaɓi motocin asibitin masu ƙafa uku ne saboda suna iya ratsawa a hanyoyin karkara masu wahalar bi, inda motocin asibiti na yau da kullum kan fuskanci ƙalubale.

Source: Facebook
A cewarsa, samar da kiwon lafiya bai tsaya ga gina asibitoci da cibiyoyin kula da lafiya matakin farko ba, domin dole ne marasa lafiya su samu damar isa asibiti cikin gaggawa idan wata matsalar lafiya ta taso.
Gwamna Abba ya kafa sabuwar hukuma
Kun ji cewa gwamnatin Kano ta kafa hukumar KASSTOWA domin inganta samar da ruwan sha a yankunan karkara da kananan birane a fadin kananan hukumomin jihar
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da nada Injiniya Sani Bala Danbatta a matsayin mukaddashin shugaban hukumar, yayin da aka nada Aminu Mamman Yaro a matsayin mataimakinsa, tare da wasu daraktoci.
Asali: Legit.ng
