Bayan Fetur, Gwamnatin Tarayya na Shirin Rage Hauhawar Farashin Muhimman Kayayyaki

Bayan Fetur, Gwamnatin Tarayya na Shirin Rage Hauhawar Farashin Muhimman Kayayyaki

  • Gwamnatin tarayya na aiki tukuru don rage hauhawar farashi zuwa ƙasa da 10%, in ji mai magana da yawun Shugaban Ƙasa, Bayo Onanuga
  • Kamfanin NNPC ya amince zai sayar da man fetur ba tare da ƙara ribar sayarwa ba na tsawon kwanaki 30 domin rage wa jama’a raɗaɗi
  • Onanuga ya ce matakin ba wai dawo da tallafin man fetur ba ne, wanda aka soke a ranar 29 ga Mayun 2023

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Gwamnatin tarayya na aiki don rage hauhawar farashi zuwa ƙasa da 10%, in ji Bayo Onanuga, mai magana da yawun Shugaban Ƙasa.

Onanuga ya bayyana hakan ne yayin sanar da wasu ƙarin matakan da gwamnati ta ɗauka domin tallafa wa ’yan Najeriya a daidai lokacin da ake fuskantar matsalar farashin mai a duniya.

Kara karanta wannan

Bayan rage farashi, Gwamnatin Tinubu ta yi bayani kan yiwuwar dawo da tallafin fetur kafin 2027

Bayo Onanuga.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga Hoto: @onanuga1956
Source: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa farashin man fetur ya kai matsayi mafi girma sakamakon toshe mashigar ruwan Hormuz a lokacin yaƙin Amurka da Iran.

A ranar Alhamis ɗin da ta gabata, Ministan Kuɗi, Taiwo Oyedele, ya sanar da cewa za a sayar da man fetur a farashi mai rangwame a gidajen mai na NNPC na tsawon kwanaki 30.

Ko da yake ministan ya bayyana cewa matakin ba ƙoƙari ba ne na dawo da tallafin man fetur, ’yan Najeriya da dama, musamman a kafafen sada zumunta, sun bayyana shi a matsayin yunƙurin sake tallafa wa man.

NNPCL ya shirya rage farashin mai

A cikin sanarwarsa, Onanuga ya ce:

“Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPC) ya amince a yau cewa zai haƙura da ribar da yake samu daga sayar da man fetur ga jama’a, ya koma sayar da shi a farashin da ya saya.

Kara karanta wannan

Atiku ya gano babban shirin Tinubu bayan sanar da rage farashin man fetur

“NNPCL, wanda tuni yake sayar da man fetur a farashi mafi sauƙi a kasuwa, zai aiwatar da wannan sabon shiri cikin kwanaki 30 masu zuwa. Wannan na nufin idan kuɗin da NNPCL ya kashe wajen shigo da litar mai ya kai N1,300, zai sayar wa ’yan Najeriya, musamman masu motocin kasuwanci, a wannan farashin.
“Wannan matakin rangwame da kamfanin ya ɗauka, tare da goyon bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu, na daga cikin jerin matakan da Ministan Kuɗi kuma Mai Kula da Tattalin Arziki, Taiwo Oyedele, ya sanar a yau.”

Onanuga ya ce Oyedele yana fatan sauran ’yan kasuwar man fetur za su yi koyi da NNPCL, ganin cewa ba a sa ran tashin farashin ɗanyen mai da man fetur zai daɗe ba.

Gwamnati na shirin rage hauhawar farashi

Ya ƙara da cewa Oyedele ya jaddada cewa amincewar NNPC na sayar da mai da rangwame bai kamata a fassara shi a matsayin dawo da tallafin man fetur ba, wanda aka kawo ƙarshensa a ranar 29 ga Mayun 2023.

Shugaba Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu lokacin da yake jawabi kai tsaye ga yan Najeriya Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Onanuga ya ƙara da cewa:

“Gwamnatin tarayya tana kuma aiki kan cikakken kunshin matakan kasafin kuɗi da za su taimaka wajen rage hauhawar farashi zuwa ƙasa da 10% a nan gaba kaɗan.”

Tinubu na shirin dawo da tallafin mai?

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta kawo tsarin da 'yan Najeriya za su sayi fetur da arha

Kun ji cewa Gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ta yi watsi da yiwuwar dawo da tallafin man fetur a Najeriya.

Gwamnatin ta yi ikirarin cewa dawo da tallafin zai iya lakume sama da Naira 20 a kowace shekara tare da lalata darajar Naira zuwa kusan N3,000 kan kowace dala guda.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262