Cika Shekaru 80: Abubuwan da Kwankwaso Ya Faɗa kan Atiku

Cika Shekaru 80: Abubuwan da Kwankwaso Ya Faɗa kan Atiku

  • Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya tura sako na musamman da ɗan takarar shugaban kasa a ADC, Atiku Abubakar
  • Kwankwaso ya bayyana Atiku a matsayin ɗan siyasa da ke bayar da gudummawa wajen bunƙasa dimokuraɗiyyar Najeriya tun tsawon shekaru
  • Ya yi wa tsohon mataimakin shugaban ƙasar fatan ƙoshin lafiya, ƙarfi da kuzari yayin da yake bikin zagayowar ranar haihuwarsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya tura sakon taya murna ga tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar.

Kwankwasa ya taya ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar African Democratic Congress (ADC), Alhaji Atiku Abubakar, murnar cika shekaru 80 da haihuwa.

Kwankwasa ya bayyana hakan ne a cikin wani saƙon taya murna da ya wallafa a shafinsa na X a yammacin yau Laraba.

Kara karanta wannan

Atiku ya sake kifar da Tinubu, ya faɗi yadda zai dawo da tallafi, rage farashin fetur

Saƙon ya bayyana Atiku, wanda aka fi sani da Wazirin Adamawa, a matsayin ɗan siyasar da ya daɗe yana bayar da muhimmiyar gudummawa wajen ci gaban dimokuraɗiyyar Najeriya.

A cikin rubutun nasa ya ce:

"Ina taya ɗan'uwana, tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar African Democratic Congress (ADC), Mai Girma Alhaji Atiku Abubakar, murnar cika shekaru 80 da haihuwa.
"Wazirin Adamawa ya ci gaba da kasancewa cikin waɗanda ke bayar da gudummawa mai muhimmanci wajen bunƙasa dimokuraɗiyyar ƙasarmu.
"Ina masa fatan samun ƙoshin lafiya, ƙarfi da kuzari a rayuwarsa."

Kwankwaso ya bayyana cewa Atiku ya kasance mai jajircewa wajen tallafa wa manufofin dimokuraɗiyya da ci gaban tsarin mulkin ƙasar.

Ya kuma yi wa tsohon mataimakin shugaban ƙasar fatan samun ƙoshin lafiya, ƙarfi da kuzari domin ci gaba da gudanar da rayuwarsa.

Atiku Abubakar ya cika shekaru 80 a ranar 25 ga watan Nuwamba, 2026, inda ya samu saƙonnin taya murna daga mutane daban-daban.

Karin bayani na tafe ....

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.