Dikko Radda Ya Ziyarci Sardaunan Daura bayan Dakatar da Sarki

Dikko Radda Ya Ziyarci Sardaunan Daura bayan Dakatar da Sarki

  • Gwamna Dikko Radda, ya ce kyakkyawar alaƙar da ke tsakanin Bola Tinubu da marigayi Muhammadu Buhari ta ƙarfafa zumuncin Fadar Shugaban Ƙasa da al’ummar Daura
  • Radda ya bayyana hakan ne yayin ziyarar da ya kai gidan Sardaunan Daura, Alhaji Auwalu Umar Faruq, tare da tawagar yaƙin neman zaɓen Tinubu–Dikko–Jobe
  • Gwamnan ya kuma nemi addu’a da goyon bayan sarakunan gargajiya da al’ummar Daura ga ’yan takarar jam’iyyar APC a zaɓen 2027 da ke tafe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Katsina – Gwamnan Katsina, Dikko Umaru Radda, ya ce dangantakar da ke tsakanin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ta taimaka wajen ƙarfafa alaƙar Fadar Shugaban Ƙasa da masarautar Daura.

A wata sanarwa da babban sakataren yaɗa labaran gwamnan, Ibrahim Kaula Mohammed, ya fitar a ranar 24 ga Nuwamba, 2026, Radda ya bayyana hakan yayin wata ziyara da ya kai gidan Sardaunan Daura.

Kara karanta wannan

Atiku ya sake kifar da Tinubu, ya faɗi yadda zai dawo da tallafi, rage farashin fetur

Gwamna Dikko Radda da Sardaunan Daura
Gwamna Dikko Radda a gidan Sardaunan Daura. Hoto: Ibrahim Kaulaha Muhammad
Source: Facebook

Ibrahim Kaulaha ya wallafa a Facebook cewa gwamnan ya je ziyarar ne tare da wasu ’yan tawagar yaƙin neman zaɓen Tinubu–Dikko–Jobe gabanin zaɓen 2027.

Abin da Radda ya faɗa a Daura

A yayin ziyarar, Radda ya ce tawagarsa ta zo ne domin gaisuwa, neman albarka da addu’o’in Sardaunan Daura da sauran dattawan yankin.

Ya bayyana cewa yana wakiltar Shugaba Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima, inda ya ce tsohuwar alaƙar Tinubu da Buhari ta ƙarfafa dangantakar tarihi tsakanin fadar shugaban ƙasa da Daura.

Gwamnan ya kuma gode wa al’ummar Daura bisa kyakkyawar tarbar da suka yi wa tawagarsa na tsawon kwanaki 10, tare da neman su ci gaba da yi wa ’yan takarar addu’a da goyon baya.

Maganar Radda kan kujerar Sanata

Haka kuma, gwamnan ya jaddada cewa kujerar Sanatan yankin tana cikin Masarautar Daura, inda ya buƙaci masu ruwa da tsaki su ɗauki batun da muhimmancin da ya dace.

Kara karanta wannan

Bayan rashin 'yan APC 15, tsohon sakataren gwamnatin Zamfara ya rasu

Ya gabatar da ’yan takarar da suka raka shi, ciki har da Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Katsina, Yusuf Muhammadu Buhari, wanda ke neman kujerar majalisar wakilai.

Sauran sun haɗa da ɗan takarar Majalisar Wakilai mai wakiltar Daura, Sandamu da Mai’Adua, da kuma Bishir Sani Daura, ɗan takarar Majalisar Dokokin Jihar Katsina.

Gwamna Dikko Radda
Gwamnan Katsina, Dikko Radda. Hoto: Ibrahim Kaulaha Muhammad
Source: Twitter

Martanin Sardaunan Daura

A nasa jawabin, Sardaunan Daura ya bayyana Radda a matsayin ɗan Daura, mutum mai gaskiya, adalci da riƙon amana wanda ke cika alƙawarinsa.

Ya ce alaƙarsu ba ta taƙaita ga siyasa ko lokacin zaɓe ba, domin ta samo asali ne daga daɗaɗɗiyar mu’amala da fahimtar juna.

Ya kuma jaddada cewa kyakkyawar alaƙar siyasa ba ta kamata ta taƙaita ga rabon kuɗi ko tallafi lokacin zaɓe ba, inda ya yi addu’ar samun zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban al’umma da ƙasa baki ɗaya..

An dakatar da Sarkin Daura

A wani labarin, kun ji cewa an dakatar da Sarkin Daura, Umar Faruk Umar, daga halartar dukkan wasu ayyukan hukuma da tafiye-tafiye bayan wata mata ’yar ƙasar Poland ta zarge shi da cin zarafinta.

Kara karanta wannan

Mutane sun yi rugu rugu da tawagar APC ta yi hadari, an rasa rayuka da yawa

Matar ta yi zargin cewa sarkin mai shekaru 92 ya taɓa ƙirjinta ba tare da izininta ba yayin wata ziyara da ta kai domin yawon buɗe ido, lamarin da ta ce ya ba ta haushi matuƙa.

Zargin ya haifar da ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta, inda mutane da dama suka buƙaci a dakatar da sarkin tare da gudanar da bincike, kiran da gwamnatin Jihar Katsina ta amsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng