Jihohi 5 a Najeriya da Suka Shirya ba da Rancen N300,000 ga Ƴan Ƙasa

Jihohi 5 a Najeriya da Suka Shirya ba da Rancen N300,000 ga Ƴan Ƙasa

Jihohi biyar a Najeriya sun fara rajista, tantancewa da tattara bayanan manoma domin shirin rancen N300,000 da gwamnatin tarayya za ta bayar ba tare da ruwa ba.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Jihohin da suka fara ba da tallafin sun hada da na yankin Kudancin Najeriya guda biyu sai kuma uku daga yankin Arewacin kasar domin tallafa wa manoma.

Za a raba wa manoma rancen kudi
Shugaba Bola Ahmed Tinubu na Najeriya da manoma da aka ware wa rancen N300,000. Hoto: Picture Alliance/Contributor.
Source: UGC

Jihohin da za su ba da rancen

Gwamnatin tarayya ta kaddamar da shirin ne karkashin tsarin GEEP domin taimaka wa manoman kanana, bunkasa noma da inganta samar da abinci a Najeriya, cewar Punch.

Legit Hausa ta jero muku jihohin da suka shirya ba da tallafin a Najeriya.

1 Jihar Lagos

Gwamnatin jihar Legas ta fara gudanar da aikin tattara bayanan manoma karkashin shirin FarmerMoni tare da hadin gwiwar Hukumar Kula da Shirye-shiryen Zuba Jari na Kasa (NSIPA), ta hannun Ma'aikatar Samar da Arziki da Ayyukan Yi.

Kara karanta wannan

Amurka ta kara sunayen 'yan Najeriya 24 cikin wasu 157 da za a fatattako daga kasar

An tura jami'an GEEP zuwa kananan hukumomi 20 na jihar domin gano manoman da suka cancanci cin gajiyar shirin da tantance bayanansu.

An shawarci manoman da ke son cin gajiyar rancen da su tuntubi jami'an shirin da aka ware a kananan hukumominsu domin samun bayanai kan rajista da takardun da ake bukata, cewar Tribune.

Lagos za ta ba manoma rance
Gwamna Babajide Sanwo-olu na jihar Lagos. Hoto: Babajide Sanwo-olu.
Source: UGC

2. Jihar Abia

Jihar Abia ta fara tantance manoman da suka nemi cin gajiyar shirin a zahiri a kananan hukumomi 17 na jihar.

Rahotanni daga TheCable sun nuna cewa manoma 1,160 ne suka kammala wani aikin sabunta bayanan rajistarsu ta yanar gizo, wanda ya ba da damar fara tantance su kai tsaye.

Ana gudanar da aikin ne domin tabbatar da sahihancin bayanan masu neman tallafin, ayyukan noman da suke yi da kuma tantance manoman da suka cancanci shiga shirin.

3. Jihar Niger

Gwamnatin jihar Neja ta bayyana shirin zabo manoma 600 daga kananan hukumomi 25 domin cin gajiyar tallafin rancen.

Haka kuma, jihar ta gudanar da horas da jami'an GEEP da za su kula da gano manoma, yi musu rajista da tantance cancantarsu.

Kara karanta wannan

Bayan hallaka basarake a Niger, gwamnati ta yi magana bayan ɗaukar matakai

Shirin zai shafi bangarorin noma daban-daban da suka hada da noman amfanin gona, kiwon kaji, dabbobi, kamun kifi da kiwon halittun ruwa.

Za a raba wa manoma tallafi
Gwamna Mohammed Umaru Bago ya mayar da hankali sosai kan noma. Hoto: Mohammed Umaru Bago.
Source: Twitter

4. Jihar Kwara

Jihar Kwara ta fara tattara bayanan manoma a kananan hukumomi 16 domin shirin bayar da rancen FarmerMoni.

Manufar aikin ita ce gano manoman kanana da ke bukatar tallafin kudi domin ci gaba da ayyukan nomansu ko fadada su, cewar rahoton Vanguard.

Ana sa ran shirin zai taimaka wa manoma wajen fuskantar tsadar kayan noma da samun muhimman kayayyakin da suke bukata wajen gudanar da ayyukansu.

5. Jihar Plateau

Gwamnatin tarayya ta fara tantance manoman da suka yi rajista domin cin gajiyar shirin FarmerMoni a jihar Plateau.

An sanar da hakan ne yayin wani taron horas da jami'an GEEP a Jos, wanda aka gudanar a ranar 20 ga watan Nuwambar 2026.

Aikin na daga cikin shirye-shiryen tantance masu neman tallafin kafin a fara matakan aiwatar da shirin na gaba.

Abin da manoma ke bukatar sani

Duk da fara wadannan ayyuka a jihohin biyar, hakan ba ya nufin cewa gwamnatin tarayya ta bude rajistar neman rancen ga dukkan 'yan Najeriya ko kuma an fara raba kudin.

Kara karanta wannan

Yahaya Bello ya fadi matakin da ya kamata El Rufa'i ya dauka kafin tsare shi

Manoman da ke son samun rancen N300,000 ya kamata su tuntubi jami'an GEEP a kananan hukumominsu domin samun sahihan bayanai kan rajista, cancanta da tantancewa.

Haka kuma, an shawarci masu neman tallafin da su guji shafukan intanet da ba na hukuma ba ko mutanen da ke karbar kudi da sunan tabbatar musu da samun rancen.

Mahimmanci, kammala tattara bayanan manomi ba ya nufin cewa ya samu tabbacin karbar kudin, domin har yanzu sai an tantance shi tare da tabbatar da cewa ya cika sharuddan shirin.

Manoman da suka cancanci samun rancen

Gwamnatin tarayya na aiwatar da shirin ne karkashin tsarin Government Enterprise and Empowerment Programme (GEEP 3.0), ta hannun Hukumar NSIPA.

Shirin na da manufar inganta ayyukan noma, karfafa samar da abinci da taimaka wa manoman karkara wajen bunkasa sana'arsu ta hanyar samun rancen da ba shi da ruwa.

Gwamnatin Tinubu za ta raba takin zamani

A baya, an ji cewa Gwamnatin tarayya ta ce za ta saki buhunan takin zamani miliyan uku da hatsi da ta tanada domin rage farashin abinci a Najeriya.

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi tanadi domin rage tsadar abinci, zai raba miliyoyin buhunan taki

Ministan noma, Abubakar Kyari, ya ce za a fitar da takin cikin wata guda, yayin da za a saki hatsin da aka ajiye nan ba da jimawa ba.

Gwamnati ta kuma ce za ta fara rabon taraktoci 2,000, yayin da ake sa ran amfanin gona 13 cikin 17 zai samu karuwar yawan amfanin gona.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.