NCC: Yan Najeriya na Cikin Alheri, An Tura Wa Masu Layukan Sadarwa Kudi Ta Wayoyinsu

NCC: Yan Najeriya na Cikin Alheri, An Tura Wa Masu Layukan Sadarwa Kudi Ta Wayoyinsu

  • Hukumar NCC ta ce masu layin waya miliyan 75 sun samu diyya ta katun waya saboda rashin ingancin sadarwa a shekarar 2026
  • Hukumar ta kuma bayyana cewa kusan masu layi miliyan uku sun samu kuɗaɗensu bayan sayen katin waya ko data ya gaza kammaluwa
  • NCC ta ce tana ƙara sanya ido kan kamfanonin sadarwa domin inganta ayyukansu, da magance korafe-korafen kwastomomi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Hukumar Kula da Sadarwa ta Najeriya (NCC) ta tabbatar da cewa an biya miliyoyin yan Najeriya da ke amfani da layukan waya kudi a matsayin diyyar matsalar daukewar sabis a 2026.

NCC ta ce masu layin waya miliyan 75 sun samu sakon katin waya a layukansu saboda rashin ingancin sadarwa a shekarar 2026.

Hedkwatar NCC.
Hedkwatar hukumar kula da harkokin sadarwa ta Najeriya, NCC Hoto: NCC Nigeria
Source: Twitter

A rahoton The Cable, hukumar NCC ta ce an biya diyyar ne sakamakon matsa wa kamfanonin sadarwa lamba su inganta ayyukansu tare da magance korafe-korafen abokan huldarsu

Kara karanta wannan

Tinubu zai fara karɓar harajin 25% daga kuɗaɗen shigan ƴan Najeriya?

NCC ta tilasta biyan mutane diyya

Mataimakin shugaban hukumar (EVC), Aminu Maida, ne ya bayyana hakan a ranar Talata yayin taron Majalisar Masu Amfani da Sadarwa ta 95 da aka gudanar a Legas.

“Ƙarƙashin tsarin biyan diyya ga masu amfani da sabis ɗinmu, masu layin waya miliyan 75 sun samu diyyar kudin waya saboda rashin ingancin sabis zuwa yanzu a shekarar 2026.
"Za mu ci gaba da ɗora wa kamfanonin sadarwa alhakin ingancin ayyukan da suke bayarwa,” in ji Maida.

Ya ƙara da cewa bayanan NCC sun nuna an gudanar da ayyukan gyaran hanyar sadarwa fiye da 6,500 zuwa yanzu a shekarar 2026.

Kamfanonin sadarwa na kokarin gyara

A cewarsa, ana sa ran waɗannan ayyuka za su taimaka wajen inganta sabis din sadarwa ga masu amfani da layukan sadarwa

“Saboda haka, muna sa ido kan yadda ayyukan ke gudana tare da buƙatar kamfanoni su gyara duk wata matsala, domin jarin da suke zubawa ya haifar da ingantaccen sabis a wuraren da kuke zama da aiki,” in ji shi.

Kara karanta wannan

Nuhu Ribadu ya jero abubuwa 4 da suka hana magance matsalar 'yan bindiga a Najeriya

Ya ce idan aka samu babbar matsalar katsewar sadarwa, dole ne kamfanonin su yi bayani kan abin da ya faru da kuma lokacin da ake sa ran za a dawo da sabis ɗin.

Sadarwa.
Wayoyin hannu da turken sabis din sadarwa a Najeriya Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

An maida wa mutane kudadensu

Mataimakin shugaban NCC ya kuma bayyana cewa an dawowa da kusan masu layin waya miliyan uku da kuɗaɗensu bayan sayen katin waya ko data ya gaza kammaluwa a shekarar 2026.

“Ya zuwa yanzu a shekarar 2026, kusan masu layi miliyan uku sun samu kuɗaɗensu bayan sayen katin waya ko data ya gaza kammaluwa, ƙarƙashin tsarin mayar da kuɗi.
"Dole ne mu ci gaba da aiki domin hana faruwar irin waɗannan matsaloli da kuma magance su cikin gaggawa idan sun faru,” in ji Maida.

NCC ta kawo tsarin duba ingancin waya

Kun ji cewa Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) ta shawarci ’yan Najeriya da su tantance wayoyin hannu kafin saye domin tabbatar da cewa an amince da su.

Hukumar ta ce masu sayen waya za su iya duba matsayinta ta hanyar danna lambar *315# ko amfani da shafinta na intanet

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262