'Yar Kasar Waje Ta Yi Magana bayan Goge Bidiyon Abin da Sarkin Daura Ya Mata

'Yar Kasar Waje Ta Yi Magana bayan Goge Bidiyon Abin da Sarkin Daura Ya Mata

  • Wata mata ƴar ƙasar waje da ta zargi Sarkin Daura da taɓa jikinta ba tare da izininta ba ta nemi a sake duba matakin cire bidiyonta daga Instagram
  • Ta ce tana zargin an cire bidiyon ne kai tsaye bayan masu amfani da kafar sada zumunta sun kai rahoto da yawa a kansa
  • Majalisar Masarautar Daura ta ce tana nazarin bidiyon da ke yawo domin tantance sahihancinsa kafin fitar da sanarwa a hukumance

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Daura, Katsina - 'Yar ƙasar waje da ta zargi Sarkin Daura da ke Jihar Katsina da taɓa jikinta ba tare da izininta ba yayin ziyarar da ta kai fadarsa, ta ce an cire bidiyon abin da ya faru daga shafinta.

Matar ta bayyana cewa ta nemi a sake duba matakin da Instagram ya ɗauka na cire bidiyon, inda ta buƙaci a gudanar da bincike domin tantance ko matakin ya dace.

Kara karanta wannan

Sheikh Ahmad Gumi ya yi kira a tunbuke duk sarkin da aka samu ya yi aikin assha

beduinqa.
Yar kasar waje da ta shigo Najeriya yawon bude ido, Mirka Hoto: @beduinqa
Source: Instagram

A cikin wani dogon saƙon bayani da ta wallafa a shafinta mai suna @beduinqa, matar ta ce tana zargin tsarin Instagram ne ya cire bidiyon kai tsaye bayan wasu masu amfani da kafar sun kai rahoto da dama a kansa.

Ta kuma bayyana cewa duk da cire ainihin bidiyon da ta wallafa, kwafinsa da mutane suka dauka ya riga ya bazu sosai a shafukan sada zumunta daban-daban.

Yadda ta ce lamarin ya faru

Matar ta ba da labarin cewa ta yi tafiye-tafiye zuwa birane daban-daban a Najeriya domin yawon bude ido, inda ta yi amfani da motocin haya da sauran hanyoyin sufuri na jama’a.

Ta ce a yayin tafiye-tafiyen nata ta haɗu da wasu sarakunan gargajiya, waɗanda ta bayyana cewa sun girmama ta sosai.

A cewarta, lokacin da ta isa fadar Sarkin Daura, wasu manyan fadawa sun tarbe ta, suka ba ta abinci, sannan suka zagaya da ita domin nuna mata wasu wurarenntarihi a cikin fadar da kuma rumfunan da ake ajiye dawaki.

Kara karanta wannan

Zargin cin zarafi: Sarkin Daura ya shiga matsala bayan yaɗuwar bidiyonsa a Intanet

Sai dai ta yi zargin cewa daga baya aka bar ta ita kaɗai tare da sarkin a wani ɗaki na musamman.

Ta ce sarkin ya zauna kusa da ita a kan kujera mai matasai, ya riƙe hannunta, sannan daga baya ya taɓa ƙirjinta lokacin da ta miƙe domin tafiya.

A cewar matar, ta kunna tabaran zamani mai ɗaukar bidiyo domin yin rikodin abin da ke faruwa ne bayan ta fara jin rashin jin daɗi lokacin da sarkin ya riƙe hannunta.

Dalilin da ya sa ta wallafa bidiyon

Matar ta ce ta yi tunani sosai kafin ta yanke shawarar wallafa bidiyon, amma daga ƙarshe ta ga ya dace ta fitar da shi domin wayar da kan jama’a da neman a ɗauki matakin da ya dace.

Ta bayyana cewa cire bidiyon daga Instagram bai hana sauran kwafensa ci gaba da yawo a shafukan sada zumunta ba.

Amnesty ta nemi a yi bincike

Kun ji cewa kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International ta bukaci gwamnatin jihar Katsina da rundunar ’yan sanda su binciki Sarkin Daura kan zargin cin zarafi.

Kungiyar ta dauki wannan mataki ne biyo bayan zargin cin zarafin wata mata yar yawon bude ido daga kasar waje da aka alakanta da Sarkin Daura, Alhaji Faruk Umar Faruk.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262