Tinubu Ya Kawar da Shakkun 'Yan Najeriya, Ya Fadi Dalilinsa na Runtumo Basussuka
- Tinubu ya ce bai kamata a mayar da hankali kan yawan bashin da Najeriya ke karɓa kaɗai ba, sai dai amfanin da ake samu daga kuɗin wajen bunƙasa ƙasa
- Shugaban ƙasar ya bayyana manyan tituna, inganta wutar lantarki da zamanantar da tashoshin jiragen ruwa a matsayin muhimman ayyukan da za su ƙarfafa tattalin arziki
- Ya ce ana sa ran titin Legas-Calabar zai rage kuɗin sufuri da kashi 15 zuwa 20 cikin 100, tare da samar da dubban ayyukan yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya kare matakin gwamnatinsa na karɓar bashi daga cibiyoyin kuɗi da bankunan ƙasashen waje.
Shugaba Tinubu ya bayyana cewa ƙasar na buƙatar ci gaba da zuba jari a manyan ayyukan more rayuwa domin cimma burinta na tattalin arzikin dala tiriliyan ɗaya nan da shekarar 2030.

Source: Twitter
Mai ba shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, 29 ga watan Oktoban 2026 a shafinsa na X
Onanuga ya ce Tinubu ya yi wannan bayani ne a cikin wata makala mai taken “Daga sauye-sauyen tattalin arziki zuwa aiwatarwa: Dabarun zuba jari a more rayuwa da bunƙasa tattalin arziki.”
Jawabin shugaban ƙasar ya zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da sukar gwamnati kan yawan bashin da take karɓa da kuma tasirinsa ga nauyin bashin da ke kan Najeriya.
Tinubu ya fadi amfanin bashi
Tinubu ya ce ya kamata a duba irin ci gaban da ake samu daga kuɗin da aka karɓa a matsayin bashi, maimakon mayar da hankali kan adadin bashin kawai.
A cewarsa, abin da ya fi muhimmanci shi ne ayyukan da aka gudanar da kuɗin, ƙimar da aka samar da kuma irin makomar da za a bar wa al’umma.
Ya ce Najeriya ba za ta iya cimma burinta na tattalin arzikin dala tiriliyan ɗaya ba idan ba ta samar da muhimman ababen more rayuwa da suka dace da girman tattalin arzikin da take son ginawa ba.
Tinubu ya lissafo manyan ayyuka
Shugaban ƙasar ya lissafa manyan ayyukan da gwamnatinsa ke sa ran za su ƙarfafa tattalin arzikin Najeriya, ciki har da titin bakin teku na Legas-Calabar, babbar hanyar Sokoto-Badagry da kuma babbar hanyar Trans-Sahara.
Sauran ayyukan sun haɗa da inganta tsarin samar da wutar lantarki da zamanantar da manyan tashoshin jiragen ruwa na kasuwanci da ke Legas.
Tinubu ya ce waɗannan ayyuka, tare da zuba jari a fannin lafiya, ilimi da koyon sana’o’i, za su haɗa yankunan tattalin arziki, rage kuɗin jigilar kayayyaki da buɗe damar bunƙasa noma da masana’antu.
Ya ƙara da cewa ayyukan za su taimaka wajen jawo hankalin masu zuba jari daga kamfanoni masu zaman kansu.

Source: Facebook
Atiku ya soki shirin Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya soki shirin gwamnatin tarayya na biyan ma’aikatan gwamnati tallafin sufuri na N70,000 duk wata.
Dan takarar shugaban kasar na jam'iyyar ADC a zaben 2027, ya bayyana cewa matakin wucin gadi ne da ba zai magance matsin tsadar rayuwa a Najeriya ba.
Asali: Legit.ng

