Gwamna Ya Ja Hankalin Mutanen Daura kan Yadda Za Su Kare Tarihin Buhari a Zaben 2027

Gwamna Ya Ja Hankalin Mutanen Daura kan Yadda Za Su Kare Tarihin Buhari a Zaben 2027

  • Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda, ya yi kira ga al’ummar Daura su mara wa Shugaba Bola Tinubu da jam'iyyar APC baya a zaɓe mai zuwa
  • Ya buƙaci su kare tarihin marigayi Muhammadu Buhari ta hanyar zaɓen jam’iyyar mai mulki, domin dorawa daga inda marirgayin ya tsaya
  • Gwamna Radda ya bayyana takarar Yusuf Muhammadu Buhari, ɗan marigayi shugaban ƙasar, a matsayin muhimmin lamari ga martabar Daura

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Katsina, Nigeria - Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya yi kira ga al’ummar Daura da su mara wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu da jam’iyyar APC baya a zaben 2027 da ke tafe.

Gwamna Radda ya buƙaci al'ummar masarautar Daura su kare tarihin da marigayi Shugaba Muhammadu Buhari ya mutu ya bari ta hanyar zaɓen jam’iyya mai mulki a zaɓe mai zuwa.

Kara karanta wannan

Dikko Radda ya ziyarci Sardaunan Daura bayan dakatar da Sarki

Dikko Radda.
Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Radda yana jawabi a taron yakin neman zabensa a Daura Hoto: Ibrahim Kaula Mohammed
Source: Facebook

Daily Trust ta ruwaito cewa Gwamna Radda ya yi wannan kira ne a ranar Talata, 24 ga watan Nuwamba, 2026 yayin gangamin yaƙin neman zaɓen Tinubu da Dikko a karamar hukumar Daura.

Radda ya ja hankalin mutanen Daura

Mai girma gwamnan ya bayyana takarar Yusuf Muhammadu Buhari, ɗan marigayi tsohon shugaban ƙasar, a matsayin wani muhimmin lokaci da zai nuna martabar garin.

Ya ce:

“Daura ta nuna biyayya, jajircewa da ƙauna ga ubanmu kuma jagoranmu, marigayi Shugaba Muhammadu Buhari. Kada ku ɗauki wannan zaɓe da wasa, musamman batun takarar Yusuf Muhammadu Buhari.”

Gwamnan ya ce al’ummar Daura sun kasance tare da shi tun daga zaɓen fitar da gwani har zuwa babban zaɓe, tare da goyon bayan da ya bayyana a matsayin alaƙar amincewa da juna.

Dikko Radda ya kara da cewa:

“Na zama ɗan Daura ,kun karɓe mu, kun tsaya tare da mu kuma kun ba mu daraja. Za mu ci gaba da gode muku a kowane lokaci.”

Kara karanta wannan

"Aisha Buhari ta nuna wanda take goyon baya tsakanin Tinubu da Atiku a zaben 2027"

Ayyukan Dikko Radda a yankin Daura

Radda ya kuma tuna da aikin gina reshen gidan gwamnatin jiha a Daura da sauran ayyukan raya ƙasa da ake gudanarwa a matsayin hujjar irin kasancewar gwamnatinsa a garin.

Tun da farko, Darakta Janar na Kwamitin aƙin Neman Zaɓen Tinubu/Dikko, Ahmed Musa Dangiwa, ya gode wa al’ummar garin bisa karimcin da suka nuna wa tawagar yaƙin neman zaɓen a tsawon kwanaki 10 da ta shafe a yankin Daura.

Ya bukaci su ci gaba da marawa jam'iyyar APC mai mulki jaya domin ci gaba da gina ayyukan raya kasa da inganta rayuwar al'umma.

Gwamna Radda ya ziyarci Sardaunan Daura

Kun ji cewa Gwamna Dikko Radda ya ce kyakkyawar alaƙar da ke tsakanin Bola Tinubu da marigayi Muhammadu Buhari ta ƙarfafa zumuncin Fadar Shugaban Ƙasa da al’ummar Daura.

Radda ya bayyana hakan ne yayin ziyarar da ya kai gidan Sardaunan Daura, Alhaji Auwalu Umar Faruq, tare da tawagar yaƙin neman zaɓen Tinubu–Dikko–Jobe.

A yayin ziyarar, Radda ya ce tawagarsa ta zo ne domin gaisuwa, neman albarka da addu’o’in Sardaunan Daura da sauran dattawan yankin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262