Gwamnatin Tinubu Ta Fara Biyan Tallafin N50,000 duk Wata ga 'Yan Najeriya, an Ji Masu Amfana
- Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da shirin NERSI, wanda zai rika bai wa iyalai masu karamin karfi tallafin N50,000 duk wata
- Ma’aikatar jin kai ta ce ba sai mutum ya nemi tallafin ko ya biya kudi ba, domin za a tuntubi wadanda suka cancanta kai tsaye
- Gwamnati ta gargadi ‘yan Najeriya kan masu damfara, tare da bukatar su guji bayar da lambobin sirrin bankinsu da BVN
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya ta fara wani sabon shirin tallafin kudi da za ta rika bai wa iyalai masu karamin karfi N50,000 duk wata domin rage musu radadin tsadar rayuwa.
Ministan Jin Kai da Rage Talauci, Dakta Bernard Doro, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, 30 ga watan Oktoban 2026 a Abuja.

Source: Twitter
Kamar yadda Channels TV ta ruwaito, ministan ya ce shirin na karkashin wani sabon tsarin gwamnati mai suna National Emergency Relief and Stabilisation Intervention (NERSI).
Ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne ya kirkiro shirin domin samar da tallafin gaggawa ga miliyoyin ‘yan Najeriya da ke fama da matsin tattalin arziki.
Dalilin fara shirin tallafin N50,000
Doro ya ce an bullo da shirin ne sakamakon hauhawar farashin kayan abinci a kasuwannin duniya da kuma tsadar kayayyakin masarufi, lamarin da ke kara jefa iyalai cikin matsin rayuwa.
A cewarsa, gwamnatin na son rage wannan nauyi ta hanyar samar da tallafin kudi kai tsaye ga wadanda suka cancanta.
"Ta karkashin wannan shiri, wadanda suka cancanta za su rika samun N50,000 duk wata. Wannan zai taimaka musu wajen biyan bukatun yau da kullum da kuma rage musu nauyin tsadar rayuwa." In ji shi.
Ya kara da cewa za a rika duba yadda shirin ke gudana lokaci zuwa lokaci, domin yiwuwar sauya adadin tallafin bisa la'akari da yadda tsadar rayuwa ke sauyawa.
Doro ya ce idan aka samu wani sauyi a tsarin, za a sanar da wadanda abin ya shafa kai tsaye, jaridar The Punch ta kawo labarin.
Yadda za a samu kudin
Ministan ya bayyana cewa ma'aikatarsa na aiki tare da kamfanonin hada-hadar kudi ta intanet da gwamnati ta amince da su domin tabbatar da cewa an rika aika kudin cikin tsaro da gaskiya.
Ya ce kamfanonin za su rika tura sakonnin waya ga wadanda suka cancanta domin neman amincewarsu kafin a aika musu da kudin.
Bayan samun amincewar wadanda abin ya shafa, za a tura kudin kai tsaye zuwa asusun bankunansu ko kuma manhajojin ajiyar kudi ta wayar salula.
Sai dai ministan ya jaddada cewa ba a bukatar mutum ya cike takardar neman tallafin, ya biya wani kudi ko ya bi ta hannun wani wakili kafin ya amfana da shirin.
Gwamnati ta yi gargadi kan masu damfara
Doro ya kuma gargadi al'umma kan masu damfara da ka iya amfani da sabon shirin wajen yaudarar jama'a da karbar kudadensu.
Ya bukaci wadanda za su amfana da tallafin da kada su bai wa kowa lambobin sirrin bankinsu (PIN) ko lambar tantance asusun banki ta BVN.
Ministan ya ce duk wanda ya samu sakon da yake zargin ba na gaskiya ba ne, ko kuma wani ya nemi ya biya kudi kafin ya samu tallafin, ya tuntubi layin taimakon shirin ta lambar 0700-022-2222.

Source: Twitter
NLC ta caccaki TUC kan tallafin N70,000
A wani labarin kuma, kun ji cewa Ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya (NLC) ta caccaki takwararta, Ƙungiyar Ƙwadago ta TUC kan maganar tallafa wa ma'aikata.
NLC ta soki TUC ne bisa ƙin amincewa da alawus ɗin sufuri na N70,000 da aka cimmawa domin tallafa wa ma’aikata.
Asali: Legit.ng


