An Zo Matakin Karshe, Za a Turawa Mutane Hannun Jarin da Suka Saya a Matatar Dangote

An Zo Matakin Karshe, Za a Turawa Mutane Hannun Jarin da Suka Saya a Matatar Dangote

  • Hukumar SEC ta amince da tsarin rabon hannayen jarin matatar Dangote bayan tayin sayar da su (IPO) ya samu karbuwa
  • Matatar ta nemi izinin ƙara yawan hannayen jarin da ta ware domin sayarwa da kashi 30 cikin 100 saboda yawan masu son saye
  • Mutanen da suka biya kudi za su fara ganin hannayen jarin da suka saya a asusunsu na CSCS

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Lagos, Nigeria - Matatar mai ta Dangote ta samu amincewar ƙarshe daga hukumomin da ke kula da harkokin kasuwannin hannayen jari, gabanin fara hada-hada a kasuwar hannayen jari ta Najeriya (NGX).

Hukumar Kula da Kasuwannin Hannayen Jari (SEC) ta amince da tsarin rabon hannayen jarin matatar Dangote a ranar Litinin, 23 ga Nuwamba, 2026.

Dangote.
Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote Hoto: Dangote Group
Source: Getty Images

Ledership ta rahoto cewa hakan ya biyo bayan tayin sayar da hannayen jarin farko ga jama’a (IPO) ya samu karbuwa matuka, inda aka samu kusan nunki uku fiye da adadin matatar ta yi niyyar sayarwa.

Kara karanta wannan

Amurka ta kara sunayen 'yan Najeriya 24 cikin wasu 157 da za a fatattako daga kasar

Wannan amincewa ta kawo ƙarshen makonni na jiran sakamakon tayin da ƙananan masu zuba jari da manyan cibiyoyin zuba jari suka yi.

Hakan zai ba da damar saka hannayen jarin da aka saya a asusun masu zuba jari na Central Securities Clearing System (CSCS), mayar da kuɗin da suka yi saura da kuma fara cinikin hannayen jarin a kasuwar NGX.

Tayin sayar da hannayen jarin, wanda aka rufe a watan da ya gabata, ya samu buƙata kusan sau uku fiye da adadin da aka fara bayarwa.

Saboda yawan masu sha’awar sayen hannayen jarin, matatar ta kuma nemi amincewar hukumomi domin ƙara adadin hannayen jarin da za ta sayar da kashi 30 cikin 100.

An tsara wannan tayin, wanda aka yi wa laƙabi da “IPO na jama’a”, ne domin bai wa ’yan Najeriya dama su mallaki hannun jari a matatar Dangote tare da cin gajiyar ribar wannan kamfani mai darajar Dala biliyan 20.

Kara karanta wannan

Abubuwa 7 da ya kamata ku sani game da matar da ake zargin Sarkin Daura ya taɓa jikinta

An samu yawan masu zuba jari daga ciki da wajen Najeriya ta hanyar kamfanonin fasahar kuɗi da manhajojin saka hannun jari na zamani, inda mutum zai iya sayen mafi ƙarancin hannayen jari guda 10.

Dangote ya kuma bayyana shirin yiwuwar fara sayar da hannayen jarin kamfanin matatar a wata kasuwar hannayen jari ta biyu a Amurka cikin shekaru uku zuwa huɗu masu zuwa.

Matatar, wadda ke yankin Lekki Free Zone da ke wajen birnin Legas, tana da ƙarfin tace ganga 700,000 na mai a kowace rana.

Tun bayan fara aikinta a shekarar 2024, ta sauya yadda ake gudanar da harkokin samar da man fetur a Najeriya, tare da rage dogaro da shigo da tataccen mai daga ƙasashen waje.

Matatar ta kuma amfana da tangarɗar samar da mai a duniya da rikicin Iran ya haddasa, inda ta faɗaɗa fitar da kayayyakinta zuwa ƙasashen waje, ciki har da jigilar man jiragen sama zuwa Yammacin Turai.

Matatar Dangote ba ta cimma buri 1 ba

Kun ji cewa shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya bayyana cewa tayin hannun jarin matatar mansa bai cimma burin jawo masu zuba jari miliyan 10 ba.

Ya ce har yanzu ba a tantance a hukumance yawan mutanen da suka zuba jarin ba, amma ya danganta rashin cimma burin da ƙarancin lokacin da aka ba da damar sayen hannun jarin da kuma matsalolin da wasu suka fuskanta wajen shiga shirin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262