An Kama Mutum 3 kan Zargin Ƙona Motar Yan Tawagar Yakin Neman Zaben Jam'iyyar APC
- Rundunar ’yan sandan Katsina ta kama mutum uku da ake zargi da hannu a rikicin da ya barke a garin Yankara, inda aka ƙona motar APC
- Rikicin ya faru ne yayin da magoya bayan APC ke tafiya taron yaƙin neman zaɓen Tinubu-Dikko 2027 a Faskari
- ’Yan sanda sun ce ana ci gaba da bincike domin gano musabbabin rikicin da kuma kama sauran waɗanda suka tsere
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Katsina, Nigeria - Rundunar ’yan sandan Jihar Katsina ta kama mutum uku bisa zargin hannu a wani hari da aka kai wa magoya bayan APC a garin Yankara da ke Ƙaramar Hukumar Faskari.
An ruwaito vewa wasu bata-gari suka ƙona motoci da ke dauke da fastocin yan takarar APC, tare da jikkata mutane da dama da ake zaton suna cikin tawagar Gwamna Dikko Radda.

Source: Twitter
Leadership ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a ranar Asabar, 31 ga Oktoba, 2026, a daidai lokacin da ake samun tashin hankali a yankin, yayin da magoya bayan jam’iyyar APC ke tafiya taron yaƙin neman zaɓen Gwamna Dikko Umaru Radda a Faskari.
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa rikicin ya fara ne bayan samun saɓani tsakanin mahalarta jerin gwanon Mauludi da jami’an tsaro kan hanyar da aka ware.
Rahotanni sun ce lamarin ya rikide zuwa tashin hankali, inda wasu bata-gari suka kai hari kan motoci a kan hanya, suka ƙona motoci biyu, ciki har da motar ƙungiyar Musa Adamu Network (MAN), sannan suka lalata wasu shaguna.
An ƙona motar ƙungiyar MAN
Shugaban ƙungiyar MAN, Alhaji Nura Sule Yandaki, wanda ke jagorantar tawagar mambobi 12 zuwa taron yaƙin neman zaɓen Dikko Radda, ya ce sun tsinci kansu a cikin rikicin amma sun tsira ba tare da sun ji rauni ba, duk da cewa an lalata musu mota.
Wani jami’in ƙaramar hukuma ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce daga bisani jami’an tsaro suka shiga tsakani tare da dawo da zaman lafiya a yankin.
Yan sanda sun kama mutum uku
A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan Katsina, DSP Abubakar Sadiq Aliyu, ya ce tafiyar Gwamna Radda ta cikin Yankara ta kasance cikin kwanciyar hankali tun farko.
Ya bayyana cewa daga bisani ’yan sanda sun samu bayanin cewa wasu da ake zargin ’yan bangar siyasa ne sun tare hanya, suna jifan mutane da abubuwa tare da banka wa fastocin siyasa wuta.
A cewarsa, maharan sun kuma ƙona wata motar Sharon mallakar wani ɗan siyasa, wadda aka ajiye a gefen hanya bayan ta samu matsalar inji, yayin da direbanta ya wuce zuwa wurin taron.

Source: Facebook
Yadda yan sanda suka kai dauki
Kakakin ’yan sandan ya ce jami’in ’yan sanda na sashen Faskari, tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro, sun gaggauta zuwa wurin, suka tarwatsa dandazon mutanen tare da dawo da zaman lafiya.
Ya bayyana sunayen waɗanda aka kama a matsayin Garba Shu’aibu, mai shekaru 25; Salmanu Ibrahim, mai shekaru 18; da Nazifi Hussaini, mai shekaru 30.
Aliyu ya ce ana zargin mutanen uku da hannu a harin, inda ya ƙara da cewa ana ci gaba da bincike domin gano hakikanin abin da ya haddasa rikicin da kuma cafke sauran waɗanda suka tsere.
Yan sanda sun kama matasa 14
Kun ji cewa ’yan sandan jihar Katsina sun kama wasu mutane 14 da ake zargi da hannu a harkar daba ta siyasa.
An kama wadanda ake zargin ne bayan wani hari da aka kai wa ayarin magoya bayan APC da aka ruwaito suna cikin tawagar Gwamna Dikko Radda a kan hanyar Yashe zuwa Funtua.
Asali: Legit.ng


