Mahara Sun Bude Wuta kan Magoya Bayan NDC bayan Isowar Kwankwaso da Peter Obi
- An shiga yanayin tashin hankali a Benin City, jihar Edo, bayan wasu da ake zargin ’yan daba ne sun kai hari kan magoya bayan jam’iyyar NDC
- Magoya bayan sun taru ne a kan titin filin jirgi domin tarbar ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar, Peter Obi, da abokin takararsa, Rabiu Kwankwaso
- An ji karar harbe-harbe yayin da tawagar ’yan takarar ke barin filin jirgin sama zuwa wurin taron masu ruwa da tsaki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Edo, Nigeria - An shiga yanayin tashin hankali a Benin City, babban birnin jihar Edo, ranar Laraba bayan wasu da ake zargin ’yan daba ne sun kai hari kan magoya bayan jam’iyyar NDC.
Rahotanni sun nuna cewa ana zargin maharan sun farmaki mambobin NDC da suka taru a kan titin filin jirgin sama domin tarbar ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar, Peter Obi, da abokin takararsa, Rabiu Kwankwaso.

Source: Facebook
Obi da Kwankwaso sun isa filin jirgin saman Benin ne ta jirgin sama na kasuwanci, tare da wasu magoya bayan jam’iyyar NDC a Benin, kamar yadda Leadership ta ruwaito.
Kwankwaso da Obi sun ziyarci jihar Edo ne domin halartar taron masu ruwa da tsaki da aka shirya gudanarwa a matsayin wani ɓangare na shirye-shiryen zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
An ji karar harbe-harbe
Rahotanni sun ce yanayin ya fara dagulewa ne a ƙofar fita daga filin jirgin saman, inda aka ji karar harbe-harbe yayin da tawagar motocin da ke ɗauke da ɗan takarar shugaban ƙasa na NDC da mutanen da ke tare da shi suka nufi wajen taron.
Tawagar ta bar filin jirgin saman ne zuwa filin Baptist Convention Ground, wanda aka zaɓa a matsayin sabon wurin gudanar da taron masu ruwa da tsaki.
Zargin harin da aka kai wa magoya bayan NDC da ke jiran isowar ’yan takarar a kusa da titin Airport Road ya ƙara dagula yanayin tsaro a yankin, inda aka samu fargaba tsakanin mutanen da ke wurin.
Jami’an tsaro sun isa wurin
Sai dai, rahoton ya bayyana cewa jami’an tsaro sun kasance a wurin domin hana tabarbarewar lamarin da ka iya haifar da karya doka da oda.
Ba a bayyana ko akwai mutanen da suka samu raunuka ko kuma waɗanda aka kama dangane da zargin harin ba.
Haka kuma, ba a samu cikakken bayani kan waɗanda ake zargi da kai harin ko kuma dalilin da ya sa suka kai wa magoya bayan NDC hari ba.
Peter Obi ya yi tir da harin Kwankwaso
A wani labarin, kun ji cewa ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya yi Allah wadai da harin da aka kai wa ayarin motocin abokin takararsa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a Bichi.
Tsohon gwamnan ya nuna bacin ransa, ina ya bukaci rundunar ’yan sanda da sauran hukumomin tsaro su gaggauta gudanar da bincike tare da hukunta wadanda suka aikata laifin.
Asali: Legit.ng

