Zance Ya Kare, El Rufai Ya Tsage Gaskiya a gaban Kotu kan Zargin Kutse a Wayar Nuhu Ribadu
- Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya musanta zargin kutse da sauraron tattaunawar wayar NSA Nuhu Ribadu ko umartar wani ya yi hakan
- Ya bayyana kalamansa na wata hira da gidan talabijin a matsayin salon magana na siyasa, ba furucin amincewa da laifi ba
- Kotun Tarayya da ke Abuja ta buƙaci ya kare kansa bayan ta yi watsi da ƙoƙarinsa na neman a soke tuhumar saboda rashin isassun hujjoji
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya musanta cewa ya yi kutse da sauraron tattaunawar wayar mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Nuhu Ribadu, ko kuma ya nemi wani ya yi hakan.
El-Fufai ya bayyana haka ne yayin da yake bayar da shaida a shari’ar da ake yi masa kan zargin satar bayanan waya a gaban Kotun Tarayya da ke Abuja ranar Laraba.
Premium Times ta rahoto cewa El-Rufai ya shaida wa kotu cewa bai taɓa mallakar na’urorin da ake amfani da su wajen kutsen waya ba, kuma ba shi da ilimin fasaha kan yadda ake yin hakan.
Yayin da lauyansa, Paul Erokoro, Babban Lauya a Najeriya (SAN), ke yi masa tambayoyi, tsohon gwamnan ya kuma musanta cewa yana da damar shiga hanyoyin sadarwa ko na’urorin NSA.
Ya dage cewa kalaman da ya yi yayin wata hira da gidan talabijin na Arise a watan Fabrairu salon magana ne na siyasa, ba wai amincewa da cewa ya kutsa cikin wayar Ribadu ba.
Ya ce:
“Na yi amfani da kalmar ‘mu’ ne ina nufin ’yan siyasar adawa. Lokacin da na ce mun saurari wayarsu, ƙarin gishiri ne a cikin magana da nufin sa gwamnati ta ji irin radadin da muke ji.
“Salon magana ne na jan hankali da ƙara gishiri. Burina shi ne in mayar da martani na siyasa tare da amfani da kalamai masu armashi.”
Shari’ar ta samo asali ne daga wata hira da El-Rufai yabyi a ranar 13 ga Fabrairu, kwana guda bayan jami’an tsaro sun yi ƙoƙarin kama shi a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, bayan dawowarsa daga ƙasar Masar.
A yayin hirar, El-Rufai ya zargi Ribadu da bayar da umarnin a kama shi. Ya ce ya san da umarnin ne saboda shi da wani mutum da bai bayyana sunansa ba sun saurari tattaunawar waya inda NSA ya umarci jami’an tsaro su kama shi.
Bayan hirar, Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (SSS) ta shigar da tuhume-tuhume uku a kansa, waɗanda daga baya aka gyara tare da ƙara su zuwa guda biyar.
Bayan El-Rufai ya musanta dukkan tuhume-tuhume biyar, masu gabatar da ƙara sun gabatar da shaidu biyu. Sun kammala gabatar da shari’arsu a watan Yuni.
Saboda haka, kotun ta umarci El-Fufai da ya fara kare kansa, wanda ya fara yi a yau Laraba, inda ya musanta yi wa wayar Nuhu Ribdu kutse.
Asali: Legit.ng

