Abubuwan da Ya Kamata Ku Duba kafin Sayen Wayoyin Hannu saboda Dokar NCC a Najeriya
- Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) ta shawarci ’yan Najeriya da su tantance wayoyin hannu kafin saye domin tabbatar da cewa an amince da su
- Hukumar ta ce masu sayen waya za su iya duba matsayinta ta hanyar danna lambar *315# ko amfani da shafinta na intanet
- NCC ta bayyana cewa tantance waya na taimakawa wajen guje wa sayen jabun wayoyi da gano ko waya ce ke haddasa matsalar sadarwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) ta shawarci ’yan Najeriya da su tantance wayoyin hannu kafin saye domin tabbatar da cewa an amince da amfani da su kafin su saya.
Hukumar ta ce masu shirin sayen waya za su iya bincika matsayinta ta hanyar danna lambar *315# ko amfani da na’urar tantance wayoyi da ke shafinta na intanet.

Kara karanta wannan
Babbar magana: Ana shirin amfani da makami mafi haɗari bayan nukiliya a yaƙin Amurka da Iran

Source: Getty Images
Daraktan NCC mai kula da ƙa’idojin fasaha da ingancin hanyoyin sadarwa, Eduyemi Ogoh, ya bayyana hakan a shirin Newsnight na gidan talabijin na Arise.
Abin da ya kamata ku duba
Ya ce wannan tantancewa na da matuƙar muhimmanci, musamman ga masu sayen wayoyin da aka yi amfani da su a baya ko waɗanda aka shigo da su daga wasu ƙasashe.
Ya ce:
“Kafin ka sayi waya, danna *315# ka tabbatar an tantance wayar yadda ya kamata kafin ka biya kuɗinta.”
Ogoh ya bayyana cewa an ƙirƙiri tsarin tantance wayoyi ne domin cika nauyin da dokar hukumar ta ɗora mata ƙarƙashin Dokar Sadarwa ta Najeriya ta 2003, kare masu amfani da kayayyaki.
“Babban manufar amincewa da nau’in na’ura ita ce tabbatar da cewa kowace na’urar sadarwa da aka shigo da ita ƙasar sahihiya ce kuma tana aiki yadda ya kamata," in ji Ogoh.
Dalilin NCC na kirkiro tsarin tantancewa

Kara karanta wannan
Dalla dalla: Yadda za ka duba wayarka ta cika sharaɗin NCC domin kada a rufe maka ita
Ya ce an tsara wannan mataki ne domin taimaka wa masu saye su guji kashe kuɗinsu wajen sayen jabun wayoyi ko waɗanda aka kwaikwaya maimakon na asali.
Ya ƙara da cewa ya kamata masu sayen waya su iya tantance sahihancinta da kuma ko ta cika ƙa’idojin hukumar kafin kammala sayen ta.
Ogoh ya ce hukumar ta gano wasu lokuta da koke-koken ƙarancin ingancin ayyukan sadarwa suka samo asali daga wayoyin da ake amfani da su, ba daga hanyoyin sadarwar kamfanonin ba.
Domin tantance waya, ana buƙatar mai saye ya danna *315# sannan ya bi umarnin da aka bayar domin shigar da lambar IMEI, wadda ita ce lambar musamman da ake bai wa kowace waya.
Masu shirin sayen waya za su iya neman lambar IMEI daga hannun mai sayarwa sannan su kammala tantancewar kafin biyan kuɗi.

Source: Twitter
Sai dai Ogoh ya fayyace cewa idan waya ta gaza tantancewa, hakan ba yana nufin kai tsaye cewa jabun waya ce ba. Ya bayyana cewa amincewa da nau’in na’ura da tantance waya matakai ne biyu masu manufar daban.
Ya ce amincewa da nau’in na’ura ya ƙunshi gwajin samfurin waya a dakin gwaje-gwaje domin tabbatar da cewa ta cika ƙa’idojin fasaha da ake buƙata, kuma za ta iya aiki yadda ya kamata a hanyoyin sadarwar Najeriya.
NCC ta kawo ssbon tsari a Najeriya
Kun ji cewa hukumar NCC ta fara tantance sahihancin na'urorin da ke amfani da katin SIM kamar wayoyin hannu domin gano na jabu da waɗanda ba su cika ƙa'idoji ba
Hukumar ta ce matakin zai taimaka wajen inganta ayyukan sadarwa da kuma kare masu amfani da na'urori marasa inganci
Asali: Legit.ng
