Yadda Ake Duba Cancantar Samun Tallafin N50,000 duk Wata na Gwamnatin Tarayya

Yadda Ake Duba Cancantar Samun Tallafin N50,000 duk Wata na Gwamnatin Tarayya

  • OPay ya ce waɗanda suka cancanci tallafin Naira 50,000 za su ga saƙon sanarwa a shafin farko na manhajarta
  • Kamfanin ya jaddada cewa rashin ganin sanarwar a manhajar na nufin mutum bai cancanci tallafin ba
  • Gwamnati ta ce ba a buƙatar neman tallafin, biyan kuɗi ko yin rajista ta hannun wakilai, tare da gargaɗin jama’a kan masu damfara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Kamfanin OPay ya bayyana yadda abokan cinikinsa za su tantance ko sun cancanci samun tallafin kuɗi na Naira 50,000 duk wata da gwamnatin tarayya ta ƙaddamar domin taimaka wa ’yan Najeriya masu ƙaramin ƙarfi.

Kamfanin ya yi gargaɗin cewa ba kowane mutum ne zai samu tallafin ba, domin an ware shi ne kawai ga mutanen da suka cika sharuddan da aka gindaya.

Kara karanta wannan

Abubuwan da ya kamata ku sani game da tallafin N50,000 da aka fara turawa mutane a Najeriya

Gwamnatin Tinubu na bayar da tallafi
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Yadda ake tantance cancantar samun tallafin

Jaridar The Punch ta ce hakan na kunshe ne a cikin wani saƙo da kamfanin ya wallafa a ranar Talata, 3 ga watan Nuwamban 2026.

OPay ta ce mutanen da suka cancanci tallafin za su ga saƙon sanarwa da zai bayyana a shafin farko na manhajarta, wanda za su danna domin bin matakan da ake buƙata.

Kamfanin ya bayyana cewa mutanen da ba su ga sanarwar a manhajarsu ba, ba su cikin waɗanda suka cancanci samun tallafin.

Kamfanin ya kuma jaddada cewa ba shi ne ke tantance mutanen da za su ci gajiyar tallafin ba.

A cikin sanarwar, OPay ta ce:

“Tallafin kuɗi na Naira 50,000 duk wata da gwamnatin tarayya ke bayarwa yana samuwa ne kawai ga ’yan ƙasar da suka cancanta.
“Mutanen da suka cancanci tallafin za su ga saƙon sanarwa a shafin farko na manhajarsu ta OPay. Da fatan za ku danna sanarwar domin bin matakan da suka dace.

Kara karanta wannan

"Zan samar da irin Dangote 20 cikin shekara 4"; Dan takarar shugaban kasa ya fadi shirinsa

“Ku sani cewa abokan cinikin da ba su ga wannan sanarwa a manhajarsu ba, ba su cancanci tallafin ba. Ku kuma lura cewa ba mu ne ke tantance cancantarku ba. Ku tuntuɓi NERSI ta lambar 07000222222 domin samun taimako.”

OPay ya gargaɗi jama’a kan masu damfara

Kamfanin ya kuma gargaɗi abokan cinikinsa da su yi hattara da masu damfara da za su iya neman kuɗi ko bayanan sirrinsu da sunan taimaka musu wajen samun tallafin.

OPay ya bayyana cewa ba za ta taɓa neman lambar sirrin asusun kwastoma (PIN) ko lambar tabbatar da ciniki ta lokaci guda (OTP) domin aiwatar da biyan kuɗin tallafin NERSI ba.

“OPay ba za ta taɓa neman PIN ko OTP ɗinku domin aiwatar da biyan kuɗin tallafin NERSI ba. Kada ku biya wani wakili ko ku danna hanyoyin intanet da ba a tabbatar da sahihancinsu ba.”

Kamfanin ya shawarci kwastomominsa da su yi amfani da manhajarsa ko lambar USSD ta 95520# kawai domin tantance cancantarsu.

Gwamnati ta fara shirin tallafin N50,000

Gwamnatin tarayya ta sanar da fara rabon tallafin kuɗin ne a ƙarƙashin shirin National Emergency Relief and Stabilisation Intervention (NERSI), wanda wani shiri ne na shugaban ƙasa domin tallafa wa gidaje masu fama da matsin tattalin arziki.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta fara biyan tallafin N50,000 duk wata ga 'yan Najeriya, an ji masu amfana

Ministan Harkokin Jin ƙai da Rage Talauci, Dakta Bernard Doro, ne ya bayyana fara shirin a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar 30 ga Oktoba, 2026.

Ministan ya ce mutanen da suka cancanta za su riƙa samun Naira 50,000 duk wata domin taimaka musu wajen biyan buƙatun yau da kullum da rage musu tasirin hauhawar farashin kayayyaki.

Ya kuma bayyana cewa za a riƙa duba shirin lokaci zuwa lokaci domin tabbatar da ingancinsa.

Hanyoyin samun tallafin da aka amince da su

A cewar ministan, ma’aikatarsa na aiki tare da kamfanonin hada-hadar kuɗi na zamani da ke da lasisi domin tabbatar da cewa ana raba kuɗin cikin aminci da gaskiya.

Ya ce kafin a tura kuɗin, waɗanda suka cancanta za su fara samun saƙon SMS domin neman izininsu. Bayan sun amince, za a tura kuɗin kai tsaye zuwa asusun bankinsu ko walat ɗin wayarsu.

Gwamnati ta amince da waɗannan kamfanoni da lambobin USSD domin tantance cancanta da amfani da ayyukansu: ALAT by Wema — 94523# MoMo PSB — 6710# NairaGram — 72600# OPay — 95520# Moniepoint — 557327#

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun yi magana kan sace dan takarar shugaban kasa, sun fadi abin da ya faru

Doro ya jaddada cewa babu buƙatar cike takardar neman tallafi, biyan kuɗi ko yin rajista ta hannun wani wakili.

Ya kuma buƙaci ’yan Najeriya da kada su bai wa kowa lambobin sirrinsu na PIN ko BVN, tare da kira gare su da su tuntuɓi layin taimakon NERSI mai lamba 0700-022-2222 idan suna da shakku kan wani saƙon da suka samu.

Gwamnatin Tinubu ta fara bada tallafi
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Gwamnatin Tinubu ta raba kudade

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta sanar da cewa ta kammala fitar da Naira biliyan 75 ga masu masana'antu 104, yayin da ta raba Naira biliyan 65.8 ga ƙananan 'yan kasuwa 15,018 a faɗin Najeriya.

Gwamnati ta ɗauki matakin ne domin ƙarfafa samar da kayayyaki a cikin gida, faɗaɗa harkokin kasuwanci da samar da guraben ayyukan yi ga 'yan Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng