Jerin Wadanda Gwamnatin Tarayya ba Za Ta Turawa Tallafin N70,000 duk Wata a Najeriya ba

Jerin Wadanda Gwamnatin Tarayya ba Za Ta Turawa Tallafin N70,000 duk Wata a Najeriya ba

Amincewar gwamnatin tarayya da biyan ma’aikatan N70,000 duk wata a matsayin tallafin sufuri na tsawon watanni shida ta jawo tambayoyi kan wadanda za su amfana.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Tun bayan cimma matsayar raba wannan tallafi, yan Najeriya suka fara tambayoyi kan ko ma'aikatan da ke aiki a karkashin gwamnatocin jihohi, kamfanoni da yan kasuwa za su amfana.

Bola Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu yana rattaba hannu a fadar gwamnatin tarayya da ke Abuja Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Leadership ta rahoto cewa an cimma yarjejeniyar tallafin ne bayan takaddama tsakanin gwamnatin tarayya da Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya (NLC) kan walwalar ma’aikata, tsadar rayuwa da wasu buƙatu da ba a biya ba.

Bangarorin biyu sun cimma matsaya a wani taron sasanci da aka gudanar a Abuja ranar Talata, 27 ga Oktoba, 2026, inda suka amince da biyan tallafin sufuri na wata-wata na tsawon watanni shida.

Ana sa ran za a fara biyan wannan tallafi na N70,000 daga watan Nuwamba domin rage wa ma’aikata raɗaɗin tsadar rayuwa.

Kara karanta wannan

Atiku ya nuna adawa da shirin Tinubu na tallafawa ma'aikata da N70,000

Duk da cewa yarjejeniyar ba ta sanya iyakar shekaru ko mafi ƙarancin shekarun ƙwarewar aiki da mutum zai kasance da su kafin ya amfana ba, har yanzu akwai tambayoyi kan rukunin ma’aikatan da suka cancanci samun tallafin.

Ga wasu rukunin ma’aikatan da ba a tabbatar za su amfana da tallafin ba.

1. Ma’aikatan gwamnatocin jihohi

Har yanzu ba a fayyace ko ma’aikatan gwamnatocin jihohi za su amfana da tallafin ba, bisa yarjejeniyar da gwamnatin tarayya ta cimma da NLC.

Ko da yake yarjejeniyar ta yi magana kan aiwatar da matakin a dukkan matakan gwamnati, ta kuma bukaci gwamnatocin jihohi su shiga cikin shirin.

Saboda haka, ma’aikatan jihohi na iya buƙatar jiran ƙarin bayani daga gwamnatocinsu domin sanin ko za a aiwatar da tallafin a jihohinsu.

2. Ma’aikatan ƙananan hukumomi

Har yanzu ba a fayyace cancantar ma’aikatan ƙananan hukumomi wajen samun tallafin ba.

Yarjejeniyar ta yi kira ga ƙananan hukumomi su shiga wannan tssri, amma ba ta bayyana cikakken tsarin yadda za a aiwatar da shi ga ma’aikatansu ba.

Don haka, ma’aikatan ƙananan hukumomi na buƙatar sanya ido kan sanarwar hukuma daga hukumominsu domin sanin ko za a biya su tallafin.

Kara karanta wannan

Abubuwa 10 da ya kamata ma'aikata su sani kan tallafin N70,000 duk wata

3. Ma’aikatan kamfanoni masu zaman kansu

Ma’aikatan kamfanoni masu zaman kansu ba sa cikin rukunin waɗanda aka ambata a matsayin waɗanda za su amfana da yarjejeniyar da gwamnatin tarayya ta cimma da NLC.

An cimma matsayar ne a tattaunawar da ta shafi walwalar ma’aikatan gwamnati, don haka yarjejeniyar ba ta wajabta wa masu kamfanoni biyan ma’aikatansu tallafin sufuri na N70,000 duk wata ba.

4. ’Yan kasuwa da masu sana’o’in kansu

’Yan kasuwa, masu sana’o’in hannu, masu ƙananan kasuwanci da sauran ’yan Najeriya masu dogaro da sana’o’insu ba a bayyana su kai tsaye a matsayin waɗanda za su amfana da tallafin ba.

Yan kwadago.
Shugabannin manyan kungiyoyin kwadago na Najeriya, NLC da TUC a taron ranar ma'aikata ta duniya Hoto: NLC Nigeria
Source: Twitter

Wannan mataki na gwamnati ya shafi ma’aikatan gwamnati ne, maimakon zama tallafin kuɗi ga dukkan ’yan Najeriya da tsadar sufuri ta shafa.

Saboda haka, waɗanda ba sa cikin ma’aikatan gwamnati ya kamata su jira ƙarin bayani daga hukumomin da abin ya shafa kafin su tabbatar ko suna cikin waɗanda za su amfana da shirin.

TUC ta yi watsi da tallafin N70,000

Kara karanta wannan

Wahalar rayuwa: Gwamnatin Tinubu ta ware N70,000 ga ma'aikata duk wata

A wani labarin, kun ji cewa ƙungiyar ƙwadago ta TUC ta yi watsi da tallafin sufuri na N70,000 da gwamnatin tarayya ta amince za ta biya ma'sikata duk wata.

Ƙungiyar ta bukaci a ƙara mafi ƙarancin albashin ma’aikatan tarayya daga N70,000 zuwa N300,000, tare da daidaita albashin sauran ma’aikata

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262