Gwamnatin Tinubu Ta Sauya Salo, Ta Amince da Wani Tsari da Talakawa Za Su Amfana a Najeriya
- Majalisar Zartarwa ta Tarayya ta amince da sabon tsarin haɗa ayyukan agajin jin ƙai, tallafin zamantakewa da shirye-shiryen yaƙi da talauci
- Tsarin zai taimaka wajen tabbatar da cewa ’yan Najeriya masu rauni sun samu tallafi cikin tsari guda domin tsamo su daga talauci
- Gwamnati ta ce za a haɗa tsare-tsaren agajin gaggawa da shirye-shiryen ilimi, koyon sana’o’i da samar da hanyoyin dogaro da kai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) ta amince da wani sabon tsarin ƙasa da aka tsara domin yaƙi da talauci ta hanyar haɗa ayyukan agajin jin ƙai, tallafin zamantakewa da shirye-shiryen rage talauci a ƙarƙashin tsari guda.
Sabon tsarin, wanda aka sanya wa suna One Humanitarian One Poverty Response System (OHOPRS), na da manufar inganta ayyukan yaki da talauci a fadin Najeriya.

Source: Facebook
Jaridar Punch ta ruwaito cewa tsarin zai inganta haɗin gwiwa tsakanin hukumomin gwamnati, abokan hulɗa da ƙungiyoyin agaji, domin tabbatar da cewa ’yan Najeriya masu rauni sun samu tallafin da ya dace cikin tsari.
Ministan Harkokin Jin Ƙai da Rage Talauci, Dakta Bernard M. Doro, ne ya gabatar da shawarar ga majalisar, wadda ta amince da ita a ranar Laraba.
A cikin wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar a ranar Alhamis, ta bayyana cewa OHOPRS na daga cikin muhimman ginshiƙan shirin Shugaba Bola Tinubu na Renewed Hope Agenda.
Ta ce gwamnatin tarayya na son amfani da shi wajen fitar da miliyoyin ’yan Najeriya daga kangin talauci.
Dalilin ƙirƙirar sabon tsarin
Ma’aikatar ta bayyana cewa a baya, shirye-shiryen rage talauci, tallafin zamantakewa da ayyukan agajin jin ƙai sun kasance suna gudana ne daban-daban.
A cewarta, hakan ya haifar da maimaita wasu ayyukan tallafi, rashin isa ga wasu mutanen da suke buƙatar taimako da kuma matsalolin taimaka wa iyalai su fita daga dogaro da agajin gaggawa zuwa samun damar farfaɗowa da dogaro da kai.

Kara karanta wannan
Isa Ashiru ya fito da gaskiyar zance bisa zargin ya fallasa El Rufai kan rashin tsaro a Kaduna
Saboda haka, an tsara OHOPRS ne a matsayin babban sauyi a tsarin gudanar da ayyukan tallafi, ba wai wani sabon shiri na daban da zai gudana shi kaɗai ba.
Yadda tsarin zai taimaka
A ƙarƙashin tsarin, iyalan da rikice-rikice ko wasu matsalolin gaggawa suka raba da muhallansu za su ci gaba da samun agajin gaggawa, ciki har da abinci, matsuguni da kula da lafiya.
Sai dai ba za a tsaya ga wannan tallafi kawai ba, domin za a haɗa su da shirye-shiryen tallafin zamantakewa, ilimi, koyon sana’o’i da taimakon hanyoyin samun abin dogaro da kai.

Source: Twitter
Doro ya ce,
"Na daɗe ana gudanar da ayyukan agajin jin ƙai, tallafin zamantakewa da rage talauci a matsayin shirye-shirye daban-daban. OHOPRS zai haɗa su wuri guda, a taimaka wa ’yan Najeriya masu rauni a tsarin da zai kai su ga farfaɗowa, juriyar fuskantar matsaloli da ’yancin tattalin arziki.”
Gwamnatin Tinubu ta dage kan yakar talauci
Kun ji cewa Gwamnatin tarayya ta ƙaddamar da wani shiri na rage talauci da ke da burin taimaka wa ’yan Najeriya miliyan biyar cikin shekaru huɗu masu zuwa.
Shirin na da nufin magance rashin aikin yi, rage gibin ƙwarewa da kuma samar wa waɗanda za su amfana da kayan aikin da za su taimaka musu kafa sana’o’i da shiga harkokin tattalin arzikin zamani.
Asali: Legit.ng
