Sheikh Ibrahim Aliyu Kaduna Ya Nemi a Ba Shi Kwangilar Magance Daba a Kano

Sheikh Ibrahim Aliyu Kaduna Ya Nemi a Ba Shi Kwangilar Magance Daba a Kano

  • Sheikh Ibrahim Aliyu Kaduna ya yi kira ga gwamnonin jihohi su tashi tsaye domin yaki da daba da sauran laifuffuka a jihohinsu
  • Malamin bayyana cewa hakki ne a kan jihohi su tabbatar da cewa sun ba matasa tarbiyya domin su zama manyan gobe na gari
  • Sheikh Kaduna ya kalubalanci gwamnatin Kano ta ba shi kwangilar yaki da daba domin yana da tabbacin zai taka rawa a magance matsalar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna - Malamin addinin Musulunci, Sheikh Ibrahim Aliyu Kaduna ya koka kan yadda matsalar daba ta ki-ci-ta-ki-cinyewa a Arewacin Najeriya.

Malamin ya bukaci gwamnatin Kano da ta bashi kwangiyar magance 'yan daba da suka addabi jihar da sace-sacen waya da sauransu.

Ibrahim Aliyu Kaduna
Sheikh Ibrahim Kaduna yayin wani wa'azi. Hoto: Ibrahim Aliyu Kaduna
Source: Facebook

Legit Hausa ta tattaro bayanan da Sheikh Ibrahim Aliyu Kaduna ya yi ne a wani bidiyon da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

2027: Fadar shugaban kasa ta yi magana kan barazanar kashe Peter Obi

Magana kan tarbiyya

Sheikh Ibrahim Aliyu Kaduna ya yi magana kan magance daba ne yayin da ya ke gabatar da wani wa'azi kan tarbiyya a jihar Neja.

Yayin da ya fadi wadanda nauyin tabbatar da tarbiyya ke kansu, ya ce hukumomi suna da alhakin tabbatar da tarbiyya a jihohi.

Ya ce idan gwamnati ba ta shigo cikin tarbiyyar ba, al'umma lalace wa ta ke. Ya ce idan ba a hada addini da tsarin kasa ba, ba za a taba ganin cigaba ba.

Lokacin da ya bukaci a saka tsarin tarbiyya a mulkin kasa, ya ce idan aka ce babu batun Allah a cikin lamarin tafiyar da kasa to ba za a taba ganin cigaba ba, domin Allah ne ya halicci mutane ya tsara yadda za su rayu.

Batun magance daba a Kano

Sheikh Ibrahim Aliyu Kaduna ya bayyana cewa gwamnatocin jihohi suna da ikon magance matsalar daba matukar suna da niyyar yin hakan.

Kara karanta wannan

Ma'aikatar bogi: Kujerun manyan jami'an Tinubu na rawa, ana kira a kore su

Ya bayyana cewa idan aka ba shi kwangilar magance matsalar zai taka muhimmiyar rawa:

"Ina kira ga gwamnatin Kano ta ban kwangilar dakatar da fadan daba, a ban dama, a sakan min komai.

Daga cikin matakan da ya nuna cewa zai dauka, malamin ya ce:

"Idan na casa su yau, na casa su gobe, babu mai fitowa jibi."
Abba Kabir Yusuf
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf a ofis. Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Abin da ya faru a Kaduna

Malamin ya bayar da misali kan yadda tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i ya magance wasu 'yan daba da suka fito masu suna 'yan shara.

Ya bayyana cewa 'yan shara da suka fito a Kaduna sun hana mutane sakat, suna saran mutane da adduna, suna kashe jama'a.

Sheikh Kaduna ya ce a lokacin, Nasir El-Rufa'i ya bayyana cewa tsohon gwamnan ya bukaci a tura duk wanda aka kama fursuna, idan uban shi ya zo shi ma a kama shi.

Ya kara da cewa dole gwamna ya tashi tsaye wajen dakile matsalolin su, inda ya ce abin Allah wadai ne:

Kara karanta wannan

Da gaske auren Laylah da dan majalisa Yusuf Gagdi ya mutu?

"Gwamna ya zama kamar budurwa, Gwamna kamar budurwa."

Maganar Sheikh Rijiyar Lemo

A wani labarin, mun kawo muku cewa malamin Musulunci a Kano, Farfesa Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo ya yi kira kan magance 'yan daba.

Malamin ya bayyana cewa dole gwamna Abba Kabir Yusuf ya tashi tsaye wajen magance matsalolin daba da suka addabi al'ummar jihar.

Dangane da hada kai, malamin ya bayyana cewa jami'an tsaro na matukar kokari kuma suna bukatar hadin kan sauran hukumomi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng