Dr. Usman Bugaje ya bayyana abin da ya sa ake ficewa daga APC zuwa PDP

Dr. Usman Bugaje ya bayyana abin da ya sa ake ficewa daga APC zuwa PDP

Mun samu labari cewa wani tsohon ‘Dan Majalisar Wakilai ta Tarayya watau Hon. Usman Bugaje yayi magana game da sauya-shekan da wasu manyan ‘Yan siyasar kasar su ke yi kwanan nan.

Dr. Usman Bugaje ya bayyana abin da ya sa ake ficewa daga APC zuwa PDP
Usman Bugaje yace akwai gyara a tafiyar siyasar kasar nan

Usman Bugaje ya nuna cewa rashin manufofi a-zo-a-gani na Jam’iyyun ya sa wasu ‘Yan Majalisar da ke APC su ka tattara su ka dawo PDP kwanaki. Bugaje yace ana amfani da Jam’iyyun ne kurum wajen cin zabe amma ba su da akida.

Bayan rashin dasasshiyar akida kuma dai tsohon ‘Dan Majalisar na Katsina ya nuna cewa Jam’iyyar ba tayi wani aiki na kwarai ba don haka yake yi wa ‘Ya ‘yan ta saukin sauya-sheka. Yace a wasu kasashen dai barin Jam’iyya na da wahala.

Dr. Usman Bugaje da yake wannan jawabi a cibiyar ITN a Garin Zariya lokacin da ya gabatar da takarda a karshen makon can yace Shugabannin APC ba su yi abin da ya dace tun farko ba wajen ganin an dinke barakar da ke cikin Jam’iyyar.

KU KARANTA: Buhari ya aika wata Runduna zuwa Garin Zamfara cikin gaggawa

Bugaje wanda ya goge a siyasa tun ba yau ba, ya ba jama’a shawara cewa su daina kallon Jam’iyyar da mutum ya fito takara illa iyaka a duba ‘Dan takarar. Bugaje ya koka da cewa wanda ya fi kudi ba wai kwarewa ba shi ne zai lashe zabe.

Kwanaki kun ji labari cewa Hon. Aliyu Gebi wanda yana cikin masu burin maye gurbin Sanata Ali Wakili da ya rasu kwanaki a Majalisa ya janye takarar sa. Gebi ya hakura saboda yadda aka tsawwala kudi kafin mutum ya samu tikiti.

Sanata Rabiu Kwankwaso wanda yana cikin wadanda su ka bar APC kwanan nan yayi kira da babban murya ga Gwamnatin Buhari ta shawo kan kashe-kashen Zamfara da ake yi kamar yadda ku ka ji dazu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng