Trump Ya Rattaba Hannu kan Dokokin da Za Su Kawo Cikas ga 'Yan Najeriya da Wasu Kasashe

Trump Ya Rattaba Hannu kan Dokokin da Za Su Kawo Cikas ga 'Yan Najeriya da Wasu Kasashe

  • Shugaba Donald Trump ya sanya dokokin zartarwa guda biyu da ke ƙoƙarin takaita zama ɗan ƙasar Amurka ga wasu jarirai da kuma ƙara
  • Sababbin dokokin sun shafi 'ya'yan wasu ma'aikatan diflomasiyya na ƙasashen waje, mutanen da aka ayyana a matsayin maƙiyan ƙasa da kuma mata da suka shiga Amurka da nufin haihuwa kawai
  • Ana sa ran za a ƙalubalanci dokokin a kotu saboda masu suka na ganin sun saɓa wa Kwaskwarimar Kundin Tsarin Mulki ta 14

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Washington, D.C. – Shugaban Amurka, Donald Trump, ya sanya hannu kan dokokin zartarwa guda biyu a ranar Alhamis, 6 ga watan Agustan 2026.

Trump ya sanya hannu kan dokokin ne da nufin takaota samun zama ɗan ƙasar Amurka ta hanyar haihuwa a wasu yanayi tare da ƙara tsaurara matakan gwamnatin tarayya kan abin da ake kira 'yawon zuwa haihuwa'.

Kara karanta wannan

Dalilin Najeriya na bude ƙofar tuba ga 'yan bindiga a Najeriya

Trump ya rattaba hannu kan doka
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Tashar Axios ta kawo rahoton sanya hannu kan dokokin da Shugaba Trump ya yi a ranar Alhamis, 6 ga watan Agustan 2026.

Haka kuma Trump na ƙoƙarin hana ba da zama dan ƙasar Amurka kai tsaye ga yaran da wasu ma'aikatan diflomasiyyar ƙasashen waje da ke aiki a Amurka za su haifa, kuma hakan na iya shafar yankunan Amurka idan doka ta ba da dama a nan gaba.

Kotun koli ta yi watsi da tsohon umarnin Trump

A ranar 30 ga Yuni, Kotun Kolin Amurka ta yi watsi da wani umarnin zartarwa da Trump ya sanya a ranar rantsar da shi kan mulki, wanda ya nemi hana ba da zama ɗan ƙasa kai tsaye ga yaran da baƙin haure marasa izinin zama 'yan ƙasa suka haifa a Amurka.

Sai dai gwamnatin Trump ta ce hukuncin kotun ya bar mata damar amfani da wasu tsofaffin keɓantattun tanade-tanade da kotu ta amince da su domin takaita wannan tsarin.

Kara karanta wannan

Akwai ladar N60m: Sojoji sun saki hotuna da bayanan 'yan ta'adda 2 da ake nema

Rukunan da sabbin dokokin suka shafa

Sabbin dokokin za su shafi haihuwar da za ta faru nan gaba a cikin rukuni huɗu:

Yaran da wasu ma'aikatan diflomasiyyar ƙasashen waje da ke aiki a madadin gwamnatocinsu a Amurka za su haifa.

Dokar ta kuma shafi yaran mutanen da aka ayyana a matsayin maƙiyan ƙasa, ciki har da waɗanda ke da alaƙa da ƙungiyoyin da gwamnatin tarayya ta ayyana a matsayin ƙungiyoyin ta'addanci.

Sabon umarnin ya kuma shafi waɗanda aka haifa a yankunan Amurka, amma hakan zai fara aiki ne kawai idan Majalisa ta sauya doka domin kawo ƙarshen ba da zama ɗan ƙasa kai tsaye a waɗannan yankuna.

An gabatar da wani ƙudiri a watan da ya gabata domin cimma hakan, amma ba a sa ran zai samu amincewar Majalisa. Idan hakan ta faru, yankin Puerto Rico na daga cikin wuraren da abin zai fi shafa.

Haka kuma dokar ta shafi yaran matan da suka shiga Amurka da gangan ta hanyar yaudara domin haihuwa kawai a cibiyoyin da ake gudanar da harkar birth tourism.

Kara karanta wannan

A ba su wuta: Gwamnan Bauchi ya umarci sojoji a shafe 'yan bindiga

Umarnin ya kuma nemi takaita amfani da mata masu ɗaukar ciki (surrogate mothers) idan manufar ita ce samun ɗan ƙasar Amurka ta wannan hanya.

Trump ya rattaba hannu kan dokoki
Shugaba Donald Trump a Oval Office Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

An umarci hukumomi su ƙara tsaurara matakai

Wani umarnin zartarwa na biyu ya umarci Minista Harkokin Wajen Amurka da Ministan Ma'aikatar Tsaron Cikin Gida su fitar da sababbin ƙa'idoji da umarni domin dakile 'birth tourism' tare da yaƙi da wannan sana'a a cikin Amurka da ma ƙasashen waje.

A halin yanzu, dokar Amurka ta haramta bai wa mutum bizar yawon buɗe ido idan babban manufarsa ita ce haihuwa a Amurka domin yaro ya samu zama ɗan ƙasar Amurka.

Haka kuma jami'an shige da fice na iya hana mace mai juna biyu shiga Amurka idan suka tabbatar cewa ta zo ƙasar ne domin haihuwa kawai.

Batun karancin makamai a Amurka

A wani labarin kuma, kun ji cewa Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yi martani kan rahotannin da ke cewa kasarsa na fuskantar matsalar karancin makamai.

Donald Trump ya yi watsi da rahotannin kafafen yaɗa labarai da ke cewa ajiyar makamai masu linzami ta ma'aikatar tsaron Amurka (Pentagon) na raguwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng