Jama'a Sun Gigice bayan Tsoron Fashewar 'Bam' a Abuja

Jama'a Sun Gigice bayan Tsoron Fashewar 'Bam' a Abuja

  • An samu rahoton fashewar wani abu da ke tsoron bam ne a kusa da gadar Apo da ke babban birnin Abuja da daren Alhamis 6 ga watan Agusta 2026
  • A lokacin da jama'a suka ji daram kowa ya kama gabansa inda aka rika gudun neman tsira a cikin firgici da tsoron abin da zai iya biyo baya
  • Hukumar kashe gobara da jami'an tsaro sun isa wurin, an kuma samu karin bayanai game da fashewar abin da kuma da halin da ake ciki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – An shiga firgici a daren Alhamis bayan da aka ba da rahoton fashewar wani abu a kusa da gadar Apo, daf da gidan mai na Shafa, kusa da Rita Lori Hotel a yankin Garki da ke Abuja.

Kara karanta wannan

Trump ya fusata, ya yi ƙarin haske kan jita jitar cewa suna fama da ƙarancin makamai

Wani da ya shaida abin da ya faru, Jason Akande, ya ce ya ji ƙarar fashewa sau da dama, lamarin da ya sa ya fara zaton cewa fashewar bam ce.

An ji karar fashewar abu a Abuja
Wasu daga cikin jami'an yan sanda a bakin aiki Hoto; Nigeria Police Force
Source: Facebook

Jaridar Leadership ta wallafa cewa wannan fashewa da aka ji ta dimauta jama'a inda aka rika gudun tsira a cikin firgici da rashin tabbas game da abin da ya faru.

Gobara ta tashi a Abuja

A ruwayar Daily Post rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne a kusa da gidan man da ake yawan zirga-zirga, lamarin da ya jefa mazauna yankin da masu ababen hawa cikin fargaba, inda da dama suka rika gudu domin tsira.

Daga bisani jami'an Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya da ta Hukumar Kashe Gobara ta Babban Birnin Tarayya (FCT) sun isa wurin domin fara aikin ceto da kuma dakile yaduwar gobarar.

Kakakin Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya, Paul Abraham, ya ce an tura jami’an agajin gaggawa zuwa wurin domin shawo kan gobarar tare da hana ta bazuwa zuwa wasu wurare.

Abraham ya bayyana cewa jami’an Hukumar Kashe Gobara suna ci gaba da aiki domin dakile gobarar tare da hana ta yaɗuwa zuwa gine-gine da sauran wuraren da ke kusa.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun tare matafiya, sun budewa jama'a wuta

Ana binciken fashewar wani abu a Abuja

Paul Abraham ya kuma jajanta wa mutanen da lamarin ya shafa, yana mai tabbatar wa mazauna yankin cewa ana ci gaba da ɗaukar matakan da suka dace domin shawo kan lamarin.

Gobara ta tashi a gidan mai a Abuja
Taswirar babban birnin tarayya Abuja Hoto: Legit.ng
Source: Original

A cewarsa:

“Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya tana jajanta wa dukkan waɗanda gobarar da ke ci a AYM Shafa Petrol Station, Area 3, Abuja ta shafa.
“Jami’anmu na kashe gobara suna wurin a halin yanzu, suna aiki ba dare ba rana cikin ƙwarewa domin shawo kan gobarar, hana ta bazuwa, tare da dawo da lamarin cikin yanayi mai kyau cikin gaggawa da aminci.”

Zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a kai ga gano musabbabin tashin gobarar ba yayin da ake ci gaba da bincike don gano abin da ya faru.

Bam ya tashi a kusa da sojoji

A baya kun samu labarin cewa Wani abu da ake zaton bam ne ya tashi a tashar motocin da ke daura da barikin sojoji na Mogadishu a babban birnin tarayya Abuja lamarin da ya jawo tashin hankali.

Kara karanta wannan

Trump ya fadi zabin Amurka tsakanin sulhu da yaki a Iran

Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa yau Litinin, ta ce tuni aka samu nasarar shawo kan lamarin kafin ya kai ga kara illata bayin Allah ko jawo asarar rayuka.

Shaidu da abin ya faru a kan idonsi sun bayyana cewa mutane sun firgita a lokacin da bam ɗin ya tashi, kowa ya yi takansa domin tsira da rayuwarsa da gudun abin da zai iya biyo bayan fashewar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng