Duk da Banbancin Addini, Gwamna Ya Dauki Mace Musulma a Matsayin Mataimakiyarsa a 2027
- Gwamna Agbu Kefas ya bayyana Zainab Ibrahim a matsayin “mataimakiyar gwamna ta gaba” ta Jihar Taraba
- Shugaban APC na kasa, Farfess Nentawe Yilwatda, shi ma ya kira Zainab da “mataimakiyar gwamna mai jiran gado”
- Gwamna Kefas ya yaba wa Shugaba Tinubu kan ayyukan da ya ce gwamnatin tarayya ta kawo wa Taraba
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Taraba, Nigeria - Gwamnan Jihar Taraba, Dr Agbu Kefas, ya nuna Mataimakiyar Shugabar Matan APC ta Kasa, Zainab Ibrahim, matssyin abokiyar takararsa a zaben 2027.
Gwamna Kefas ya bayyana hakan ne ranar Juma’a a gidan TY Danjuma da ke Jalingo, lokacin da yake karbar bakuncin Shugaban APC na Kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda.

Source: Facebook
Farfesa Yilwatda ya je jihar ne domin bikin cikarsa shekaru 58 da haihuwa, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
A yayin gabatar da manyan baki, Kefas ya kira Zainab Ibrahim da “mataimakiyar gwamna ta gaba” ta Jihar Taraba.
Shugaban APC na kasa shi ma ya yi amfani da irin wannan bayani, inda ya kira ta “mataimakiyar gwamna mai jiran gado”.
Gwamna Kefas ya yaba wa Tinubu
Gwamna Kefas ya nuna godiyarsa ga shugabancin APC saboda shirya wani shirin bayar da magani kyauta a fadin jihar a matsayin wani bangare na bikin cikar Yilwatda shekaru 58.
Ya ce likitocin da jam’iyyar ta turo sun shafe kwanaki suna gudanar da aikin jinya da tiyata kyauta, yana mai cewa labaran da suke samu daga jama’ar jihar na da matukar kayatarwa.
“A gare mu a Jihar Taraba, dukkanmu muna goyon bayan APC domin mu rama abin da Mai Girma Shugaban Kasa ya yi mana," in ji shi.
Kefas ya ce irin ayyukan da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi wa al’ummar Taraba ba za a iya kididdige su ba.
Ya kuma bayyana amincewar shugaban kasar na kafa rundunar soji ta Division a Taraba a matsayin wani mataki da zai taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya a jihar.

Kara karanta wannan
Kano: Gwamna Abba ya ƙaddamar da aikin da ba a taɓa ganin irinsa ba a Arewacin Najeriya
Yilwatda ya bayyana dalilin zabar Taraba
A nasa jawabin, Yilwatda ya ce ya zabi Taraba a matsayin wurin bikin cikar sa shekaru 58 domin nuna irin jajircewar jam’iyyar wajen kula da jin dadin al’umma.
Ya ce APC ba ta tsaya kawai wajen neman kuri’u ba, tana kuma kokarin nuna tausayi da qkulawa ga jama’a, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Source: Twitter
Shugaban APC ya ce:
“APC ba ta neman kuri’u kawai, tana kuma nuna fuskar tausayi ta jam’iyyarmu.”
Ya kara da cewa jam’iyyar ba ta zuwa wurin jama’a domin neman kuri’u kawai, tana kuma kula da lafiyarsu, iliminsu da makomarsu.
Gwamna ya tsara nasarar Tinubu a 2027
A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Agbu Kefas ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai samu kuri'un jihar Taraba 100% a zaben 2027.
Kefas ya bayyana kwarin gwiwar cewa goyon bayan da yake da shi daga talakawan jihar yana nan daram kuma Tinubu ya ci zabe cikin sauki.
Gwamnan ya jaddada cewa dabarunsa na tsohon jami'in soja sun ba shi damar tsara taswirar da za ta ba shugaba Tinubu gagarumar nasara a Taraba.
Asali: Legit.ng
