An ba da Tallafin Buta da Sauransu a Filato, za a Taho Gombe, Kaduna
- Rahoto ya nuna cewa ukumar PRUWASA ta fara rarraba kayan gina banɗaki ga gidaje 155 a karamar hukumar Langtang ta Arewa a Plateau
- Shirin SURWASH ne ya dauki nauyin wannan taimakon da nufin kawar da yin bahaya a fili da inganta lafiyar al'umma a ƙauyuka
- Hukumar ta ce ana sa ran Langtang ta Arewa za ta zama cikin wuraren da za a ayyana a matsayin yanki mai tsafta nan da Nuwamban 2026
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Filato - Hukumar Ruwa da Tsafta ta Jihar Plateau wadda ake kira PRUWASA ta dauki wani mataki mai muhimmanci na yaki da yin bahaya a fili, inda ta raba kayan gina banɗaki a karamar hukumar Langtang ta Arewa.
Gidaje guda 155 da ke yankunan Langtang ta Arewa sun samu taimakon a lokacin wani biki da aka shirya a hedikwatar karamar hukumar.

Source: Facebook
Gwamnatin Plateau ta wallafa a Facebook cewa an gudanar da aikin ne a karkashin shirin SURWASH, wato shirin samar da ruwa mai tsafta a birni da karkara.
Dalilin raba tallafin a Plateau
Shugaban PRUWASA, Godfrey Nuhu Dashuhar, ya yi bayani cewa babban burin shirin shi ne samar wa al'ummar karkara ruwan sha mai tsafta, sannan a rage cututtukan da ruwan da ba shi da tsafta ke kawo wa mutane.
Ya nuna cewa jihohi bakwai ne ke a ƙarƙashin shirin a halin yanzu, wadanda suka hada da Delta, Ekiti, Gombe, Imo, Kaduna, Katsina da Plateau.
Dashuhar ya kara da cewa kowace karamar hukuma da aka ayyana a matsayin wacce ba a yin bahaya a fili, ana sanya sunan ta a rajista ta ƙasa, wanda hakan ke jan hankalin masu zuba jari.
Ya nuna cewa karamar hukumar Riyom ta riga ta samu wannan matsayi kuma ita ce farko a jihar Plateau, inda ya yi kira ga mutanen Langtang su yi kokarin zamana biyu.
Burin tsaftace jihar Filato
Daraktar tsafta da kiwon lafiya a PRUWASA, Magdalene Jibri, ta bayyana farin cikinta da yadda al'ummar yankin suka nuna haɗin kai.
Ta ce idan aka cigaba da kokari, ana sa ran hakan zai sa Langtang ta Arewa a matsayin yanki mai tsafta a watan Nuwamba 2026.
Kowanne daga cikin gidajen 155 da suka amfana sun karɓi abubuwa da suka haɗa da langa-langa guda shida, katako guda 14, buhun siminti guda ɗaya da sauran kayan da ake buƙata don gina bayan gida.

Source: Facebook
Shugaban karamar hukumar Langtang ta Arewa, Pirfa Jingfa Ntyem, wanda wakilinsa ya halarta, ya gode wa gwamnan jihar Plateau, Caleb Manasseh Mutfwang, saboda goyon bayansa ga ayyukan yankin.
Ya kuma yi kira ga dukkan gidajen da suka amfana da su yi amfani da kayan domin manufar da aka tsara ba wata dabam ba.
An raba tallafin Saudi a Yobe
A wani labarin, mun kawo muku cewa gwamnatin kasar Saudiyya ta kawo tallafin Najeriya domin a tabawa talakawan Najeriya.
Legit Hausa ta tattaro cewa shugabar hukumar ba da agajin gaggawa ta NEMA ce ta jagoranci raba kayan tallafin a jihar Yobe.
Wani jami'in kasar Saudiyya ya kasance a wajen da aka raba kayan abincin, inda aka sanar da cewa za a rana shi a wasu jihohin Najeriya.
Asali: Legit.ng


