Fadar Shugaban Kasa na da Hannu a Kafa Hukumar Bogi ta PFIPC? ICPC Ta Gano Gaskiya
- Hukumar yaki da rashawa ta ICPC ta wanke Fadar Shugaban Kasa daga zargin hannu wajen nada Adeniyi Adeyemi ko kirkirar PFIPC
- Hukumar ta gano cewa takardar nadin Adeyemi da sauran takardun da ya yi amfani da su duk na jabu ne
- Bincike ya kuma gano wasu karin hukumomi biyu na bogi da Adeyemi ya kirkira domin gudanar da ayyukan haramtattu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) ta wanke Fadar Shugaban Kasa daga zargin nada Adeniyi Adeyemi a matsayin shugaban hukumar bogi (PFIPC) da ake ta surutu a kanta.
Hukumar ta ce takardar nadin da Adeniyi Adeyemi Matthew ya gabatar ta jabu ce kuma ba ta fito daga Fadar Shugaban Kasa ba.

Source: Twitter
Daily Trust ta ruwaito cewa shugaban ICPC, Dakta Musa Adamu Aliyu, ne ya bayyana hakan bayan ya mika rahoton wucin gadi na bincike ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu a Aso Fock.
Ya ce:
A ranar 7 ga watan Yuli ne Shugaba Tinubu ya umarci ICPC ta gudanar da bincike kan ayyukan wannan hukuma tare da gabatar masa da rahoto cikin kwanaki 30.
ICPC ta wanke fadar shugaban kasa
Musa Adamu Aliyu ya ce binciken ya tabbatar da cewa fadar shugaban kasa ko wata hukuma ta gwamnatin tarayya ba ta taba nada Adeyemi ba.
Ya kara da cewa:
"An tabbatar cewa ba gwamnatin tarayya ba ce ko wata hukuma da ta nada Adeyemi."
An taba tura wa hukumar bogi kudi?
Shugaban ICPC ya ce binciken ya nuna cewa babu wani kudi da gwamnatin tarayya ta amince ko ta fitar domin PFIPC.
A cewarsa:
"Mun gano cewa gazawar tsarin tantance takardu da hadin gwiwar hukumomi ya ba Adeyemi damar anfani da wasu gibba wajen gudanar da wadannan ayyuka."
Fadar Shugaban Kasa ta nesanta kanta da PFIPC
A nata bangaren, Fadar Shugaban Kasa ta ce ba ita ce ta kirkiri PFIPC ba kuma ba ta taba rubuta wata takarda da ta shafi kasafin kudinta ba, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan
2027: Babban jigon APC a Arewa ya tada rigima, ya ce ba zai sake tallata Tinubu ba
Daraktan Gudanarwa, Abdulkadir Idris, wanda ya wakilci Babban Sakataren Fadar Shugaban Kasa a gaban Kwamitin Musamman na Majalisar Wakilai, ya ce gwamnati ta fara jin labarin PFIPC ne ta kafafen yada labarai.
Ya ce:
"Ba mu aika wata takarda ga Ofishin Akanta Janar kan wannan hukuma ba. Hasali ma ba mu san komai game da ita ba. Mun fara jin labarinta ne bayan ta bayyana a kafafen yada labarai."
Ya kuma musanta sahihancin takardun da ake ikirarin sun fito daga Fadar Shugaban Kasa domin neman lambar kasafin kudin PFIPC.

Source: Facebook
Idris ya ce mutumin da aka ce ya sanya hannu a takardun, Akande Adewale, ba ya cikin ma'aikatan Fadar Shugaban Kasa, yana mai cewa takardun gaba daya na jabu ne.
ICPC ta gano karin hukumomin bogi 2
A wani rahoton, kun ji cewa hukumar ICPC ta gano cewa Adeniyi Matthew Adeyemi ya kirkiri wasu hukumomin gwamnati biyu na bogi baya ga PFIPC.
Hakan na kunshe ne a cikin rahoton binciken da hukumar ICPC ga mika wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ranar Alhamis, 6 ga Agusta, 2026
Asali: Legit.ng
