Gwamnatin Najeriya Ta Karya Farashin Taki a Shirin Tallafin Noma na 2026

Gwamnatin Najeriya Ta Karya Farashin Taki a Shirin Tallafin Noma na 2026

  • Gwamnatintarayyar Najeriya ta ƙaddamar da shirin tallafin noma na Renewed Hope domin bunkasa samar da abinci fadin kasa
  • Wani rahoto ya nuna cewa shirin zai tallafa wa kananan manoma sama da 100,000 a faɗin Najeriya domin inganta noma da samar da abinci
  • Gwamnatin Najeriya ta sanar da cewa manoma daga dukkan yankunan kasar za su samu tallafin kaso mai tsoka na takin zamani

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta kaddamar da shirin tallafin kayan aikin noma na Renewed Hope a Najeriya.

Kaddamar da tallafin na zuwa ne yayin da damuwar bana ke kankama a yankunan Najeriya da dama, musamman a Arewacin kasar.

Kayan tallafin da aka kaddamar
Yadda aka tara takin da aka ba manoma a Najeriya. Hoto: @nadfng
Source: Twitter

An kaddamar da tallafin noma

Tashar NTA ta wallafa a Facebook cewa mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ne ya ƙaddamar da rabon kayan aikin noman.

Kara karanta wannan

Bayan kotu ta nemi a soke ADC, Tinubu ya yi kira ga alkalai

Shettima ya bayyana cewa shirin, wanda Asusun Bunƙasa Noma na Ƙasa (NADF) ke jagoranta, wani muhimmin ɓangare ne na Ajandar Renewed Hope ta gwamnatin Tinubu.

Game da adadin wadanda za su amfana kuwa, an sanar da cewa shirin na da nufin tallafa wa kananan manoma 128,930 a faɗin ƙasar nan.

Za saka tallafin takin zamani

Gwamnatin Najeriya ta ce manoma za su amfana da tallafin kashi 75 cikin 100 na takin zamani, tare da mayar da hankali kan noman masara, shinkafa, rogo da waken suya.

Ta ce shirin zai fi mayar da hankali kan rarraba takin NPK mai rangwame, wanda ake samarwa a cikin gida kuma aka yi masa alamar “Ba na sayarwa ba ne” domin hana karkatar da shi.

Yadda za a raba tallafin taki

Manoma 20,160 ne daga kowace shiyya ta ƙasa za su amfana da kayan tallafin, inda za a raba buhunan taki 80,640 (kimanin buhu huɗu ga kowane manomi).

Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima da ministan noma, Aliyu Sabi Abdullahi ya wakilta, ya ce aiwatar da shirin ƙarƙashin kulawar NADF ya mayar da hankali kan isar da kayan aikin noma da suka dace a kan lokaci.

Kara karanta wannan

Tinubu zai kashe Naira tiriliyan 5 kan tsaro, za a dauki sababbin ƴan sanda 50000

Ya kara da cewa hakan zai samar da haɗin gwiwa da gwamnatocin jihohi, da kuma haɗa shi da sauran shirye-shiryen bunƙasa darajar noma.

Wadanda suka samu tallafin noma
Wasu daga cikin wadanda aka ba tallafin noma a Najeriya. Hoto: @nadfng
Source: Twitter

Sabi ya ce shirin na samun goyon bayan masana’antun taki na cikin gida, masu sarrafa kayan amfanin gona da kuma masu kasuwancin kayan noma.

Hukumar NADF ta wallafa hotunan yadda aka kaddamar da shirin tallafin a wani sako da ta fitar a shafinta na X a ranar Talata.

An saka harajin noma a Katsina

A wani labarin, mun kawo muku cewa 'yan bindiga masu garkuwa da mutane suka saka wa jama'a harajin noma a jihar Katsina.

Wani rahoto da Legit Hausa ta samu ya nuna cewa mutanen ƙauyukan da aka kakabawa harajin sun fara hada kudi domin ba 'yan ta'adda.

Sai dai duk da haka, mutanen yankunan sun nuna fargabar cewa ba lallai harajin ya zama na karshe ba, domin za su iya dawowa neman karin kudi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng