Tashin Hankali: 'Yan Bindiga Sun Shiga cikin Gari Suna Ta Kashe Bayin Allah a Kogi
- An kashe akalla mutane bakwai bayan wasu ‘yan bindiga sun kai hari kan al’ummomin Abugi, Kuchinda da Mikugi a Masarautar Kupa
- Harin ya biyo bayan kashe wani makiyayi da ake zargin mai satar shanu ne yayin wata arangama da jami’an sa-kai a shingen bincike
- Gwamnatin Kogi ta yi Allah wadai da hare-haren, ta umarci jami’an tsaro su kamo waɗanda ke da hannu tare da hana sake kai hare-haren ramuwar gayya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Kogi – Akalla mutane bakwai ne aka tabbatar da mutuwarsu bayan wasu ‘yan bindiga sun kai hari kan al’ummomin Abugi, Kuchinda da Mikugi da ke Masarautar Kupa, ƙaramar hukumar Lokoja a Jihar Kogi.
Harin ya faru ne a ranar Alhamis, inda mazauna yankin suka ce ‘yan bindigar sun mamaye garuruwan tare da yin harbi ta hanyoyi daban-daban.

Source: Original
Yadda aka kai hari jihar Kogi
Lamarin ya kuma haifar da raunuka da kuma lalata dukiyoyi, yayin da wasu mazauna yankin suka tsere zuwa wuraren da suke ganin sun fi tsaro, in ji rahoton Daily Trust.
A cewar mazauna yankin, lamarin ya fara ne da misalin ƙarfe 8 na safe bayan wani makiyayi, wanda ake zargin mai satar shanu ne, ya gamu da arangama da jami’an sa-kai a wani shingen bincike.
A yayin rikicin, an harbe makiyayin har lahira.
Wani mazaunin Abugi mai suna Ahmed ya ce bayan ƴan sa’o’i da faruwar lamarin ne wasu ‘yan bindiga suka mamaye garin tare da fara harbe-harbe.
Ya ce harin ya shafi tituna, kasuwanni da kuma fadar babban basaraken gargajiya na yankin.
Ahmed ya bayyana cewa zuwa daren ranar, an tabbatar da mutuwar mutane bakwai, amma ya ce ana iya samun ƙarin adadin waɗanda suka rasa rayukansu yayin da ake ci gaba da bincike da tabbatar da waɗanda abin ya shafa.
Dan Mayaki na Kupa ya mutu
Daga cikin waɗanda aka tabbatar da mutuwarsu akwai Yarima Aliyu Isah Kabir, ɗan Mayaki na Kupa kuma shugaban matasan jam’iyyar APC na mazabar Kupa ta Kudu.

Kara karanta wannan
Tsugune ba ta kare ba, an rena kokarin Tinubu kan ceto daruruwan mutane da aka sace
Lamarin ya jefa al’ummar yankin cikin zaman makoki tare da ƙara fargabar sake barkewar tashin hankali.
Shugaban ƙaramar hukumar Lokoja, Comrade Abdullahi Adamu, ya tabbatar da harin, yana mai cewa an rasa rayuka tare da lalata dukiyoyi.
Ya ce:
"Mun umarci hukumomin tsaro da abin ya shafa su gaggauta ɗaukar mataki tare da kama duk wanda ke da hannu, kai tsaye ko a kaikaice, wajen harin domin ya fuskanci hukunci."
Adamu ya yi kira ga mazauna yankin da su kwantar da hankalinsu yayin da jami’an tsaro ke ɗaukar matakan da suka dace.
Gwamnatin Kogi ta yi Allah wadai
Gwamnatin Jihar Kogi ta yi Allah wadai da lamarin, inda ta bayyana shi a matsayin harin ramuwar gayya mai muni, mara ma’ana kuma wanda ba za a amince da shi ba.
A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yaɗa Labarai da Sadarwa na jihar, Kingsley Fanwo, ya fitar ranar Juma’a, gwamnatin ta ce za ta binciki musabbabin lamarin tare da gano waɗanda suka aikata laifin.
Gwamnatin ta ce:
"Gwamnatin Jihar Kogi ta yi Allah wadai da kisan makiyayin da ba shi da makami da kuma harin ramuwar gayya da ya biyo baya."
Ta kuma jaddada cewa duk wanda aka samu da hannu a kisan, ba tare da la’akari da matsayinsa ko ƙabilarsa ba, zai fuskanci hukuncin doka.

Source: Twitter
Ododo ya umarci jami’an tsaro
Gwamnan Jihar Kogi, Ahmed Usman Ododo, ya jajanta wa iyalan waɗanda suka mutu tare da umartar jami’an tsaro da su gaggauta dawo da zaman lafiya a yankin.
Gwamnatin ta ce an kuma umarci jami’an tsaro su karɓe iko da lamarin tare da kamo waɗanda ke da hannu wajen kashe-kashen.
Ta yi kira ga mazauna yankin da su guji sake kai hare-haren ramuwar gayya, tare da ba jami’an tsaro sahihan bayanan da za su taimaka wajen gudanar da bincike.
A halin yanzu, Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kogi, ASP Saliu Oyiza Afusat, ba ta mayar da martani ga kiran waya da saƙon da aka aika mata ba har zuwa lokacin kammala wannan rahoto.
Asali: Legit.ng

