Yadda 'Yan Ta'adda Suka Lakadawa Dalibai da Malaman Oyo Duka a Daji
- Shugabar makarantar da aka sace dalibai a jihar Oyo, Racheal Alamu ta bayyana yadda suka kwana kwanaki 56 a hannun 'yan bindiga
- Masu garkuwa sun rika dukan yara kanana saboda yadda suka ta kuka, kuma sun daure malamai maza da sarka a kafafunsu a cikin dajin
- An tseratar da dalibai 39 da malamai 7 da 'yan ta'addar Ansaru suka yi garkuwa da su a yankin Oriire bayan shafe kwanaki da dama
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Ibadan - Shugabar makarantar da aka sace tare da malamai da dalibai a karamar hukumar Oriire a jihar Oyo, Racheal Alamuta bayyana yadda suka sha wahala a lokacin da suka shafe kwana 56 a hannun masu garkuwa.
Hakan na zuwa ne bayan sojoji da sauran jami'an tsaro sun hada kai sun ceto su daga mutanen da suka yi garkuwa da su suna karatu a makaranta.

Kara karanta wannan
'Rai bai fi rai ba': Bulama ya nemi Tinubu ya ceto daliban Arewa a hannun yan bindiga

Source: Facebook
Vanguard ta wallafa cewa ta yi wannan bayani ne bayan an mika ta da sauran malaman da aka ceto zuwa ga Gwamna Seyi Makinde a ofishinsa da ke a Ibadan.
Yadda suka rayu a cikin daji
Alamu ta ce yawancin kwanakin da suka yi a hannun masu garkuwa sun yi su a fili a cikin daji, a karkashin rana da ruwan sama, suna kula da yaran da suke tare da su.
Daily Trust ta wallafa cewa malamar ta ce abin da ya basu karfin gwiwa shi ne bangaskiyarsu da imani cewa mutane na addu'a dominsu.
Shugabar makarantar ta bayyana cewa ita kanta ba a buge ta ba, amma an doke wasu yaran kanana ba tare da tausaya masu ba.
Ta ce duk lokacin da yara suka yi kuka, masu garkuwa sukan yi fushi domin sun yi imani cewa sautin zai jawo hankalin jami'an tsaro.
Game da malamai maza, ta ce su ne suka fi kowa fama saboda an daure idanunsu an kuma sa masu sarka a hannu da kafa.
Alamu kuma ta bayyana cewa duk da tsananin halin da suke ciki, ba a ci zarafin kowa a hanyar lalata ba.
Tafiye-tafiyen dare a daji
Ta kara da cewa duk lokacin da masu garkuwa suka ji an gano wurinsu, sukan tilasta wa wadanda aka yi garkuwa da su su koma wani wuri da tsakar dare.
Malamar ta ce wannan tafiya kan fara tsakanin karfe 7:00 zuwa 8:00 na dare, wani lokacin kuma ta kai tsawon awowi uku zuwa hudu. Ta ce wannan shi ya sa aka samu raunuka a jikinsu.
A bayanan da ta yi, ta ce ana daukan yara kanana a hannu, amma manyan suna tafiya a kafa, kuma suna faduwa a kan hanyar.

Source: Original
Wata 'yar uwar daya daga cikin daliban da aka ceto ta bayyana cewa ana ba yaran da aka sace doya da taliya, kuma suna shan ruwa daga wani kogi a cikin dajin Oyo, inda 'yan ta'addar Ansaru suka tsare su.

Kara karanta wannan
Yadda sojoji suka kutsa dajin Oyo, suka gwabza da 'yan bindiga yayin ceto dalibai
An kama iyalan masu garkuwa
A wani labarin, mun kawo muku cewa hukumomin Najeriya sun kama iyalan 'yan ta'addan da suka ace dalibai da malamai a jihar Oyo.
Hakan na cikin matakan da hukumomi suka dauka domin tabbatar da cewa an matsawa 'yan ta'addan lamba sun saki daliban da suka sace.
Wani rahoto ya tabbatar da cewa 'yan ta'addan sun kalli bidiyon da jami'an tsaro ke rike da 'yan uwansu, lamarin da ya kara tayar masu da hankali.
Asali: Legit.ng
