Sarkin Kano Ya Gargadi Najeriya kan AI, Ya bada Shawara kan Fasahar Zamani
- Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya ce Najeriya na cikin bukatar gaggawa wajen tsara manufofi kan fasahar zamani musamman AI
- Ya bukaci jami’o’i su jagoranci kirkirar taswirar AI ta kasa wanda za ta dace da tsarin Najeriya domin a mori fasahar zamanin yadda ya dace
- Khalifa Muhammadu Sanusi II ya kara da cewa Najeriya na fuskantar barazanar koma baya matukar aka yi sako-sako da batun AI a kasar nan
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya bayyana cewa Najeriya na bukatar tsari mai ma’ana da kuma cikakken tsarin manufofi domin amfani da sababbin fasahohi.
Khalifa Muhammadu Sanusi ya ce ana bukatar tsarin musamman don dadaita yadda ake amfani da fasahar AI, wajen bunkasa ci gaban kasa mai dorewa.

Kara karanta wannan
Gwamnan Kano, Abba ya gano yan siyasar da ke rura wutar matsalar tsaro a Najeriya

Source: Twitter
Daily Trust ta wallafa cewa Sanusi ya bayyana haka ne a yayin taron karo na 8 na duk shekara biyu na kwamitin shugabannin jami’o’in gwamnati na jihohi (COPSUN) da aka gudanar a Kano.
Muhammadu Sanusi II ya magantu kan fasahar zamani
Jaridar Daily Post ta wallafa cewa Sarkin Kano ya yi jawabin a taron ya da ya yi duba kan matsayin AI yanzu a Najeriya da rawar da jami'o'i za su taka wajen bunkasa ta, da kuma matakin da ake a duniya.
A cewarsa:
“Wannan kasa na bukatar tsari. Wannan kasa na bukatar tsarin manufofi. Wannan kasa na bukatar ta kasance cikin shirin wannan karni da muke ciki.”
Ya bukaci jami’o’in Najeriya su jagoranci samar da taswirar AI ta kasa, yana mai jaddada cewa dole ne su wuce koyarwa da bincike kawai, su shiga cikin tsara manufofin da za su bunkasa ci gaban kasa.
Sarki Sanusi II ya gargadi Najeriya
Sarki Sanusi II ya yi gargadin cewa Najeriya na fuskantar barazanar koma baya idan aka kwatanta da wasu kasashe kamar Ghana da tuni suka fara aiwatar da tsare-tsaren AI da suka hada da horar da matasa, bunkasa bayanai da sauya tattalin arziki.

Source: Facebook
Khalifa Muhammadu Sanusi II ya jaddada muhimmancin jami’o’i a matsayin ginshikan al’umma, yana mai cewa dole ne su taka rawa wajen tattaunawa kan harkokin shugabanci, tattalin arziki, kimiyya da fasaha.
Sarki Sanusi II ya yaba wa gwamnatocin jihohi kan fahimtar muhimmancin shugabannin jami’o’i wajen tsara manufofi da inganta shugabanci.
Sarki Sanusi II zai yi gagarumin biki
A baya, mun wallafa cewa masarautar Kano karkashin Mai martaba Khalifa Muhammadu Sanusi II za ta yi bikin nadin sarauta ga wasu hakimai da aka kara daga likkafarsu wajen jagorantar al'umma.
Rahotanni sun nuna cewa mai martaba Muhammadu Sanusi II ya amince da sauye-sauye da suka shafi wasu masu rike da sarauta kamar yadda aka gani a wata takarda da Danmakwayon Kano, Alhaji Abba Yusuf ya fitar.
Mai martaba Muhammadu Sanusi II zai jagoranci bikin karin matsayi ga wasu mutane shida da suka hada da hakimai a jihar Kano a ranar Juma'a mai zuwa domin gudanar da bikin kara masu girma a masarautar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
