Jigon APC Ya Fadi Yadda Kiristoci Suka Karbi Tikitin Muslim Muslim a Najeriya

Jigon APC Ya Fadi Yadda Kiristoci Suka Karbi Tikitin Muslim Muslim a Najeriya

  • Wani jigo a jam'iyyar APC, Farouk Aliyu, ya ce Kiristocin Najeriya sun karɓi tikitin Muslim-Muslim yanzu fiye da yadda suka yi 2023
  • Ya bayyana hakan ne bayan Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar da cewa zai sake tsayawa takara tare da Kashim Shettima a 2027
  • A bayanin da ya yi a wata hira, Aliyu ya ce gwamnatin Tinubu ta nuna a aikace cewa ba ta nuna bambanci ko wariya ga kowane addini

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Wani jigo a jam'iyyar APC, Farouk Aliyu, ya ce muhawarar da aka yi kan tikitin Muslim-Muslim a lokacin zaɓen 2023 ta riga ta zama tarihi.

Yayin tattaunawa kan zaben 2027, dan siyasar ya bayyana cewa Kiristoci da dama sun karɓar wannan tsari a yanzu fiye da lokacin da aka fara gabatar da shi.

Kara karanta wannan

Buba Galadima: 'Dalilin da tikitin Obi,Kwankwaso ya zama mafitar Najeriya '

Shugaba Bola Tinubu da Kashim Shettima
Bola Tinubu da Kashim Shettima a fadar shugaban kasa. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Aliyu ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da tashar Arise TV a ranar Alhamis, bayan shugaba Bola Tinubu ya sanar da cewa Kashim Shettima zai ci gaba da kasancewa abokin takararsa a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

APC: Dalilin tafiya da Shettima

A cewar Aliyu, jam'iyyar APC ta zaɓi ci gaba da amfani da tikitin da ta samu nasara da shi a zaɓen 2023 ne domin kauce wa jawo ce-ce-ku-ce da rikice-rikicen cikin gida.

Ya ce ya yi farin ciki da matakin da shugaba Tinubu ya ɗauka na ci gaba da tsayawa tare da Shettima, yana mai cewa hakan ya nuna shugabanci cikin hikima.

"Shugabanmu, Bola Ahmed Tinubu, ya yanke shawarar ci gaba da tafiya da tikitin da ya samu nasara da shi. Kuma ina ganin Kiristoci a Najeriya yanzu sun fi karɓar wannan tikitin fiye da yadda suka yi a shekarar 2023,"

Kara karanta wannan

Babban jigon APC a Arewa ya yi magana kan barin jam'iyyar bayan Tinubu ya zabi Shettima

In ji Aliyu.

"Ba a nuna wariya ga Kiristoci ba"

Aliyu ya tuna cewa lokacin da APC ta fito da tikitin Muslim-Muslim a shekarar 2023, mutane da dama sun nuna damuwa, suna zargin cewa Kiristoci za su fuskanci wariya idan jam'iyyar ta samu nasara.

Sai dai Vanguard ta rahoto ya ce abubuwan da suka faru tun bayan kafa gwamnatin Tinubu sun nuna cewa abin da suke tsoro bai tabbata ba.

"A lokacin an yi ta cewa za a ware Kiristoci. Amma yanzu kowa ya ga cewa hakan bai faru ba."

Ya ƙara da cewa shugaba Tinubu yana tafiyar da gwamnati ne ba tare da nuna bambanci tsakanin 'yan Najeriya bisa addini ba.

Farouk Aliyu ya kammala da cewa APC ta gwada wannan tikiti a lokacin da ake da ƙalubale sosai, kuma 'yan Najeriya suka ba ta goyon baya. Ya ce jam'iyyar na sa ran sake samun amincewar jama'a da wannan tikiti a zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Adeyemi: 'Yadda na samo aron N400m wajen kafa hukumar bogi

Shugaban jam'iyyar APC ma kasa
Shugaban APC a Najeriya, Yilwatda Nentawe. Hoto: All Progressive Congress
Source: Facebook

Shettima ya sharbi kuka

A wani labarin, mun kawo muku cewa mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima ya yi magana kan wasu abubuwa da suka faru da shugaba Muhammadu Buhari.

Yayin taron tunawa da marigayi Muhammadu Buhari na farko, Shettima ya bayyana cewa Bola Tinubu ya umarce shi da ya je London duba lafiyar Buhari.

A lokacin da Shettima ya isa asibitin, ya bayyana cewa ya zubar da hawaye sosai kan yadda ya ga an sanya marigayi Muhammadu Buhari a ICU.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng