Najeriya Ta Yi Babban Rashi, Dr. Adamu Mohammed Fika Ya Riga Mu Gidan Gaskiya
- Tsohon Darakta Janar kuma Magatakardan Majalisar Tarayya na farko, Dr. Adamu Mohammed Fika, ya riga mu gidan gaskiya a Abuja
- Marigayin ya taba zama shugaban Hukumar Kula da Ayyukan Majalisar Tarayya (NASC) kafin Allah ya karbi rayuwarsa
- Rahotanni daga iyalansa sun nuna cewa an shirya za a yi masa jana'iza a Masallacin Kasa da ke Abuja ranar Juma'a, 7 ga Agusta, 2026
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
F.C.T Abuja, Nigeria - Tsohon jigo a harkokin mulkin Najeriya kuma tsohon Darakta Janar sannan kuma Magatakardan Majalisar Tarayya na farko, Dr. Adamu Mohammed Fika, ya rasu.
Marigayin, wanda ke rike da sarautar Zarma Kura na Fika, ya riga mu gidan gaskiya ne a wani asibiti da ke babban birnin tarayyya, Abuja.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an tabbatar da rasuwar dattijon kasar ne a wata sanarwa da mai ba Sarkin Fika shawara kan harkokin yada labarai, Alhaji Mohammed Abubakar (Chokalin Fika), ya fitar da yammacin jiya Alhamis.
Manyan mukaman da marigayin ya rike
Bayanan da aka tattaro sun nuna cewa marigayi Dr. Adamu Muhammad Fika shi ne Darakta Janar kuma Magatakardan Majalisar Tarayya na farko da aka yi bayan kafa majalisar dokokin Najeriya.
Haka kuma ya taba zama Shugaban Hukumar Kula da Ayyukan Majalisar Tarayya (National Assembly Service Commission - NASC) a lokacin rayuwarsa.
Kafin rasuwarsa, Adamu Muhammad Fika shi ne Shugaban Kwamitin Amintattu na Kungiyar Tsofaffin Magatakarda da Sakatarorin Majalisar Tarayya.
Marigayin ya kuma taba aiki a Cibiyar Nazarin Manufofi da Dabaru ta Kasa (NIPSS) da ke Kuru a jihar Filato da ke Arewa ta Tsakiya.
An sa lokacin da za a yi jana'izarsa a Abuja
Sanarwar da masarautar Fika ta fitar ta bayyana cewa za a gudanar da sallar jana'izarsa ranar Juma'a, 7 ga Agusta, 2026, a Babban Masallacin Kasa da ke Abuja.
Rahotanni sun nuna cewa 'yan uwa, abokan aiki da sauran masu alaka da marigayi Dr. Muhammad Fila sun fara bayyana alhininsu kan rasuwarsa tare da mika sakon ta'aziyya.

Source: Original
Sun bayyana mutuwarsa a matsayin babban rashi ga Masarautar Fika, jihar Yobe da kuma Najeriya baki daya, kamar yadda jaridar Leadership ta rahoto.
Ana san ran dai manyan jiga-jigai a kasar nan da suka hada da shuganani da sarakuna da sauran mutane musamman daga masarautar Fika da jihar Yobe za su halarci wannan jana'iza yau Juma'a.
Tsohon mataimakin gwamna ya rasu
A wani labarin, kun ji cewa tsohon mataimakin gwamnan Kebbi, Ibrahim K. Aliyu, ya rasu bayan doguwar jinya, lamarin da ya girgiza iyalansa da al'ummar jihar.
Marigayin, wanda ya fito daga ƙaramar hukumar Yauri a jihar Kebbi, ya rasu ne a wani asibiti da ke jihar Sokoto bayan ya shafe lokaci yana fama da rashin lafiya.
Gwamna Nasir Idris ya bayyana rasuwar Aliyu a matsayin babban rashi ga Masarautar Yauri, Jihar Kebbi da Najeriya baki daya, tare da mika sakon ta'aziyya ya iyalai da yan uwan mamacin.
Asali: Legit.ng

