Buba Galadima: 'Dalilin da Tikitin Obi, Kwankwaso Ya Zama Mafitar Najeriya '
- Makusancin tsohon gwamnan Kano, Injiniya Buba Galadima ya ce a yanzu, mafita daya ce ta rage wa Najeriya wajen tabbatar da hadin kai da ci gaba
- Bubala Galadima wanda makusancin Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ne ya bayyana cewa akwai hikima mai girma a hadin Peter Obi da Kwankwaso
- Ya bayyana cewa da wannan hadin APC da Bola Ahmed Tinubu ba za su kai labari a babban zaben 2027 da ke tafe bayan an gano gazawar gwamnati
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Jigo a jam'iyyar NDC, Injiniya Buba Galadima, ya bayyana cewa tikitin shugaban ƙasa na Peter Obi tare da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso shi ne zai taimaka wajen haɗa kan Najeriya.
Ya ce daga cikin hikimar da aka duba wajen yin wannan hadi, ana da tabbacin zai dinke rarrabuwar kawunan da aka daɗe ana fama da ita.

Source: Facebook
Ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da Arise News a ranar Laraba 15 ga watan Yuli, inda ya kara da cewa sun mara wa Obi baya ne saboda akwai yakinin zai ceto Najeriya.
Buba: Obi, Kwankwaso za su hada kan Najeriya
Jaridar Daily post ta ruwaito cewa Buba Galadima ya ce Kwankwaso ya goyi bayan Peter Obi ne saboda sun yi imanin cewa haɗin nasu zai inganta zaman lafiya tsakanin Arewa da Kudu maso Gabas.
Ya ce:
"Mun yi imanin wannan shi ne tikitin da zai ceci Najeriya. Ba wai ceton ƙasa kaɗai ba, amma tikitin da muke kira 'tikitin warkarwa' ne domin mu manta da abubuwan da suka faru a baya."
Buba Galadima ya ƙara da cewa manufarsu ita ce samar da sulhu tsakanin yankunan biyu, yana mai cewa bai kamata a ci gaba da kallon Obi a matsayin ɗan takarar ƙabilar Igbo ba, sai dai a matsayin ɗan takarar Najeriya baki ɗaya.
Yadda aka cimma matsaya tsakanin Obi, Kwankwaso
Ya kuma ce sun shafe sama da shekaru biyu suna aiki kan wannan shiri tare da wasu fitattun 'yan siyasa daga Kudu maso Gabas, lamarin da ya taimaka wajen rage rashin jituwar da ake samu tsakanin yankunan.
Injiniya Buba Galadima ya yi watsi da masu cewa haɗin Obi da Kwankwaso dabarar siyasa ce kawai domin a ci zaɓe, yana mai cewa manufar ita ce sake gina amana tsakanin al'ummomin Najeriya.

Source: Facebook
A cewarsa, Peter Obi ya yi alkawarin cewa idan ya zama shugaban ƙasa, zai ba da fifiko ga magance matsalolin tsaro, noma da ilimi, musamman a Arewacin Najeriya.
Ya ce:
"Peter Obi ya amince cewa idan ya zama shugaban Najeriya, zai jagoranci magance waɗannan matsaloli, kuma zai haɗa mu cikin masu tsara hanyoyin warware su."
Buba Galadima ya gayyaci Atiku
A baya, kun samu labarin cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Peter Obi sun sauya sheka zuwa jam'iyyar NDC bayan sun raba gari da da ADC a lokacin da ake rade-radin tsayar da Atiku Abubakar takara.
Sai dai jagororin biyu sun bayyana cewa dalilin barin ADC ba shu da alaka da batun takara, illa sun gano akwai matsala a shari'ar da jam'iyyar ke ciki da kuma rigingimun shugabanci da ake fama da shi bayan an hade.
Amma jigo a NDC, Buba Galadima, ya yi wa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, tayin shigowa sabuwar jam'iyyar inda ya gargadin cewa kada ya raba kan yan hadakar adawa.
Asali: Legit.ng


