Kasa Ta Rikice, Mawaki Davido Ya Fadi Yawan Miliyoyin da Yake Kashewa a Wata
- Fitaccen mawaki a Najeriya, David Adeleke ya yi magana game da abin da yake kashe a wata saboda tsadar rayuwa
- Mawakin wanda aka fi sani da Davido, ya bayyana cewa yana kashe makudan kudi kowane wata wajen tafiyar da rayuwarsa da aikinsa
- Davido ya ce wannan kudin bai hada da kashe-kashen da ake yi wa matarsa Chioma Adeleke, sauran iyalansa ba da sauran lamura
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Osogbo, Osun - Fitaccen mawaki a Najeriya, David Adeleke ya yi magana game da tsadar rayuwa a kasar.
Mawakin wanda aka fi sani da Davido, ya bayyana cewa yana kashe Naira miliyan 300 zuwa 400, a kowane wata.

Source: Twitter
Mawakin ya bayyana hakan ne yayin wani shirin kai tsaye da ya yi tare da fitaccen mai yada shirye-shiryen intanet, Davrel, cewar Punch.
Davido ya magantu kan matsin tattalin arziki
Shirin ya yi karin haske kan matsin tattalin arziki inda suka tattauna kan irin tsadar rayuwar fitaccen mawaki.
A cewar Davido, kudin da yake kashewa a kowane wata bai hada da kudaden da ake kashewa kan matarsa, Chioma Adeleke, ko sauran mutanen gidansa ba.
Davido ya kara da cewa wannan adadin bai hada da manyan sayayya irin su motocin alfarma da kayan ado masu tsada ba.
Ya ce:
"Ina kashe tsakanin dala 200,000 zuwa 300,000 a kowane wata, kuma wannan bai hada da kudin da ake kashewa kan matata ko sauran mutanen gidana ba.
"Haka kuma wannan bai hada da kudin sayen motocin alfarma da kayan ado ba."

Source: Instagram
Davido ya magantu kan kudade da yake kashewa
Davido, wanda yake cikin manyan mawakan Afirka da suka yi fice a duniya, ya sha bayyana cewa kula da aikinsa yana bukatar makudan kudade, cewar Pulse.
A cewarsa, tafiye-tafiye zuwa kasashe daban-daban, samar da tsaro, biyan albashin ma'aikata, harkokin sufuri da sauran al'amuran kasuwancinsa na daga cikin abubuwan da ke kara yawan kudin da yake kashewa.
A cewar Davido, kudaden da yake kashewa suna raguwa sosai idan yana zaune a Amurka, saboda yana rayuwa cikin kwanciyar hankali tare da iyalansa.
"Ya danganta da inda nake. Ina kashe kudi kadan idan ina Amurka, saboda ni kadai nake tare da matata da 'ya'yana."
Sai dai mawakin ya bayyana cewa kudaden da yake kashewa suna karuwa matuka idan yana wajen Amurka.
Ya ce hakan na faruwa ne saboda yawan ayyukansa, tafiye-tafiyensa akai-akai da kuma rayuwarsa mai cike da cudanya da jama'a.
Bayanan da Davido ya bayyana sun bazu cikin sauri a kafafen sada zumunta, inda suka jawo martani daga magoya bayansa da dama.
Oluremi ta roki Davido game da talakawa
A wani labarin, an ji cewa uwargidan shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta bukaci Burna Boy, Davido da Asake su kafa gidauniyoyi domin taimaka wa talakawa.
Ta ce Najeriya na da attajirai da dama, amma ya kamata su ƙara ba da gudummawa saboda nauyin da ke kan gwamnati.
Uwargida shugaban kasar ta kuma sanar da tallafin Naira miliyan 100 ga ƙananan ƴan kasuwa 2,000 a jihar Kogi wanda aka ce ya taimaka matuka ga al'umma.
Asali: Legit.ng

