Gwamna Inuwa Ya Yi Babban Sauyi a Gwamnatin Gombe, Ya Hade Wasu Ma'aikatu

Gwamna Inuwa Ya Yi Babban Sauyi a Gwamnatin Gombe, Ya Hade Wasu Ma'aikatu

  • Gwamna Muhammadu Yahaya ya ce gwamnatinsa za ta fara aiwatar da shawarwarin kwamitin da ya yi nazari kan gyaran ilimin firamare da na fasaha
  • Gwamnatin jihar Gombe ta haɗe Ma’aikatar Ilimi da Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi domin inganta daidaita ayyuka da aiwatar da manufofi
  • Gwamnan ya ce za a ci gaba da saka hannun jari a fannin ilimi domin inganta koyo da samar da ƙwararrun ma’aikata a dukkan fadin jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida

Gombe – Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Yahaya, ya ce gwamnatinsa za ta fara aiwatar da shawarwarin da ke cikin rahoton kwamitin da ya yi nazari kan gyara da farfaɗo da ilimin firamare da na fasaha a jihar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne ranar Juma’a yayin da yake karɓar rahoton kwamitin da aka kafa domin duba hanyoyin sake fasalin da kuma farfaɗo da ilimin firamare da na fasaha a jihar.

Kara karanta wannan

Gwamna Sule ya fadi babban abin da yake so a rika tuna shi bayan barin mulki

Gwamna Inuwa Yahaya ya hade wasu ma'aikatun ilimi
Gwamna Inuwa Yahaya ya na jawabi ga manema labarai a taron kungiyar gwamnoni. Hoto: @IsmailUMisilli
Source: Twitter

An gabatar da rahoton ilimin Gombe

Tom Maiyashi, ɗaya daga cikin mambobin kwamitin kuma ƙwararren masani kan ilimi, ne ya gabatar da rahoton tare da Kwamishiniyar Ilimi kuma shugabar kwamitin, Dakta Aishatu Maigari, in ji rahoton Punch.

Yahaya ya bayyana rahoton a matsayin wani muhimmin tsari da zai taimaka wajen sauya fasalin tsarin ilimi a jihar.

Ya tabbatar da cewa gwamnatinsa ba za ta ajiye rahoton ba tare da ɗaukar mataki ba.

“Game da rahoton, ina so in tabbatar muku cewa ba za mu yi watsi da wannan takarda ba. Za mu nazarce ta nan take sannan mu fara aiwatar da shawarwarin da ke cikinta,” in ji gwamnan.

Gwamnati ta haɗe ma’aikatun ilimi

Gwamna Yahaya ya bayyana cewa tuni gwamnatinsa ta fara wasu sauye-sauye a tsarin gudanar da harkokin ilimi a jihar.

Ya ce daga cikin matakan da aka ɗauka akwai haɗe Ma’aikatar Ilimi da Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi zuwa ma’aikata guda ɗaya.

Kara karanta wannan

2027: Pantami ya fadi abubuwan da zai yi wa Gombe idan ya zama gwamna

A cewarsa, matakin na daga cikin sauye-sauyen da ake yi domin ƙarfafa haɗin gwiwa, inganta aiwatar da manufofi da kuma samar da ingantaccen aiki a fannin ilimi.

Ya bayyana cewa:

“Za mu yi wasu sauye-sauye a tsarin fannin ilimi. Zan iya cewa mun riga mun fara, saboda yanzu na haɗe Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi da Ma’aikatar Ilimi suka zama ma’aikata guda ɗaya, kamar yadda ake yi a matakin tarayya."

An tsara inganta ilimin Gombe

Gwamnan ya ce sauye-sauyen wani ɓangare ne na ƙoƙarin sake fasalin fannin ilimi domin ya dace da ajandar ci gaban jihar na shekaru 10.

Ya ƙara da cewa gwamnatinsa na da niyyar ɗaukar manyan matakan manufofi da za su taimaka wajen inganta sakamakon karatu da kuma samar da ƙwararrun ma’aikata da za su iya fuskantar buƙatun nan gaba.

Jaridar Leadership ta rahoto cewa Yahaya ya kuma waiwayi halin da fannin ilimi yake ciki lokacin da gwamnatinsa ta hau mulki a shekarar 2019.

Ya ce tun daga lokacin gwamnati ta aiwatar da wasu shirye-shirye da suka shafi gine-ginen makarantu, bunƙasa ƙwarewar malamai, ƙara yawan ɗalibai da kuma inganta damar samun ilimi mai inganci.

Kara karanta wannan

Jagorori sun hadu a Masar bayan an gano ƙaruwar ƙin Musulmi a Duniya

“Mun san irin halin da muka tarar da wannan fanni lokacin da muka hau mulki a shekarar 2019, kuma muna gode wa Allah da muka samu damar cimma abubuwa da dama. Ina so in sake jaddada alkawarin da na yi cewa za mu bar Gombe cikin yanayi mafi kyau fiye da yadda muka same ta a fannin ilimi,” in ji shi.
Gwmana Inuwa Yahaya ya ce zai ci gaba da zuba jari a fannin ilimi
Gwamna Inuwa Yahaya yana magana a lokuta da wurare daban daban. Hoto: @GovernorInuwa
Source: Twitter

Kwamitin ya nemi a gaggauta aiki

Da yake gabatar da rahoton a madadin kwamitin, Maiyashi ya yabawa Gwamna Yahaya kan kafa kwamitin da kuma ba shi goyon bayan da ya dace domin gudanar da aikinsa.

Ya ce rahoton ya kunshi nazari na gaskiya kan matsalolin da ke addabar ilimin firamare da na fasaha a Gombe.

Maiyashi ya bayyana cewa shawarwarin da kwamitin ya gabatar suna da amfani kuma za a iya aiwatar da su.

Ya kuma buƙaci gwamnatin jihar ta gaggauta sauya shawarwarin daga matakin tsara manufofi zuwa matakin aiwatarwa domin a samu sauyi a fannin ilimi.

Gwamna Abba ya hade wasu ma'aikatu

A wani labari, mun ruwaito cewa, Gwamnatin Kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Yusif ta dauki matakin hade wasu ma'aikatu guda biyu a wuri guda.

An hade ma'aikatar albarkatun ruwa da ma'aikatar muhalli da canjin yanayi wuri guda ta yadda za su ci gaba da gudanar da ayyukansu.

Matakin hadewar dai na zuwa ne bayan a kwanakin baya kwamishinan da ke kula da ma'aikatar ruwa ya yi murabus daga mukaminsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com