Gwamnatin Tinubu Ta Fadi Yadda ake Kashe Tulin Bashi da ake Laftowa Najeriya
- Fadar Shugaban Kasa ta kare manufar karɓo bashi ta Bola Tinubu ke yi, wanda ya fara jawo maganganu daga yan adawa da masu sharhi
- Hadimin Shugaban kasa, Bayo Onanuga ya bayyana cewa ana ganin inda kuɗin ke tafiya ta hanyar manyan ayyukan more rayuwa
- Bayo Onanuga ya lissafo wasu ayyuka da ya kira manya-manya, wanda ya ce kadan ne daga cikin hanyoyin da Tinubu ke kashe basussukan da ya amso
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Fadar Shugaban Ƙasa ta kare manufar shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, na karɓo bashi, tana mai cewa manyan ayyukan more rayuwa da ake gani a jihohin Najeriya sun tabbatar da cewa ana amfani da kuɗin bashin wajen ci gaban ƙasa.
Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ne ya bayyana haka a ranar Alhamis yayin rangadin duba ayyukan gwamnatin tarayya da aka gudanar a jihar Benuwai.

Source: Facebook
The Nation ta wallafa cewa kungiyar RHA mai goyon bayan Tinubu tare da haɗin gwiwar tawagar yada labaran Fadar shugaban kasa ta shirya rangadin domin nuna ayyukan gwamnatin tarayya da na jihohi.
An fara nuna ayyukan Tinubu
The Guardian ta kawo labarin cewa bayan duba gadar Buruku da ke kan kogin Katsina-Ala, Onanuga ya ce zuba jari da gwamnati ke yi a tituna, gadoji da masana'antu amsa ce ga masu sukar yadda gwamnati ke karɓo bashi.
Ya ce:
"A matsayinsu na 'yan Najeriya, muna ganin ana zargin gwamnati da karɓo bashi. Amma kuma muna iya ganin inda kuɗin ke tafiya; wajen gina ababen more rayuwa, haɗa mutanen da aka manta da su, tabbatar da kasuwanci yana gudana cikin sauƙi da kuma bai wa manoma damar kai amfaninsu kasuwa kai tsaye."
Onanuga ya bayyana cewa gadar Buruku mai tsawon mita 854 tana daga cikin gadoji biyar da gwamnatin tarayya ke ginawa a jihar Benuwai.

Kara karanta wannan
Atiku da Peter Obi sun tafka kuskure, an cire su daga barazanar da Tinubu zai fuskanta a 2027
Gwamnatin Tinubu na saukaka zirga-zriga
Ya ce idan an kammala ta za ta sauƙaƙa zirga-zirga tsakanin jihohin Benuwai, Taraba da Adamawa, tare da samar da muhimmin hanyar tattalin arziki tsakanin yankin Arewa ta Tsakiya da Arewa maso Gabas.
Ya nuna gamsuwa da yadda aikin ke tafiya, inda jami'ai suka tabbatar masa cewa babu matsalar kuɗi saboda ana ɗaukar nauyin aikin ne ta Renewed Hope Infrastructure Fund.

Source: Facebook
Bayo Onanuga ya ƙara da cewa:
"Wannan aiki zai amfani kowa ta fuskar tattalin arziki."
Mai kula da ayyukan ma'aikatar ayyuka ta tarayya a jihar Benuwai, Engr. Mukaila Danlandi, ya ce an fara aikin gadar ne a shekarar 2023, kuma ana sa ran za a kammala shi zuwa Disambar 2027.
An yi wa Tinubu alkawarin kuri'a
A baya, kun samu labarin cewa Mataimakin Gwamnan Jihar Benue, Samuel Ode, ya ce jihar na da shirin samar wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu kuri'u miliyan 1 a zaben shugaban ƙasa na 2027.
Ya ce gwamnatin Gwamna Hyacinth Alia za ta tattara mambobin Majalisar Zartarwa ta jihar da al'ummar Benue domin tabbatar da cika wannan alƙawari a babban zaben da ake sa ran yi nan da wasu watanni.
Ode ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis 7 Agusta, 2026 yayin da yake jagorantar tawagar Sashen Sadarwa na Fadar Shugaban Ƙasa, ƙarƙashin jagorancin Bayo Onanuga inda ake nuna ayyukan Tinubu.
Asali: Legit.ng

