Za a shigo da kayan noma na zamani Najeriya

Za a shigo da kayan noma na zamani Najeriya

Majalisar dattawa ta bayyana cewa kudurin da za a gabatar da bunkasa harkar noma a kasar nan zai taimaka mutuka wurin habaka tattalin arziki, sannan zai taimakawa manoma da kayan aikin irin na zamani

A jiya ne 'yan majalisar dattawa, suka tabbatar da cewa idan kudurin bunkasa harkar noma a kasar nan ya tabbata, zai kawo cigaba sosai ga tattalin arzikin kasar nan.

A cewar Sanatocin, idan kudurin ya tabbata, zai bayar da hanyar fara noma na zamani a fadin kasar na, musamman ma wuraren da suke da kasar noma mai kyau.

A lokacin da ya ke jawabi a Abuja, bayan ya karbi kyautar girmamawa a wani taro da suka gudanar, shugaban kwamitin, Sanata Sabi Abdullahi (APC Niger), ya ce: "Manoman mu na wannan lokacin ba su da niyyar yin amfani da kayan noman da suka gada a wurin iyaye da kakanni.

Za a shigo da kayan noma na zamani Najeriya
Za a shigo da kayan noma na zamani Najeriya
Asali: Depositphotos

"Sun fi son hanyar noma ta zamani, da zasu dinga gabatar da noman su cikin sauki. Kuma hakan ba zai taba yiwuwa ba, ba tare da an gabatar da dokar hakan a kasa ba.

A binciken dana gabatar akan kasashen da suka samu cigaba a harkar noma irin s, Philippines, Malaysia, Singapore, India, Srilanca, Thailand da sauran kasashe na yanki Asia, ina da tabbacin cewa idan har aka gabatar da wannan kudurin a Najeriya, harkar noma zata bunkasa kwarai da gaske." A binciken dana gabatar akan kasashen da suka samu cigaba a harkar noma irin s, Philippines, Malaysia, Singapore, India, Srilanca, Thailand da sauran kasashe na yanki Asia, ina da tabbacin cewa idan har aka gabatar da wannan kudurin a Najeriya, harkar noma zata bunkasa kwarai da gaske."

Ku Karanta: Jerin Ministocin da shugaba Buhari zai koma mulki da su

Za mu kawo harkar noman zamani a kasar nan, sannan zamu dinga amfani da ita a kowanne lungu da sako na kasar nan, domin manoma su ci ribar abubuwan da suke nomawa.

Sanata Abdullahi, ya bayyana cewa idan har manoma za su bi yadda doka ta tsara wurin sayar da kayayyakin gonarsu, ya ce za su dinga samun riba mai yawa a harkar noma.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng