PFIPC: Manyan Jami'ai da Hukumomi 9 da Ake Zargin Suna da Laifi a Kafa Hukumar Bogi

PFIPC: Manyan Jami'ai da Hukumomi 9 da Ake Zargin Suna da Laifi a Kafa Hukumar Bogi

Abuja, Nigeria - Rahotanni sun nuna a cewa abubuwa sun fito fili kan yadda zargin sojan gona mai ban tsoro da ba-zata, wacce aka ce Adeniyi Adeyemi ya tafka, ta ratsa manyan ma'aikatun gwamnatin tarayya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Adeyemi ya nuna kansa a matsayin shugaban wata hukuma mai suna Presidential Foreign Intervention Promotion Council (PFIPC), wacce fadar shugaban kasa ta ce ta bogi ce.

Adeniyi Adeyemi.
Shugaban hukumar da ake zargin ta bogi ce, Adeniyi Adeyemi Hoto: @IkeGod
Source: Facebook

Rahoton bincike na Bussines Day ya gano cewa wasu manyan ma'aikatan gwamnati da hukumomi sun sanya hannu kan wasu takardu da suka taimaka wa Adeyemi wajen kafa wannan hukuma.

A wannan rahoton, mun tattaro muku jerin jami'an gwamnatin tarayya da hukumomin da ake dakon amsa daga gare su kan yadda suka taka rawa wajen kafa wannan hukuma ta bogi.

1. Femi Gbajabiamila

Adeniyi Adeyemi ya yi ikirarin cewa takardar da ta ba shi damar kama aiki a matsayin shugaban hukumar PFIPC ta fito ne kai tsaye daga hannun shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila.

Kara karanta wannan

Ma'aikatar bogi: Kujerun manyan jami'an Tinubu na rawa, ana kira a kore su

Wannan ikirari ya jefa babban jami'an fadar shugaban kasa cikin tsakiyar wannan badakala ta sojan gona, kamar yadda Tribune Nigeria ta kawo.

Duk da cewa Gbajabiamila ya musanta bada takarda kuma ya rubuta wa hukumomin tsaro wasika tun a watan Oktoba 2025 domin a binciki Adeyemi, rahotanni sun nuna cewa har yanzu ba a tantance sa hannunsa da ke jikin takardar ba.

Bugu da kari, an tsananta tambayoyi kan dalilin da ya sa fadar shugaban kasa ta yi shiru na tsawon watanni shida ba tare da an fitar da sanarwar gargadi ga jama'a ba, har sai a watan Yuni 2026.

Femi Gbajabiamila.
Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila a bakin aiki a ofishinsa Hoto: Femi Gbajabiamila
Source: Twitter

2. Ofishin kasafin kudin tarayya

Ɗaya daga cikin abubuwan da suka fi ba da mamaki a wannan badakala shi ne yadda wata hukuma ta bogi ta samu lambar kasafin kudi har aka amince da kudadenta a cikin kasafin 2026.

Wannan lamari ya janyo tambayoyi game da mutanen da ke da alhakin tantancewa da bada lambobin kasafin kudi a fadar shugaban kasa, da kuma yadda aka yi aka tsallake tsauraran matakan tantancewa ba tare da an gano cewa hukumar ta jabu ce ba.

Kara karanta wannan

Abu ya girma: Shugaba Tinubu ya ba ICPC umarni kan ma'aikatar bogi

Ya zuwa yanzu, gwamnatin tarayya da rundunar 'yan sanda da ke binciken lamarin ba su fito sun ba da amsar wanda ya sanya hukumar a kasafin kudin ba.

3. Nnamdi Mbaeri (Ofishin OSGF)

Takardun bincike sun nuna cewa Nnamdi Mbaeri, a lokacin da yake Babban Sakatare a Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya (OSGF), ya sanya hannu kan wata wasika a ranar 21 ga Nuwamba 2024 yana neman a samar wa PFIPC ofis na aiki.

Mbaeri ya aike da wannan takarda ne zuwa ga shugaban hukumar EFCC, inda yake bukar a ware wa hukumar ta Adeyemi ofis daga cikin gine-ginedan gwamnati da hukumar ta kwato.

Rahoton This Day ya nuna cewa kafin a gano badakalar, Mbaeri ya yi ritaya daga aiki a watan Yulin 2025, wanda hakan ya sa ake ganin ya kamata ya amsa tambayoyi.

4. Nadungu Gagare (Ofishin OSGF)

A ranar 24 ga Yuni 2025, wani babban jami'i a ofishin OSGF, Nadungu Gagare, ya rubuta wasikar gayyata zuwa ga Adeyemi, inda ya girmama shi a matsayin "Darakta Janar" na hukumar PFIPC.

A cikin wasikar, Gagare ya gayyaci Adeyemi ne domin shiga tawagar da za ta wakilci Najeriya a taron Canada-Africa Fintech Summit da aka gudanar a kasar Kanada a watan Agustan 2025.

Kara karanta wannan

Ma'aikatar bogi: Gbajabiamila ya yi barazana kan Adeyemi, zai nemi N10bn

Gagare ya yi amfani da sunan ajandar "Renewed Hope" ta Shugaba Tinubu wajen aiko da gayyatar, hakan ya sa ake neman jami'in da ya yi bayanin yadda ya san da zaman hukumar ta bogi.

5. George Akume (SGF)

Ana ganin ya kamata Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume, ya fito fili ya yi wa al'umma bayanin yadda aka tafka wannan gagarumar badakala a lokacinsa ba tare da ya ankara ba, cewar rahoton Punch.

Ofishin SGF shi ne kadai ke da ikon fitar da takardun nadin mukamai na irin wadannan hukumomi, kuma ofis din bai taba fitar wa Adeyemi takarda ba, amma kuma ma'aikatan ofis din sun rika amsa bukatun Adeyemi.

Akume.
Sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume Hoto: @Akume
Source: Twitter

6. Jami'an da suka bude asusun CBN

A ranar 29 ga Yuli 2025, wasu jami'ai a Ofishin Akanta Janar na Tarayya (OAGF) sun rubuta wasika zuwa ga Babban Bankin Najeriya (CBN) domin a bude wa hukumar ta PFIPC asusun ajiya na kudaden kasashen waje.

Rahoton Premium Times ya ce daraktan sashen ayyukan banki na CBN, Hamisu Abdullahi, ya amsa wasikar inda ya tabbatar da bude asusun ajiya guda biyu na kudin Dala da Fam domin amfanin hukumar ta jabu.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun cafke mahaifin wanda ya kafa ma'aikatar bogi a gwamnatin Tinubu

Wannan mataki ya janyo tambayoyi a kan dalilin da ya sa CBN bai gudanar da binciken sanin wane ne abokin ciniki (KYC) ba, da kuma rashin neman dokar da ta kafa hukumar kafin su bude mata asusu.

7. Dauda Abdulhamid (Ofishin OAGF)

A ranar 28 ga watan Agusta 2025, Dauda Abdulhamid, wanda shi ne Daraktan Gudanarwa a Ofishin Akanta Janar na Tarayya (OAGF), ya sanya hannu kan takardar tura ma'aikatan gwamnati sama da 300 zuwa wuraren aiki daban-daban.

A cikin wannan tsari na tura ma'aikata, Abdulhamid ya amince da tura jmi'an kula da baitulmali guda uku (3) zuwa wannan hukuma ta bogi, PFIPC domin su fara aiki.

Wannan tura ma'aikata ya nuna yadda tsarin hukumar bogi ta Adeyemi ta yi nasarar samun ma'aikatan gwamnati na gaske da za su rika gudanar da ayyuka a cikinta.

8. Rundunar 'Yan Sandan Najeriya

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta kammala bincikenta a kan wannan batu cikin sauri tsakanin ranar 23 ga Oktoba zuwa 13 ga Nuwamba 2025, kuma ta shigar da tuhume-tuhume a gaban kotu a ranar 27 ga Nuwamba 2025.

Sai dai kuma, jinkirin da aka samu wajen fara sauraron shari'ar ya janyo shakku, ganin cewa an sanya ranar farko ta zaman kotun ne a ranar 27 ga Yuli 2026, wato watanni takwas bayan shigar da karar.

Kara karanta wannan

Komai zai fito: APC na shirin fitar da bayanan mataimakin Tinubu a 2027

Sufeto
Sufeto Janar na rundunar yan sandan Najeriya, Tunji Disu Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

9. Shugaban NITDA, Kashifu Inuwa

Hukumar Bunƙasa Fasahar Sadarwa ta Kasa (NITDA) a karkashin jagorancin Kashifu Inuwa, ita ce ta ba wa PFIPC damar yin amfani da adireshin yanar gizo na gwamnati, wato pfipc.gov.ng.

Wani matashi da yake kokarin bankado rashin gaskiya a shafinsa X, Henry Shield ya tabbatar da cewa hukumar tana da adireshin yanar gizo.

Binciken na'ura na "WHOIS" ya gano cewa masu kula da shafukan yanar gizo na NITDA ne da kansu suka amince da kirkirar sahfin a ranar 30 ga Satumba 2024, kodayake shafin ya daina aiki bayan badakalar ta bulla.

Kamar yadda doka ta tsara, adireshin .gov.ng na halastattun hukumomin gwamnati ne kawai, don haka daukacin 'yan kasa suna jiran NITDA ta bayyana irin tantancewar da ta yi kafin ta bai wa hukumar bogi wannan kariya ta intanet.

Tinubu ya fara daukar mataki

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya ba hukumar ICPC umarnin bincike kan hukumar PFIPC da ake ta cece-kuce a kanta.

Kara karanta wannan

Umarnin da fadar shugaban kasa ta ba DSS, EFCC kan batun ma'aikatar bogi

Shugaba Tinubu ya umarci cewa a kammala binciken sannan a mika masa cikakken rahoto duka abubuwan da aka gano cikin tsawon kwanaki 30.

Tinubu ya jaddada cewa dole ne a kare martabar fadar shugaban kasa da kuma cibiyoyin gwamnatin tarayya daga kowane irin aikin damfara da karya doka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262