Kwankwaso Ya Yi Magana da Limaman Katolika Suka Cire Tsoro, Sun Ja da Tinubu

Kwankwaso Ya Yi Magana da Limaman Katolika Suka Cire Tsoro, Sun Ja da Tinubu

  • Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yaba wa taron limaman Katolika kan bayyana halin da Najeriya ke ciki duk da sun sa labule da Bola Tinubu
  • Fastocin da Gwamnatin Tarayya na ci gaba da musayar yawu bayan limaman cocin sun nemi Bola Tinubu ya yi aikin da aka zabe shi na ci gaban kasa
  • Daga cikin martaninsa, kwankwaso ya bukaci shugabanni su mayar da hankali kan walwala da tsaron al'umma tare da tabbatar da gaskiya a mulki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar NDC a zaben 2027, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya yaba wa Taron Limaman Cocin Katolika na Najeriya (CBCN).

Ya ce shugabannin cocin sun yi kokari matuka saboda bayyana damuwarsu kan tsadar rayuwa da matsalolin rashin tsaro da suka addabi kasar.

Kara karanta wannan

INEC ta yi fatali da sanya sojoji a tsarin zaben Najeriya, an ji dalili

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bi bayan limaan katolika
Shugaban kasa Bola Tinubu, Rabiu Musa Kwanwaso Hoto: Bayo Onanuga/Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Twitter

Kwankwaso ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafukansa na sada zumunta da suka hada da Facebook a daren Laraba, 4 ga watan Yuli, 2026.

Kwankwaso ya jinjinawa Fastoci

'Dan takara a zabe mai zuwa ya ce limaman sun nuna jarumtaka da kishin kasa ta hanyar jawo hankalin jama'a da gwamnati kan hakikanin kalubalen da 'yan Najeriya ke fuskanta.

A cewarsa, matsalolin da cocin ta bayyana ba batun siyasa ba ne, illa dai suna wakiltar irin wahalhalun da talakawan Najeriya ke ciki a kullum.

Ya ce korafe-korafen da suka shafi tashin farashin kayayyaki, tabarbarewar tsaro, raguwar amincewar jama'a ga gwamnati da kuma wahalhalun da miliyoyin mutane ke fuskanta, suna bayyana abin da ke faruwa a kusan dukkan sassan kasar nan.

Rabiu Musa Kwankwaso ya kara da cewa duk da yalwar albarkatun kasa da na dan Adam da Najeriya ke da su, har yanzu miliyoyin 'yan kasa na fama da tsananin matsin tattalin arziki, rashin aikin yi da kuma matsalolin tsaro.

Kara karanta wannan

Karfin hali: Yadda aka kama mutum 2 da zargin cefanar da filayen gwamnatin Kano

Kwankwaso ya fadi wasu matsalolin Najeriya

Ya kuma bayyana cewa karancin samun ingantaccen ilimi da kiwon lafiya, tare da karancin damar ci gaba, na daga cikin manyan kalubalen da ke addabar al'umma.

Tsohon gwamnan jihar Kano ya ce wadannan matsaloli na bukatar daukar matakin gaggawa, cikin gaskiya da kuma fifita bukatun jama'a daga duk wanda aka dora wa amanar shugabanci.

Rabiu Musa Kwankwaso ya nemi a ci gaba da fada wa shugabanni gaskiya
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, dan takarar Mataimakin Shugaban kasa a NDC Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Facebook

Haka kuma ya bukaci 'yan Najeriya su ci gaba da tattaunawa da shugabanni cikin lumana da mutunta juna a duk lokacin da aka samu dama.

Ya ce ya kamata jama'a su ci gaba da neman shugabanci nagari, tabbatar da rikon amana da kuma manufofin da za su fifita tsaro, walwala da ci gaban al'umma.

Kwankwaso ya kwashe mutanen Abba

A wani labarin, kun ji cewa Mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NDC, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya karɓi wasu masu sauya sheƙa daga jam'iyya mai mulki na APC.

Sanata Rabiu Kwankwaso ya tabbatar musu da cewa za su samu adalci da kuma matsayi mai kyau a cikin jam'iyyar bayan komawarsu duk da sun baro inda ake da mulki a hannu.

Karɓar masu sauya sheƙar na zuwa ne yayin da jam'iyyar adawa ta NDC ke ƙoƙarin faɗaɗa tasirinta a Kano gabanin zaɓen 2027 domin ta tunkari gwamnatin da Abba Kabir Yusuf ke jagoranta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng