‘A Je Kotun Mana’: ‘Shugaban’ Hukumar PFIPC da Ake Zargin Ta Bogi Ce Ya Magantu

‘A Je Kotun Mana’: ‘Shugaban’ Hukumar PFIPC da Ake Zargin Ta Bogi Ce Ya Magantu

  • Wanda ake zargi da kirkirar hukuma ta bogi a Najeriya, Adeniyi Adeyemi ya dage cewa nadin da aka yi masa gaskiya ne
  • Adeyemi ya ce shari'ar tana gaban kotu, yana da takardar nadinsa kuma yana da kwarin gwiwar cewa kotu za ta wanke shi daga zarge-zarge
  • Fadar Shugaban Ƙasa ta ce Adeyemi ɗan damfara ne, tana zarginsa da ƙirƙirar hukuma, jabun takardu da buɗe asusun banki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Prince Adeniyi Adeyemi, wanda ake zargi da gabatar da kansa a matsayin Darakta Janar na hukumar PFIPC ya yi magana.

Shugaban hukumar PFIPC da ake zargin da bogi ce da aka kirkira ya dage cewa nadin da aka ba shi na gaskiya ne.

Gwamnatin Tinubu ta barranta kanta da wanda ya kirkiri sabuwar hukuma
Shugaban hukumar PFIPC da ake zargin ta bogi ce, Adeniyi Adeyemi. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Facebook

Ya bayyana hakan ne a yayin wata tattaunawa ta wayar tarho a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels TV.

Kara karanta wannan

Yadda shugaban ma'aikatar bogi ya rika tarurruka da manyan jami'an gwamnatin Tinubu

Adeyemi ya nuna karfin hali

Adeyemi, wanda ake tuhuma da haɗa baki, yin jabun takardu da kuma kwaikwayon mukami, ya ce shari'ar ta riga ta kai gaban kotu, yana kuma da kwarin gwiwar cewa za a wanke shi.

Game da ko yana shirye ya fuskanci shari'a, ya ce idan yana da laifi kotu ta hukunta shi, idan kuma ba shi da laifi kotu ta tabbatar da adalci.

Ya ce tun da shari'ar tana gaban kotu, yana son kotun da ke da hurumin sauraron shari'ar ta wanke sunansa, domin ya shirya tsaf don kare kansa.

Adeyemi ya ƙara da cewa yana da takardar nadi, amma ba zai iya yin ƙarin bayani ba saboda shari'ar tana kotu, yana kuma karɓar magani saboda rashin lafiya.

Yayin da yake jawabi ga 'yan Najeriya, ya nuna shakku kan ikirarin cewa hukumar da ake magana a kanta ba ta wanzu ba.

Ya ce da ace hukumar ba ta wanzu ba, da bai yi ƙarfin halin zagayawa ma'aikatu da hukumomin gwamnati tsawon kusan shekara uku ba.

Kara karanta wannan

Canji ya tabbata, an bayyana sabon tufafin aikin bautar ƙasa na NYSC a Najeriya

An zargi Adeyemi na kirkirar hukumar bogi a Najeriya
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya yana jawabi. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

'Hakan ba zai yiwu a Najeriya ba' - Adeyemi

Adeyemi ya ce Najeriya ba ƙasa ba ce da za a iya gudanar da irin wannan aiki ba tare da hukuma ta san da shi ba.

Rahotanni sun ce ya shafe watanni yana gudanar da ayyukansa a ƙarƙashin sunan PFIPC, inda ofishinsa ya shirya manyan taruka tare da hulɗa da hukumomin gwamnati.

Bugu da ƙari, rahotanni da kalaman da ya yi a baya sun nuna cewa an ware wa majalisar kusan Naira biliyan 1.3 a kasafin kuɗin shekarar 2026.

PFIPC: Martanin fadar shugaban kasa

Sai dai Fadar Shugaban Ƙasa ta yi watsi da ikirarinsa cewa shi Darakta Janar ne, tana bayyana shi a matsayin ɗan damfara da ake tuhuma kan jabun takardu da kwaikwayon mukami.

A cikin wata sanarwa da Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Yaɗa Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar a Facebook, an ce binciken 'yan sanda ya gano Adeyemi ya ƙirƙiri takardar nadin shugaban ƙasa da aka jingina wa Femi Gbajabiamila.

Kara karanta wannan

An mika wa Tinubu rahoto kan kara wa shugaban kasa da masu mukaman siyasa albashi

Sanarwar ta ce ya kuma gudanar da wata hukuma ta bogi tare da buɗe asusun banki guda 34, ciki har da tara da aka buɗe da sunayen hukumomin gwamnati da ba su wanzu.

Atiku ya bukaci Tinubu ya kori Gbajabiamila

A wani labarin, an ji cewa dan takarar shugaban kasa a ADC, Atiku Abubakar ya nuna damuwa game da karuwar cin hanci da rashawa a Najeriya.

Atiku ya bukaci Shugaba Tinubu ya dakatar da Femi Gbajabiamila tare da binciken zargin karɓar Naira miliyan 400.

Gbajabiamila ya musanta sanin PFIPC ko naɗa Adeniyi Adeyemi, yayin da Adeyemi ke zarginsa da neman kaso daga kuɗin fara aikin hukumar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.