Magana Ta Fito, An Ji Asalin Dalilin Dakatar da Shugabannin Kananan Hukumomi 3 a Kano
- A jiya Talata ne Majalisar Dokokin Kano ta dakatar da shugabannin kananan hukumomin Rogo, Bebeji da Bagwai
- Rahotanni sun nuna cewa an dauki matakin ne bayan samun korafe-korafe daga kungiyoyi da zababbun kansiloli
- Ana zargin shugabannin da almundahana da kudaden gwamnati, cin zarafin mukamin da suke kai da cin amana
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - An samu ƙarin bayani game da dakatarwar da Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi wa shugabannin ƙananan hukumomin Rogo, Bebeji, da Bagwai.
Majalisar Dokokin Jihar Kano ta fito karin bayanai kan dakatar da shugabannin kananan hukumomin uku, inda ta ce matakin ya biyo bayan wasu korafe-korafe da suka shafi zargin rashin da’a ta bangaren kudi da gudanarwa.

Source: Facebook
Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar, Lawan Hussaini Dala, ne ya bayyana hakan a wata tattaunawa da ya yi da jaridar Daily Trust.
Ya ce an samu korafe-korafen ne daga bangarori daban-daban da suka hada da kungiyoyin al’umma, kungiyoyin farar hula da kuma zababbun kansilolin kananan hukumomin da abin ya shafa.
Dalilin dakatar da shugabanni uku
Majalisar ta dakatar da Abubakar Mustapha na Rogo, Dr. Alhassan Salisu na Bebeji da Bello Gadanya na Bagwai bayan amincewa da rahoton Kwamitin Kananan Hukumomi da Harkokin Sarauta yayin zamanta.
Hon Lawan Dala ya bayyana cewa kwamitin ya yi nazari na farko kan korafe-korafen ta hanyar duba bayanan kudi da gudanarwa da aka samo daga kananan hukumomin, tare da gudanar da tattaunawa da manyan jami’an hukumomin.
A cewar shugaban masu rinjaye, korafe-korafen sun kunshi zargin karkatar da kudaden gwamnati, cin zarafin mukami, karya amana, zamba da wasu kura-kuran gudanarwa.
Ya ce ana kuma zargin shugabannin da rashin iya tafiyar da harkokin kananan hukumominsu da kuma karkatar da kudaden jama’a domin amfanin kansu.
“Binciken bai kammala ba tukuna,” in ji Dala.

Kara karanta wannan
Kano: Halin da kadarorin Malami ke ciki bayan kotu ta kwace su saboda almundahana
Ya kara da cewa kwamitin zai fadada bincikensa ta hanyar gayyatar dukkan masu ruwa da tsaki domin gabatar da hujjoji tare da kare matsayinsu kafin fitar da shawarwarin karshe.
An nada wadanda za su maye gurbinsu
Lawan Dala ya ce bisa ikon sa ido da kundin tsarin mulki ya bai wa majalisa, an umurci Ma’aikatar Kananan Hukumomi ta tabbatar da mika ragamar shugabanci ga mataimakan shugabannin kananan hukumomin uku har zuwa lokacin kammala bincike.
Ya bayyana cewa kwamitin na da watanni uku domin kammala aikin da aka ba shi tare da mika rahoto ga majalisar.
Bayan haka ne ‘yan majalisar za su tantance ko an tabbatar da zarge-zargen da ake yi wa shugabannin da aka dakatar ko kuma za a wanke su daga dukkan tuhuma.

Source: Facebook
Da Legit Hausa ta tuntube shi ta wayar tarho, mai magana da yawun majalisar dokokin Kano, Kamaluddeen Sani Shawai ya yi karin haske da cewa ciyamomin da aka dakatar na iya rasa kujerunsu gaba daya.
Ya ce ciyamomin na iya rasa kujerunsu gaba daya idan har aka tabbatar da sun aikata zarge zargen da ake yi masu.
Shawai ya ce:
"Idan har bincike ya tabbatar da wadannan zarge zargen haka suke,to za mu iya cewa za su iya sallama da kujerunsu, idan kuma bincike ya nuna akasin haka, to za su iya dawo wa kujerunsu kamar doka ka'ida ta tanadar."
Gwamnan Kano ya kafa tarihi a Arewa
A wani labarin, kun ji cewa gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf , ya kaddamar da hedikwatar Cibiyar Kula da Cututtuka ta Jihar Kano (KNCDC).
Haka zalika Gwamna Abba ya kuma bude cibiyar kula da masu cutar sikila ta Abba Care da ke Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad, irinta ta farko a fadin Arewacin Najeriya.
Asali: Legit.ng

