Sojoji Sun Yi gaba da gaba da 'Yan Bindiga a Kauyen Sokoto, An Yi Barin Wuta
- Dakarun rundunar sojin Najeriya sun kuɓutar da mutum 14 da aka yi garkuwa da su bayan sun fafata da ƴan bindiga a wata ƙaramar hukuma a Sokoto
- Sojojin sun kuma ƙwato shanu 195, tumaki 84, raƙuma biyu da babura biyu bayan maharan sun tsere sakamakon luguden wutar da aka yi musu
- Jami'an tsaro sun ce haɗin gwiwar al'umma da bayanan sirri ne suka taimaka wajen samun nasarar wannan samame a yankin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida.
Sokoto - Dakarun Rundunar Sojin Najeriya ta 8 Division Garrison sun kuɓutar da mutum 14 da aka yi garkuwa da su tare da ƙwato dabbobi 281 da aka sace bayan sun fafata da ƴan bindiga a ƙauyen Horo Birni da ke ƙaramar hukumar Shagari a jihar Sokoto.
Wata majiya mai tushe a harkokin tsaro ta tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a ranar Laraba, tana mai cewa an gudanar da samamen ne a ranar Talata bayan sojojin sun samu kiran gaggawa daga mazauna yankin.

Source: Twitter
Sojoji sun fatattaki ƴan bindiga
Majiyar ta bayyana cewa ƴan bindigar sun mamaye ƙauyen tare da yin awon gaba da mutane da kuma dabbobin al'umma kafin sojoji suka cimma su, in ji rahoton This Day.
Da isar sojojin, an yi musayar wuta mai ƙarfi, lamarin da ya tilasta wa maharan tserewa cikin rudani bayan sun samu raunukan harbin bindiga.
A sakamakon haka, sun yi watsi da mutanen da suka sace da kuma dabbobin da suka kwashe.
An kwato dabbobi 281
Vhannels TV ta rahoto cewa bayan fafatawar, sojojin sun ci gaba da sintiri a yankin, inda suka kuɓutar da dukkan mutum 14 da aka yi garkuwa da su.
Haka kuma, sun ƙwato shanu 195, tumaki 84, raƙuma biyu da babura biyu da ake zargin mallakin ƴan bindigar ne.
Majiyar ta ce an samu mutanen da aka ceto cikin ƙoshin lafiya, kuma tuni aka tsare su domin kammala tantancewa kafin a miƙa su ga iyalansu.
An yaba da haɗin gwiwar al'umma
Jami'in ya yabawa saurin martanin sojojin, yana mai cewa hakan ya hana asarar rayuka da dukiyoyi a yankin da ya sha fama da hare-haren ƴan bindiga a watannin baya.
Ya kuma ce haɗin gwiwar hukumomin tsaro da bayanan sirri da mazauna yankin suka bayar ne suka taimaka wajen samun nasarar samamen.

Source: Original
A cewarsa, dakarun sojoji a shirye suke koyaushe domin yaƙar ƴan bindiga da sauran masu aikata laifuka, amma sun bukaci al'umma su ci gaba da ba su haɗin kai da sahihan bayanai.
Wannan nasara na zuwa ne yayin da dakarun Operation FANSAN YAMMA ke ci gaba da gudanar da hare-hare kan ƴan bindiga a jihohin Sokoto, Zamfara da sauran sassan Arewa maso Yamma.
Asali: Legit.ng

