Aikin Gwamnatin Najeriya
Gwamnatin tarayya ta fara cire harajin N50 kan kowace mu'amalar kudi ta N10,000. Kamfanonin Opay da Moniepoint sun fara aiwatarwa daga 1 ga Disamba.
Legit Hausa ta lissafa ranakun hutu a Najeriya na Disamba 2024 da Janairun 2025. Wadannan sun hada da bukukuwan Kirsimeti, Ranar Dambe, da kuma na Sabuwar Shekara.
Ministan Kwadago, Dingyadi, ya bayyana cewa gwamnati za ta hana shiga yajin aiki ta hanyar tattaunawa da 'yan kwadago da samar da hanyoyin warwarewar matsaloli.
Hukumar Kididdiga ta Kasa (NPC), karkashin shugabanta, Nasir Isa Kwarra, ta sanar da cewa za a gudanar da kidayar jama’a a Najeriya a shekarar 2025.
Babban mai binciken kudi na tarayya (AGF) ya bankado yadda aka tafka badakalar kwangilar N197.72bn a ma’aikatu, da hukumomi. Ya fitar da cikakken rahoton badakalar.
Gwamnatin tarayya ta karyata ikirarin da Shehu Sani ya yi na cewa ta kori ma'aikatan tarayya da aka dauka aiki da digirin kasar Benin da Togo. Ta yi karin haske.
A rahoton nan kun ji asusun bayar da lamuni na duniya (IMF) ya sake matsayar da ya bayyana a kan manufofin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu kan tattalin aziki.
Fela Durotoye, tsohon hadimin Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa ya yi aiki a fadar shugaban kasa na tsawon watanni shida ba tare da an biya shi albashi ba.
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa za a samu karin kaso 60 na kudaden albashin ma'aikatan tarayya a shekarar 2025 wand ake nufin cewa ma'aikatan za su kashe N6.5trn.
Aikin Gwamnatin Najeriya
Samu kari