Ma'aikatar Bogi: Gbajabiamila Ya Yi Barazana kan Adeyemi, Zai Nemi N10bn
- Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa ya yi barazanar daukar matakin shari'a kan Adeniyi Adeyemi mai ikirarin shugabantar hukumar PFIPC
- Femi Gbajabiamila ya aika da wasika ga Adeniyi Adeyemi inda ya bukace shi da ya janye zarge-zargen da ya yi a kansa
- Wasikar wadda aka aika ga Adeyemi ta ba shi wa'adi don ya fito ya janye kalamansa idan ba haka ba kuma a kai shi kara gaban kotu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila, ya yi barazanar shigar da karar bata suna da neman diyyar Naira biliyan 10 (N10bn) a kan Prince Adeniyi Adeyemi.
Femi Gbajabiamila ya yi barazanar ne biyo bayan zarge-zargen da suka danganta shi da kisan kai, karbar cin hanci, da sauran ayyukan laifi.

Source: Twitter
Wasikar, wadda jaridar The Punch ta gani, tana dauke da kwanan wata 6 ga Yuli, 2026, kuma 'Kemi Pinheiro (SAN) ne ya sanya wa hannu a madadin kamfanin lauyoyi na Pinheiro LP, masu kare Gbajabiamila.
Adeyemi ya yi zarge-zarge kan Gbajabiamila
Wasikar ta biyo bayan wani taron manema labarai da aka yi a ranar 25 ga Yuni, inda Adeyemi wanda ke fuskantar tuhume-tuhume na laifuka kan zargin rawar da ya taka wajen gudanar da hukumar PFIPC, ya yi zarge-zarge kan Gbajabiamila.
Adeyemi ya zargi Gbajabiamila da neman kason kudaden da ake zargin na fara gudanar da hukumar ne, karbar kudi ta hannun wasu mutane, amfani da ikonsa ba bisa ka'ida ba.
Haka kuma, Adeyemi ya bayyana Gbajabiamila a matsayin "makashi" kuma "dan ta'addan kisa" a lokacin taron na manema labarai.
Wadanne bukatu aka nema wajen Adeyemi?
Wasikar ta bukaci Adeyemi da ya goge dukkan bayanan, da suka hada da rubuce-rubuce, bidiyoyi, da muryoyin da aka nada.
Sannan ya buga cikakken janye zargin da neman gafara a akalla gidajen jaridun kasa guda biyar da kuma dukkan kafofin sada zumunta da aka yayata taron manema labaran a kansu, sannan ya bayar da rubutaccen alkawari na kauce wa sake yin wani rubutu a kan Gbajabiamila.
A cikin wasikar, Gbajabiamila ya bayyana cewa bai taba yin wata hulda ko haduwa ta ko wane nau'i ba da Adeyemi.

Source: Twitter
Za a kai Adeyemi kotu
Lauyoyin sun ba da damar tsawon sa'o'i 72 domin cika sharuddan tun daga lokacin da aka karbi wasikar.
Rashin cika wadannan sharudda, wasikar ta yi kashedin cewa, zai sanya shigar karar bata suna da da kuma karar neman diyyar naira biliyan 10 (N10bn), wadda za a biya ga wata gidauniya da Gbajabiamila zai zaba.
Tinubu ya titsiye Gbajabiamila
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila, ya bayyana yadda ya kusa rasa mukaminsa.
Femi Gbajabiamila ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu ya yi masa tambayoyi kan rikicin tsige shugaban majalisar dokokin jihar Legas, Mudashiru Obasa.
A cewarsa, jami’an tsaro sun yi zargin cewa yana goyon bayan Desmond Elliott wajen haddasa rikicin siyasar majalisar dokokin Lagos.
Asali: Legit.ng

