Zargin Badakalar N400m: Atiku Ya Bukaci Tinubu Ya Kori Shugaban Ma’aikatansa

Zargin Badakalar N400m: Atiku Ya Bukaci Tinubu Ya Kori Shugaban Ma’aikatansa

  • Dan takarar shugaban kasa a ADC, Atiku Abubakar ya nuna damuwa game da karuwar cin hanci da rashawa a Najeriya
  • Atiku ya bukaci Shugaba Tinubu ya dakatar da Femi Gbajabiamila tare da binciken zargin karɓar Naira miliyan 400
  • Gbajabiamila ya musanta sanin PFIPC ko naɗa Adeniyi Adeyemi, yayin da Adeyemi ke zarginsa da neman kaso daga kuɗin fara aikin hukumar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Atiku Abubakar, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC, ya yi magana magana game da zargin na kusa da Bola Tinubu da badakala.

Atiku ya bukaci Shugaba Bola Tinubu da ya dakatar da Shugaban Ma'aikatansa, Femi Gbajabiamila, bisa zargin karɓar Naira miliyan 400.

Atiku ya fusata game da badakala a gwamnatin Tinubu
Dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar da Shugaba Bola Tinubu. Hoto: Atiku Abubakar, Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Getty Images

Hakan na cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Paul Ibe, ya fitar a shafin X a jiya Talata 30 ga watan Yunin 2026.

Kara karanta wannan

Yadda Bukola Saraki ya kalubalanci Buhari kan cin bashi a gwamnatinsa

Shawarar da Atiku ya ba gwamnatin Tinubu

Ana zargin an yi badakalar ta hannun wani wakili tare da neman ƙarin Naira miliyan 200 domin sauƙaƙa naɗin Adeniyi Adeyemi a matsayin babban daraktan Hukumar PFIPC.

Atiku ya ce ya kamata Tinubu ya jagoranci gwamnati ta hanyar tabbatar da cewa duk jami'ansa suna fuskantar hukunci idan aka samu zarge-zargen cin hanci ko rashin gaskiya.

Ya ce ikirarin da Gbajabiamila ya yi na cewa PFIPC ba ta wanzu a matsayin hukuma ya ƙara jefa gwamnatin cikin matsala, domin an ware mata Naira biliyan 27.4 a kasafin kuɗin shekarar 2026.

Atiku ya kalubalanci yadda za a ware irin wannan makudan kuɗi ga wata hukuma da ake cewa ba ta wanzu ba.

Ana zargin Gbajabiamila da badakalar makudan kudi
Shugaba Bola Tinubu da shugaban ma'aikatansa, Femi Gbajabiamila. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Twitter

Kiran da Atiku ya yi ga Tinubu

Atiku ya jaddada cewa shugabanci nagari yana dogara ne kan gaskiya da ɗaukar alhaki, yana mai cewa ba za a iya cimma hakan ba idan ana kare abokai da 'yan uwa masu rike da mukamai.

Kara karanta wannan

Iyayen daliban da aka sace sun rusa kuka bayan ziyarar tawagar Zulum

Tun da farko, Adeniyi Adeyemi ya yi zargin cewa Gbajabiamila ya nemi kashi 48 cikin 100 na kuɗin fara aikin PFIPC da ya kai Naira biliyan 27.4.

Adeyemi ya ce ya ƙi amincewa da wannan buƙata bayan an riga an karɓi Naira miliyan 400 ta hannun wakili, yayin da ake neman ƙarin Naira miliyan 200 domin tabbatar da naɗinsa.

Sai dai a martaninsa da ya fitar a ranar 11 ga Yunin 2026, Gbajabiamila ya musanta duk wata alaƙa da PFIPC, yana mai cewa babu irin wannan hukuma a ƙarƙashin gwamnatin Tinubu, kuma bai san wani naɗin Adeyemi ba.

Atiku ya zargi ana shirya masu gadar zare

An ji cewa dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar ADC Alhaji Atiku Abubakar ya yi zargin cewa ana ana kulla wani shiri da zai hana jam'iyyarsa shiga zaben 2027.

Atiku Abubakar ya bayyana cewa sun bankado akwai yunkurin amfani da shari'a da hukumomi wajen raunana jam'iyyar adawa.

Ya bayar da shawara ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da bangaren shari'a a kan yadda za su kauce wa zama 'yan abi yarima.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.