Yan Bindiga Sun Yi Ajalin Ƴan Gida Ɗaya Mutum 3 da Ke ba da Tsaro a Plateau

Yan Bindiga Sun Yi Ajalin Ƴan Gida Ɗaya Mutum 3 da Ke ba da Tsaro a Plateau

  • Wasu da ake zargin 'yan bindiga ne sun kashe 'yan sintiri uku 'yan uwa a Tarai da ke Riyom, yayin da suke tsaron al'umma cikin dare
  • Mamatan su ne Dachung Danjuma, Victor Danjuma da Nyam Danjuma, kuma an ce an kashe su nan take bayan maharan sun yi musu kwanton bauna
  • Shugabannin al'umma sun bukaci jami'an tsaro su kara matakan kariya a Riyom tare da kamo wadanda suka aikata harin domin tabbatar da adalci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Jos, Plateau - Wasu da ake zargin 'yan bindiga ne sun kashe jami'an sintiri uku, wadanda duk 'yan gida daya ne.

Majiyoyi sun hakan ya faru ne bayan sun kai hari a yankin Tarai da ke kauyen Jol a karamar hukumar Riyom ta Plateau.

Yan bindiga sun kai hari kan ƴan sintiri a Plateau
Taswirar jihar Plateau da ke Arewacin Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

Lamarin ya faru ne kwana guda bayan kashe jami'an tsaro biyu a Riyom, lamarin da ya kara nuna tabarbarewar tsaro a yankin, cewar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Sojoji sun gano inda aka boye gawar shugaban al'umma da aka hallaka a Imo

Rahotanni sun ce harin ya faru da misalin karfe 10:47 na daren Talata, lokacin da maharan suka kutsa cikin al'ummar tare da bude wa masu sintirin al'umma wuta.

An bayyana sunayen wadanda aka kashe da Dachung Danjuma mai shekara 51, Victor Danjuma mai shekara 37 da kuma Nyam Danjuma mai shekara 35.

Rahotanni sun ce mamatan, wadanda duk 'yan uwan juna ne, sun mutu nan take bayan harin, lamarin da ya jefa iyalansu da daukacin al'umma cikin alhini.

Wani mazaunin yankin mai suna Lyop Bitrus ya shaida wa manema labarai cewa 'yan uwan suna sintirin dare ne kamar yadda suka saba domin kare al'umma lokacin da maharan suka yi musu kwanton bauna.

Ya ce harin ya haddasa firgici, inda mazauna yankin da dama suka tsere daga gidajensu domin neman mafaka, cewar Vanguard.

A cewarsa, mamatan sun sadaukar da rayuwarsu wajen kare al'ummarsu, yana mai cewa mutuwar Victor Danjuma ta fi taba zuciya saboda ya bar mata da 'ya'ya biyar.

Mai magana da yawun ƙungiyar Berom Youth Moulders Association (BYM), Rwang Tengwong, ya tabbatar da aukuwar harin, yana cewa maharan sun kutsa Tarai da dare tare da kai hari kan jami'an sintirin al'umma.

Kara karanta wannan

Sojoji sun sada Idi Abasu Aiki da wasu 'yan bindiga 60 da Mahaliccinsu a Katsina

Ya bayyana kisan a matsayin abin takaici, yana mai cewa hare-haren da ake ci gaba da kai wa al'ummomin Riyom da sauran sassan Plateau sun zama abin damuwa duk da kiraye-kirayen kara tsaro.

Tengwong ya bukaci hukumomin tsaro su kara kaimi wajen kare al'ummomin da ke cikin hadari tare da kamo wadanda suka aikata harin domin su fuskanci hukunci.

Ya kara da cewa mazauna yankin ba za su iya ci gaba da rayuwa cikin tsoron hare-hare ba.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, kakakin rundunar 'yan sandan Plateau, SP Alabo Alfred, da na Operation Enduring Peace, Captain Polycarp Oteh, ba su amsa bukatar jin ta bakinsu ba.

Yan bindiga sun yi barna a Plateau

Mun ba ku labarin cewa wasu ‘yan bindiga sun yi kwanton bauna ga jami’an tsaro da ke sintiri a karamar hukumar Riyom ta jihar Plateau.

Rahotanni sun nuna cewa maharan sun kashe jami’an tsaro biyu tare da kwace bindigoginsu a yayin harin.

Jami’an tsaro sun kaddamar da bincike da sintiri a kauyukan da ke kusa domin gano maharan da suka kawo harin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.